Chapter 32

44 2 0
                                    

_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
                  (The Orphan)
                        *MARAINIYA*

        Wattpad:AbubakarUsaeena

      
                *💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

                 Written by:
                    *HUSAINA B.ABUBAKAR*
      *(Mrs Abubakar)*

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM


🅿 3⃣2⃣

Tunda ya fara maganar nake kukan rabuwa dashi, domin na san babu shaka Kawu na ba wasa yake min ba, lokacin da ya fita ya bar ni na fara duba saƙonin da MAN ya aiko min, tsatsar soyayya da zallar ƙauna na gani, nayi kuka kamar bazan ɗaina ba, wata irin soyayyar sa nake ji tana ruɗ'a ta,  gaba ɗ'aya barci ya ƙaura cewa idanu na, banda hawaye babu abinda nake, a gaskiya ina mutuƙar ƙ'aunar MAN har cikin zuciya ta....

******.  *****.   ****

Cike da nuna kulawa Daddah tace"" Nusaiba  kin san me nake so dake yanzu.."

" A'A hajiyar mu!.."

" Gobe in  Allah ya kai mu, ki gyara min ɗ'akin baby zanyi baƙuwa, duk abinda ya kamata a sake ki tabbatar ana saka shi kinji!..." 

cikin biyayya tace" insha Allah! Hajiya, su Auta zasu dawo kenan?.."

Murmushi tayi marar sauti kana tace" a'a halan kin manta su da alhaji zasu dawo? wannan baƙuwa tace zata zo.."  kafin ANTY ta sake magana har Daddah ta fice a ɗakin...

ɗaki na ANTY ta shiga, jikin ta a sanyaye take duban komai na ɗakin, wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, cikin murya me rauni tace" yaushe zaki dawo gareni baby na!?.." ta jima a zaune tana tunani na, daga bisani ta fice a ɗakin...

Washe gari, da sasafe na fice a gidan mu, kai tsaye gidan su Aysha na nufa zuciya ta na zafi, sai da na tsaya a zauren gidan naci kuka na na gode Allah sanan na ida shiga ciki, ita kaɗai na samu a tsakar gida, da alama yanzu ta tashi,  ganin ta da nayi a yanzu take naji zuciyata na tafasa, ji nake kamar na fasa gaya mata, amma dana tuna halacin da tayi min sai na ɗ'anne zuciya ta, nace" AYSHA!..." 

Da sauri ta ɗ'ago, fuskar ta cike da an'nuri tace" MUNIBBAT kece da sasafe haka?..." ta faɗ'a tana wani duban baya na kamar wace bata yarda dani ba...

Hannun ta na kamo, cikin ƙarfin hali nace" zo kiji.." ba musu ta biyo ni har zaure,  na ma rasa ta ina zan fara gaya mata, gani shirun yayi yawa yasa tace" MUNI lafiya dai ko?.."

" Eh lafiya kalau, dama ehm dama.." wallahi na gaza faɗa mata...

A hankali ta dafa kafaɗa ta cikin sigar rarashi tace" me yake damuki kawa ta? ko ANTY CE?..."

" Za muyi tafiya ne, kuma ban san ranar dawo war mu, shine nazo nayi muku sallama, ina Yaya Jameel?.."

Shiru tayi na yan mints  sannan tace" amma shine kika tashi hankalin ki haka,  anya gaskiya kika gaya min kuwa?.."

Murmushi nayi nace" tunda nake dake na taɓ miki karya? Allah tafiya zanyi yau din nan!..."

" To naji me ya samu idanuki suka kumbura, ni gani nake ma kamar baki samu isha-ishan barci ba?.."

Tausayi ta bani gani yanda take bani kulawa ta musamma, again murmushi na sake saki, kana nace" gulma kawai me ya shafeki da idanuna! ni dai ina Yaya Jameel yake?.."

Ita ma murmushi tayi kana tace"  kamar kin san jiya sai da muka raba dare dashi muna hirar ki, shi a lallai sai na fara faɗa miki, amma bari na taso shi waƙ'a a bakin me ita tafi daɗi..."

Ban kawo komai a raina ba, har ta wuce ciki babu jimawa ta dawo, hirar makaran ta muka fara, a nan ne na samu damar tambayar ta, cewa" Aysha niko ya soyayyar ki da Mal Haidar kuwa? kin samu ci gaba ko kuwa?.."

