_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿3⃣8⃣
" Oyoyo dear! tun dazu nake baza ido banga shigowar ki, ina kuka tsaya?.." cewar ANTY..
Cikin sauri Aysha ta ɗago d'aga kallon ƙurillar da take mawa MAN, muna haɗa ido da ita na sakar mata wata muguwar harara, ta buɗe bakin ta galala tana duba na, cikin matsanancin mamaki, tace" MUNIBBAT! me kike a nan kuma?..."
Ban kula ta ba ila zama da nayi, kusa da ANTY cikin shagwaɓ'a nace" ANTY!!! yunwa nake ji!..."
Murmushi tayi haɗi da turo min na gaban ta, tana cewa" to BISMILLA ci mana BABY na!..."
MAN ya taso shima, haɗ'i da turo min nashi yana murmushi, muryar sa a rausaye yace" MY HAPPINESS nima ga nawa nan ki haɗa duk ki cinye!!.."
Na fiddo ido waje zanyi magana sai ga Daddah ma ta turo nata, ai ban san lokacin da na fashe da dariya ba, inayi ina nuna su da hannu ɗaya bayan ɗaya, suma dariya suke abin gwani ban birgewa, AYSHA ta zuba min ido babu ko kifftawa...
ANNUWAR tun da ya kalle Aysha sau ɗ'aya bai sake kallon inda take ba, haushi ya cika mai zuciya musamma da yaga ina dariya shi baiga abin dariya a nan ba, ya saki tsaki a baiyyane...
" Ɗibi naka ka tashi mana, ko munci dole sai ka zauna..." Cewar Daddah dake zafga mai harara a wayance...
Shiru yayi kamar bazaice komai ba, sai zuwa can kuma yace" na fara gajiya wallahi, kun dai san har yanzu bamu gama yarda da abinda kuka ɗ'auko ba, yanzu kuma gashi na sake ganin wata ƙazamar talaka a cikin mu, har waye ma ya bata damar zama a inda muke cin abinci? Allah ya dawo min da Mommy wallahi duk sai kun gane..." A fusace yayi maganar...
MAN ya miƙe zuciyar sa babu daɗi yace" ANNUWAR! su waye zasu gane? menene aka ɗ'auko wanda baku gama yarda dashi ba? wacece ƙazama a nan? kana da hankali kuwa? dama har yanzu wannan muguwar ɗabi'ar baka barta ba? me kake nufi ne ANNUWAR?..."
ya ida zance da cafko ma kafaɗa yana matseta da ƙarfi...
To kun dai sai mutumin na ku dan hutu ne, cikin alamar yatse fuska da gajiyawa yace" MAN bana son irin wanna ka sake nace! dama nace na sauya ne wallahi bana ƙaunar talaka kuma bazan taɓ'a son ba har abada!.."
shima ƙ'arfin sa ya saka ya ture MAN din ya wuce abin sa...Daddah ta dafe goshi game da cewa" MAN ka rabu dashi please, inaga ya fara samun matsala a kan sa gaskiya..."
Aysha gaba ɗaya sai taji gidan ya gundire ta, ta taƙure a waje ɗaya sai jujuya abincin take, a hankali na juya wajen ta cikin kulawa nace" karki ji komai akan Yaya na zan fahimtar dashi kinji, ba wai dake yake ba shi din na daban ne..."
kallo tayi bata sake cewa komai ba har mutane suka fara tashi, aka bar mu dagani sai ita da MAN, Allah Allah nake ya tashi a wajen kar ya ɓaromin aiki...
"" Baby Ina son magana dake yanxu kinji?.."
Murmushin ƙarfin hali nayi kana nace" to ba damuwa amma bari zuwa anjima yanzu na gaji sosai Ya MAN!..."
Cikin kulawa yace" yawo yai tai min dake ko?..""
Ban kula shi ba ila tashi da nayi, dai-dai kunnen Aysha na sunƙ'uyar cikin raɗ'a nace" to yau fa gaki ga MAN, sai ki baiyyana mai abinda ke ranki ko zaa dace!..." duk da zuciya ta sam batayi min daɗi ba haka na ɗaure na furta dan na fita a zargi a wajenta...
