Chapter 53

39 2 2
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
For you husaini atk wannan nakane 'na gode kware da gaske Allahu ya bar zumunci,

🔚🔚🔚🔚

🅿 5⃣3⃣

Batai tammanin samun haɗin ka Daddah, kaf cikin gidan babu wanda ya bata matsala duk wanda taiwa maganar auren sai ance mata Allah ya sanya alhairi, wanna abun yayi mata dadi sosai, sai take ganin yanzu ta kai matsayin da zatayi komai da kanta, a cewar ta MAN dinma bazata fad'a mai ba sai bayan ana daura auren zatai mai albushir...

Daddah da Mama nee suka zo har gida, mura ta kamani kamar nace me dan dadi, sai hidima nake dasu na kasa zama waje guda duk wani abun da nake dashi motsa baki zuwa nake na d'auko musu,  cikin hikimar zance da dabara Daddah ta ringa yin min nasiha wace na kasa fahimtar dalilin ta, sai da tai me isar ta kana Mama na ta daura itama duk abinda suke cewa da insha Allah nake binsu dashi,  tausayi na suke ji sosai a ran su babu wanda ya gaya min dalilin zuwa su har suka wuce...

Naji dadin zuwan nan da su kayi min musamma da Mama na ta sake min zuwa na biyu...

To MAN ana kira shi sosai su Daddah su kai mai fad'a kamar yanzu ne farkon aure mu, shima da insha Allah ya bisu d'aga bisani ya dawo gida.

A rayuwar auren mu babu wata matsala dake tsakana dashi kullum cikin farantawa  juna rai muke, mu kan samu akasi ta wanin b'angare na halin rayuwa amma cikin sauki muke maganin matsalar mu, na fahimce shi sosai kamar yanda shima ya fahimci halina...

Kamar yanda Mommy take buk'ata haka ce ta kasance, shiryawa sukayi  shiri na ban mamaki an kashe kud'i iya kud'i tamkar wace zaaje d'auko amarya gaba d'aya, ficikar Dady ba tai kuka ba domin cewa tayi a yanzu zabin ta zai aure dole ne ta nunawa duniya zai aure yar gata me cikaken iko,  kanin Dadda sai kanin mahaifin su Dady wanda ya rage musu, neman aure har da Mommy kamar wata d'iyar sarki...

Duk wannan hidimar da Mommy take bata san yarinyar da take burin d'anta ya aure yau nee ake dinna din ta, da wani hamshakin me kud'i wanda ya ke ji da kan shi a kasar Dubai, ya tara abin duniya sosai jin sa yake tamkar wani ƙaruna kallon kowa yake a wulak'ace, domin dan izza ne na bala'i ita kanta Hafsat zai aure ta ne dan wani burin sa ba wai dan ta kai ajin auren sa ba,  a cikin sati gudu yake so ayi komai a gama, kud'i kawai yake turo musu kamar hauka amma har yanzu basu ga keyar sa ba, a yau aka daura auren su a cewar sa baya buk'atar komai sai matar sa kawai kuma a ranar yake so zasu bar kasar, Murjanatu  bata d'auki Mommy a matsayin wata kawar kirki ba shi yasa ko bikin bata ganyace ta ba, hidima suke bana wasa Mommy tazo da mota biyu na kayan alatu, sai dai aka gama bincike kayan tas sannan suka barta ta wuce, manya kawaye Murjanatu ne duk inda ka duba ka san kud'i ya zauna haka Mommy tai ta wuce su zuciyar ta cike da mamakin wannan taron, tsayar da ita akai a wani karamin falo ace war su Hajiya babba tace kar kowa ya shigo tana ganawa da yarinyar ta ne!..

Da yake ta san halin kawar ta bata ji komai ila, zaman jiranta da tai sosai ta b'ata lokaci kafin ta fito hannun ta rik'e dana Hafsat dake ta washe baki kamar gonar audiga, ko kallon Mommy Hafsat batai ba bare ta sa ran gaida ta..

A yanƙwane Murjanatu ta amsa gaisuwar Mommy tana yi tana duban jama'ar dake nesa da ita suna magana a haka, zuciyar Mommy ta soso da irin wulak'acin da akayi mata amma ta jure cikin k'arfin hali tace" kawa ta magana nazo muyi akan wannan alkawarin namu!.."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 13, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now