_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar Ce)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 1⃣8⃣
Tana isowa ta ɗaga hannu da nufi tsige ni ta ƙarfi, cikin rashin nasara Nusaiba ta damƙe mata hannu, ido cikin ido tace" kul!! kika taba mun yarinyar!.."
Fizzgi hannun ta mommy tayi ranta a mutuƙar ɓace take duban Haidar, bai bari tayi magana ba yayi saurin janyoni ɗaga bayan sa, yana tura ni wajen Nusaiba cikin girmamawa yace" Anti kuje kawai.."
Ba musu ta ja hannu na muka wuce, zuciyar kowa ba dadi, daddah na tsaye tana kallon mu...
Mommy bata ce mai komai ba sai ma juyawa da tayi ta wuce ciki abun ta, jikin sa a mutuƙar sanyayye ya bi bayan ta...
*****
Tunda ta fara magana har ta kai ƙarshe, bai ce mata ƙazaba ita kaɗai tayi ƙiɗanta tayi rawar ta, ta ɗaura da cewa" tabbas 'na san nayi kuskure amma kai ne silar faruwar komai tunda kai kake nuna babban-babbanci tsakanin yaran ka da ita, ka fiffita ta da yawa ka ɗaukake ta a gaban idanun mu kake kiran ta da sanyin idaniyar ka, ka faɗa min ko kai waye zuciyar ka dole ta ɗalsa maka wani abu, wallahi dah da aure a tsakanin ku bazan riƙe ta ba, nayi haƙuri nayi haƙuri sosai dana jure komai har muka kawo iyanzu, naji na amsa laifi na Amma alfarma d'aya nake nema a wajenka shine *KA MANTA DA ITA PLEASE TUNDA TA TAFI...??"*
Cike da firgici yake duban ta, ji yayi kirjin sa yayi masa nauyi wani irin zafi ne yake ratsa mai zuciya, take ya fara gani dishi-dishi, a hankali ya sulale akan kafafun aa ya fad'i a wajen...
Wani irin ihu ta saki cike da tsantsar kad'uwa tayo kan shi, had'i da Kiran suna shi da k'arfi amma ina tunin ya kai kasa...
*****
" Ka tashi ka bani waje Haidar, a yanzu kam na yarda baka jin magana ta, ya mu kayi daku kafin na amince yarinyar nan ta zauna a gidan nan?.."
" Ki gafarce ni Mommy banyi da wata manufa ba, kawai tausayi ta bani shine na taimaka musu.."
" Ba shi na tambaya ba, ka fad'a min da bakin ka abinda ya faru lokacin da aka sallamo ta!?.."
Ya sunk'uyar da kan shi k'asa murya can k'asan mak'oshi yace" Mommy please...
" Wallahi zan sab'a maka.."
Cike da tsoron yanda ta sauya ma cikin k'ank'ani lokaci ya fara magana kamar haka:
Yanda ta kasance,
*****
Kamar yanda ya saba yau ma yana zaune a gaban gado na, sai addu'a yake tufa min a hankali yatsar hannu na ta fara motsawa, sam bai kula ba sai zuwa can hankalin sa ya kai waje, da wani irin sauri ya mik'e tsaye had'i da dafa gadon zai duba fuska ta, aiko caraf na danke mai hannu ina wata irin jijiga tamkar wace aka sani a majajawa, tsoro da firgici ya shi kwallawa doctors kira cikin gagawa, tun kan ya gama rufe bakin sa sai gasu nan sun shigo, tamkar dama suna bakin kofa cikin sauri aka fara bincika ta d'aya b'angare kuka anyi-anyi ta sake shi taki sakin shi, domin wani irin rok'o tayi masa na gani kashe NI...
Cikin ikon Allah da yarda sa, suka samu jijigar ta tsaya ta hanyar yi mata allurar barci, shi dai Haidar yana tsaye komai a gaban idanun sa kayi mata, wani irin tausayin ta ya kama shi...
Su Daddah suna bakin kofa sai aikin sintirin suke...
Bayan ta dawo normal ne doctor ya dube shi murmushi fal kan fuskar sa yace" aboki na congratulations kanwar ta zata iya farkawa a ko wanne lokaci, sai da kuma kamar yanda na fad'a maka a baya, muna dai sa ran tashi lafiya kalau babu wata matsala..."
Yake kawai Haidar yayi mai amma bace komai ba, har suka fice Nusaiba ta shigo hankali a tashe take duban Haidar kana tace" ya ake ciki yanzu?.." " sunce zata iya tashi a ko wanne lokaci.."
Wata ajiyar zuciya ta sauke cikin an'nashewa tace" Alhamdulillahi bari nayi ma AN'NUWAR albushir..." ta fad'a tana k'ok'arin zaro wayar ta...
Cikin sauri ya rik'e hannun ta fuskar shi babu wadatacen murmushi yace" kiyi hak'uri Anti jiya Mommy ta tura shi Landon, kuma duk akan wannan baiwar Allah nee.."
Jikin ta a sanyaye ta mayar da wayar maajiyar ta, a zuciyar ta tana jijina bakin hali irin na Mommy, tace" zanje gida na had'o mata abinda zataci.."
"Ok sai kin dawo zan zauna da ita.."
A waje da ta fad'awa hajiya abinda zatayi sai tace su tafi tare ita ma a matse take...
Tafiyar su ko awa d'aya ba suyi ba na farka, da fari d'akin na fara kallo a hankali cikin halin jinya, na dube mutumin dake zaune kusa dani yana dana waya tamkar dama can na san shi nace" Kawu na!!.." da murya ta da ta koma ta sangartatun Yaya..
Cikin mamaki da alajab'i yake buda na, a hankali kuma ya koma ya zauna had'i da cewa" Baby kin tashi?.."
Ido kawai na zuba mai bance komai ba, dan bana ganewa..
Tunda d'aga lokacin ya dawo abokin hira ta, bana wa kowa magana sai shi, bana cin komai in bashi zai bani ba, duk wani abu muddin ba d'aga hannun shi ya fito ba bana amsa, shi ya kowa ya min magana, ya koya min yanda zanci abu duk yanda rayuwa take tafiya shiya koya min, sanu a hankali na fara sabawa da mutane biyun da nake gani kullum Nusaiba da hajia, na samu sauki sosai kamar yanda sukace sun dibar min lokacin da zaa dawo dani suyi min aiki a kai na, aka sallamo ni kai tsaye gida su kayo dani...
Zaune take a babban palon gida, taci uban ado kamar yanda ta saba sai k'amshi take zubawa, cikin tsananin isa da gadara ga mulki da izza da take zuwa, da kyar ta iya amsa musu salamar da suke, har sun gota ta zasu wuce ta d'ago cikin isa tace" Nusaiba! ina zakai wannan abun na hannun ki..?" ta fad'a a gadarance...
Comments
And
Shared
Please
Mrs Abubakar ce
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.