Take an'nurin fuskar ta ya ɗ'auke damuwa ta maye gurbin sa, cikin tsaki tace" wallahi  MUNI kin taɓo min inda yake min ƙyaƙƙayi, mutumin nan ya mayar dani wata sha-sha, tunda nake dashi bai tab min kallon so ba, bare na sa ran nan gaba zai furta min kalamar so, kullum ni kaɗ'ai nake hauka na, gashi ke da NAFESATU  yanzu duk ba zuwa kuke ba, na ma rasa ta yanda zan bullowa lamarin, sam zuciyata bata kyau ta min ba,  please ki bani shawara ya zanyi ya so ni dan Allah!??..." ta faɗ'a tana kama hannu na cikin wani yanayi na buƙatuwa...

" Ki cire shi a ranki Aysha! zan so ace shi ne nuna miki so kafin ke, bana so ki wahala akan soyayyar da bata da riba, wato makauniya soyayya, kiyi haƙuri dashi shine mafi alhairi!.."

Zare hannun ta tayi ɗaga nawa, idanun ta har sun kawo ruwa, tace" hmm kin ɗauka soyayya ta a gare shi wasan yarace? a'a MUNI dan baki san zafin so bane kawai, shi yasa zakice na rabu dashi, ina masa san so! soyayya da babu irin ta,  har yanzu ke yarinya ce a fagen soyayya, ina mutuwar ƙaunar HAIDAR duk  da shi bai san ina yi ba, Allah yasa shi rabu na ne!..."  wasu  hawaye masu zafi ne suka zubo mata, ta sake duba na cikin karaya tace" muddin kin san ba addu'a zakiyi min akan na samu cikar buri na ba, karki sake magana akan mal Dan ALLAH!.."

Na kasa magana sai aukin kukan zuci da nake, tausayin Aysha ya gama cika min zuciya, ga tausayin rayuwar da nake ciki,  zuciyata taki bani cewa da gaske Aysha yake aikowa da saƙ'onin sa, to in ba ita bace WACECE? gaba ɗ'aya kai na ya ƙulle, tabbas Aysha baza tayi min karya ba...

*Yanzu waye zaɓi na a cikin su?..."*

Zanyi magana kenan sai ga Jameel ya fito, fuskar sa cike da farin ciki, sam bai kula da yanayi da muke ciki ba...

" My kanwa ta! ashe ko da gaske take ke kike kira na..."

Kallo ɗaya nayi mai  na gane cewar wanka yayi da safiyar nan, da ƙyar na iya ƙaƙalu murmushin yake, nace" barka da safiya Ya Jameel?.."

" Yauwa barka dai, ina fatan kanwar tawa tashi cikin ƙoshin lafiya?.."

" Lafiya kalau.."

"Aysha ta isar miki da saƙo na kuwa?.."
a gajiye nace" a'a ta dai sheda min, gaisuwar ka amma ban da wanna banji komai ba!.."

Ya wani rage murya, haɗi da kashe min ido, cikin wata murya da ban san shi da ita ba yace" MUNIBBAT tun  ba yau ba, tun kan kika haka, nake jin wani baƙwan yanayi a tare dake, a kawai  wani babban sirri dake cin raina, kullum ƙwana duniya dashi nake tashi, dashi nake ƙwana, ban sani ba ko kema kina jin irin abinda nake ji?.."

Gaba ɗaya ban fahimci inda ya dosa ba, hankali na yana ga kanwar sa, a gajiye nace" bana jin komai a raina ni kam kamar yanda Aysha take nima haka na ɗ'auki kai na a wajen ka..."

" Ɗ'aga yanzu ki cireni a wannan matsayin, ki ɗ'auki kan ki ke  kyakykyawar kaddar tace, '''MUNIBBAT INA SONKI, INA ƘAUNAR KI, KIN AMINCE ZAKI AURE NI'''..."

Cikin sigar soyayya ya faɗ'i maganar, yana wani langwabar da kai gefe...

Cikin tsananin tashin hankali nake kallon sa, gaba ɗaya jikina ya ɗ'auki rawa, idanu na sun firfito waje na shiga girgiza kai na tamkar wata ƙyadangaruwa, wasu hawaye masu dumi suka zubo min, na juya zan gudu Aysha tayi saurin shan gaba na, idanun ta fas akai na...

" A'a MUNI, dan Allah karki zamo sanadin tarwatsiwar farin cikin gidan mu, na amince zan amshe k'addara ta ta rashi sa'a a soyayya da hannu bibiyu,  zan jure bakin ciki na, dan Allah karki sa na fara tunanin rashin sa'ar mu a jini yake! YAYA yana mutuƙar ƙaunar ki, tun farko zuwanki rayuwar mu, a ta dalilin ki ya dawo zama cikin anguwa, dan Allah ki amince dashi, na san bazaki watsa mana kasa a ido ba!.."

Tabbas Aysha tafi kowa sani, in na shiga ruɗani bana iya magana, amma yau sai ta gaza fahim ta ta...


Comments

And




Shared


Mrs Abubakar ce

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now