*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*
💑 *WAYE ZAƁIN MUNIBAT*?❤
(The orphan lady)Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR**(Mrs Abubakar)*
Wattpad @AbubakarUsaeena🅿 1⃣
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Tafe nake a kan hanƴata na komawa gida, zuciyata cike da saƙe-saƙe babban tashin hankalina bai wuce abin da zanje na tarar a gidan ba, bayan layin mu na biyo ko Allah zai sa a dace na samu abin da na fito nema, yau ma kamar kullum babu kowa a wajen da yake unguwace ta masu hannu shuni.
masifar ta kawai nake tunowa, take wasu hawaye masu zafin gaske suka zubo min a kuncina,gefen hijabina na kamo na share hawayen.
Wani tank'ameman gida na zo giftawa cak naja na tsaya ina kallon wata dattijuwar mace, wace ak'alla shekarun ta bazasu hau ra 45 ba, kai daga ganin ta ba sai an fad'a ba ka san kud'i sun zauna duba da irin kayan dake jikin ta, masu tsadar gaske ga wasu manƴan gwalgwale dake manne a wuyanta da hannunta masha Allah nace zuciyata cike da sha'awa..
Ɓangaren ta na hagu na hango wani had'ad'an gay a kusa da ita ya wani neke fuska tamkar k'aramin yaro, gaskiya ya had'u sosai fari ne kar da shi fuskar nan cike da saje, me dan k'aramin baki ko ba'a fad'a min ba na san babu abinda yasa a lips din sa kawai hallintar sa ce a haka, gani zasu shige mota ne nayi saurin isa inda suke murya na rawa nace" Asalam alaikum.."
Cikin daddaɗar muryata wacce ko ni ina alfhari da ita, cikin biyayya da girmamawa zuciyata cike da tararabin yanda zasu amshe ni na sake k'ok'arin furta " ina wunin ku hajiya? dan Allah taimako nake nema?.." suka juyo cike da mamaki suna min wani irin duba wanda sai yanzu na gane tsantsar wauta ta, muryar dattijuwar nan ce ta daki dodon k'unne na cikin azama na sake gyara tsayuwata ina sauraron ta.
Ta ce "ƴan mata wani irin taimako kike nema a tsakar ranan nan.?"" ta ida maganarta tana mai k'arasa shiga motar...
Na bude baki zanyi magana kenan yayi saurin rigani da cewa" ohh Daddah! kin fa san sauri nake irin wannan mutanen babu abin da suka iya sai k'anzan k'urege, ki bata wani abu kawai tunda kinyi niyya bazan hanaki ba.." ya fad'a cikin murya sa me sanyi da shegan dadi, wai haka a masifance yayi maganar ikon Allah, duk da banji dadin yanda ya k'atse ni ba amma haka na daure banyi magana ba..
Cikin wasa da manƴan taka ta ce"Allah ya shirya ka yasa ka gane, jakata babu canji bata wani abu to..." ta fad'a cike da zolaya..
" Daddah! bana so fa..."
domin maganar ma bason yin ta yake ba..." ANNUWAR nace kaba ta wani abu, in ba so kake yanzu ka ga b'acin raina ba.." ita ma ta fad'a cikin isa da izza...
Gudun b'acin ranta yasa shi zaro d'ari biyar yana shirin jefe mata, Daddah! tace" hannu da hannu nake so ka bata, sannan kuɗin sunyi kaɗan ka ƙara mata" ɓoyayyen tsaki ya saki, kana ya ƙara mata yawan kuɗin cikin fushi ya zaro rafa din d'ari biyar biyar ya miƙa mun a wulaƙance fuskarsa na kallon gefe ran nan nasa a had'e...
Na kasa amsa jikina ya ɗauki rawa domin tunda uwata ta kawo ni duniya ban taɓa ganin kuɗi masu yawa haka ba, hajiya ta dube ni a tsanake take ta hango tsantsar tsoro da firgici a kwayar idona, sai hakan yayi mata daɗi sosai cikin nuna kulawa da kamewar mutuncin ta tace" amsa mana ba taimako kike nema ba? ai kin samu amsa sai ki mai godiya.." ta fad'a tana fad'ad'a yalwatacen murmushi...
Hannuna yana rawa na amsa cike da girmamawa da nuna jin daɗi nace" na gode Allah ya ƙaro arziki da wadata, ya ƙara lafiya da nisan kwana na gode sosai hajiya.." na fad'a har ina goge hawayen da suka sub'uce min...
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.