_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*~Alhamdulillahi wannan kyautace gare ku masoya na, masu bin novel ɗinna kaɗai wannan pagen naku ne, masu comments na gode ƙware da gaske Allah ya bar ƙauna, ku ci gaba da sambaɗo min comments ni kuma zan dage da typing, fata na ayi aiki da alhairin dake cikin sa~
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 2⃣2⃣
Da wani irin fushi Mommy ta waigo. fuskar sa yalwace da murmushi yace" sorry Mommy yarinya ce, wannan hukuncin yayi mata tsauri..."
A hankali tayi kasa da hannun ta, ranta nayi mata ƙuna..
Daddah ta shafa min fuska ta cike da tausayi na, kana ta kalle mommy dake nishi tayi wani guntin murmushi me ciwo tace" kin kyau ta! kinyi abinda ranki ke so! amma karki manta akwai ranar nadama! wannan da kike rainawa insha Allah wata rana sai kin nemi taimakon ta! yaron ki ya hauka ta musu yarinya daga ƙarshe kin ɗaure mai gindi har da tura shi wata kasa, sabida yau ya dawo tana mai kallo Jan zaki! Shine kika zage ƙarfin ki akan ta kika wanka mata mari? ina jiye miki wallahi! sakare kawai marar wayo da tunani! Allah ya dawo dashi lafiya dole ne ma naji shi ya ɗaure miki gindi wannan rashin hankali Koko? zai dawo ya same ni ne, tunda ni kin nuna min ba a bakin komai nake ba, ko banci ɗaya darajar matsayi na ba ai naci na ƙarshe, tunda ni na haifa mijin da kike tunƙaho dashi, wallahi zaki sha mamaki ne Ameenatu!..." da ƙarfi Daddah take magana, kana duban fuskar ta ka san tana cikin bacin rai me tsanani, a fusace tace" muje ciki Nusaiba!!.."
Luf nayi a jikin Anty ina kuka kasa-kasa a hankali tsoron matar yake ratsa ni, wallahi har cikin raina bana ƙaunar na sake haɗa hanƴa da ita ko na ga fuskar ta...
AN'NUWAR ya dubi Mommy cikin yanayi ba dadi yace" why!! Mommy? ai da kin barni da ita, gashi yanzu kin ɓatawa Daddah rai!.." yanayi maganar sa cikin gajiya wa...
Mommy da jikin ta ya sanyi, jin irin kalaman Hajiya domin basu taɓa haka da ita ba sai yau, take tsanar yarinyar ya sake ratsa ta, tayi sauri basar wa haɗi da cewa" manta da su Son! yanzu ka shiga ciki ka watsa ruwa ka kwanta ka huta zuwa anjima ka fito mu gaisa.. "
Ba haka ranshi yaso ba, amma ya iya dole ya amsa da to...
Tunda muka koma ciki nake kuka, su Daddah sai aikin rarashi na suke, gani naƙi yin shiru yasa Daddah sake komawa shashin Mommy fuskar nan ta ta a murtike, zaune ta same shi ya dafe kai kamar marar lafiya, tace" Aliyu! zo ka rarashi yarinyar nan!!.."
Cikin sauri Mommy ta ɗago tana duban ta, kirjin ta na halbawa, hango tsagwaron rashin mutunci a idanun Hajiya yasa tayi saurin kasa da idanun ta, shiko kamar jira yake ya mike da sauri ya shige ciki, duk da irin harara da Mommy take aika mai...
Daddah ta fara tafiya Mommy tace" kinyi haƙuri Hajiya! nakasa jurewa ne! dan Allah karki gaya mai..."
Ko kallon ta Daddah ba tayi ba ta wuce ciki abun ta...
Cikin sigar rarashi yace" yan matan Kawu waye ya taɓa mini ke!..?" ina jin murya sa nayi saurin faɗawa jikin sa ina sake sakin kuka, cikin dabara ya tureni daga jikin sa, tausayi na na kara mamaye mai zuciya yace" kiyi shiru kin ji! ba ruwan mu da Mommy!.." ya ƙarke maganar da share min hawaye...
Na turo baki na gaba murya a shake nace" kuma sai na faɗawa Anty na!.."
"Eh ki faɗa mata, yanzu kiyi shiru muje na kai ki yawo, ai zaki je ko.." duk da ban san me yake nufi da yawo ba amma haka nan naji ina son bisa...
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.