MAN ya tsareni da ido haka nima, ji nake kamar na fashe da kuka amma babu hali, Aysha tazo a lokacin da nake so na manta da soyayyar ta ga MAN, shikenan komai ya watse...
" Daddah ita ce fa kawar tawa, AYSHA da nake gaya miki, yanzu haka na bar su da MAN zata baiyyana me sirrin ta..."
" Sannu sarki hankali kin kyauta ai sarauniyar tausayi, tashi ki bani waje shasha kawai..." ta faɗa cike da jin haushi na, zan sake magana ta d'agatar dani ta hanyar ɗaga min hannu, jikina a sanyaye na fice a sashin ta, gani na rasa mafita a karo na farko kenan...
Ina tafiya MAN ya mik'e zai wuce Aysha tayi saurin cewa" am Mal, sai kuma tayi shiru can kuma tace" nayi mamaki sosai da naga nan gidan ku ne, gaskia kun burgeni sosai dama kun haɗa wata alaƙa da MUNIBBAT ?..."
" To AYSHA mun gode, '''Eh ita ce matar da zan aura ina fatan zaki tsaya har bikin mu'''?.."
Cak ta makyale a waje guda, zuciyar ta nayi mata zullo wata irin zufa na karyo mata, hankali a tashe tace" MUNIIBAT fa Mal?.."
*" Eh Ita fa, ko akwai matsala ne?..."*
Ko kallon shi bata sake ba tayo ciki zuciyar ta nayi mata suya, a hargitsi take raɗa min kira, Ina kan ciyar ANTY bayan na gama gaya mata wacece AYSHA a waje na, jikin ta yayi sanyi har ta kasa ce mun komai, sai kuma ga kiran AYSHA...
Na mike da sauri tana zuwa ta kafe ni da ido, wasu hawaye masu zafi suna zubo mata, a haka har ta iso gaba na cikin kuka tace" kin kyau ta MUNI! na zaɓeki a matsayiƙ me rokon amana da alƙawari, na faɗ'a miki damuwa ta dan ina gani zan samu kulawa a gareki, na ɓata lokaci na domin muguwar shawarar ki, Ashe duk kina yin haka ne domin cikar burinki! kin shiga tsakani dashi, kin rabani da masoyi na na gaskiya a ƙ'arshe kin zagayi zaki aure shi, wato ni na zauna zaman jiran gawar shanu ko? me yasa kika sauya a yanda na san ki MUNI? yaushe kika dawo mayaudariya ne? kin cuce ni MUNI kin rabani da abinda nafi kauna, kullum kina cewa _ƙawata zan so ya fara furta miki kafin ke ki fara,_ Ashe duk cutace kika shirya ban sani ba, kin zalinci zuciyar da ta jima da matowa akan maradin ta..."
Gaba ɗaya kaina ya kule hankali na ya tashi, cikin rashin fahimta nace" Aysha tsaya ki ji, har abada bazan ci amanar ki ba!..."
" Karya kike karya ne wallahi, munafika kawai me tausayin munafirci, kin gama dani MUNI, sai yanzu na gano dalilin ƙin amicewar ki ga Ya jameel, yanzu na fahimci komai kina so ki aure MAN dan abinda yake dashi ko?..."
" Aysha wace irin magana kike haka ne? sanin kanki ne kuɗ'i basa gaba na!.."
" Karya kike! kina son shi ne domin wannan dukiyar da kike hange, haka ne mana in ba haka ba yaushe kika san su? nafi kowa sanin wacece ke, duk duniya baki da wasu yan uwa ko dangi da ya wuce Kawu da matar sa, me yasa kika dawo nan gidan da zama? kinyi haka ne duk sabida kudi! Eh amasar kenan MUNI, son abun duniya ya mayar dake wanda yayi miki domin Allah bashi kike gani da daraja ba, kin fifita kuɗi akan komai _sabida baki gada ba! rudin zuciya da nuna ƙulafici yasa kika kwaso jiki, kika taho gidan masu kuɗi munafika kawai wace bata gaji arziki b_..." Kauuu kauuu kauuu shuuuu taji ƙunne ta ya ɗauka, idanun ta suka lumshe jinta da ganin ta suka ɗauke na wucen gadi....
MUNIBBAT ta zare ido gani irin aika-aikar da kayi...
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce
ESTÁS LEYENDO
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Historia Cortalabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.