Chapter 3

61 9 0
                                    

*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*

     💑 *WAYE ZAƁIN MUNIBAT*?❤
              (The orphan lady)

Written by:
  *HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*
        
      
Wattpad @AbubakarUsaeena

🅿 3⃣

BISMILLAHIR RAHMANIR   RAHIM

MUNIBBAT yarinya ce k'waye d'aya tak da iyayen ta suka mallaka a duniya, mahaifiyar ta me sunan Rabi'atu macece me hak'uri da juriya,  bama su kud'i bane suna  da rufin asirin su dai-dai gwargwad'o, basu rasa cin yau basu rasa sutura ba, domin malan Dahiru yana da sana'ar sa kuma Alhamdulillahi yana samu sosai, kayan miya yake siyar wa a cikin kasuwar  gwarawa, dake cikin hayin rigasa,
yarinya ta taso cikin kulawar uwa da uba, ta samu ingantaciyar tarbiya ta 'bangaren biyu, tun tana k'arama iyayen mahafin ta suka rasu, sshi kad'ai ne dasu, bashi da wa bare k'anni haka ne yasa ya mayar da duk wata kulawar sa ga matar sa wace ita ma tun tana k'arama Allah ya amshi ran iyayen ta, bata da kowa sai Yayan ta na miji, yana bata kula sosai duk da sunyi ma juna nisa yakan ziyartar ta lokaci bayan lokaci tare da matar sa me sunan SHAFA'ATU, wace Mama na, ke kiran ta da ANTY kasancewar ta matar Yayan ta amma ba wai dan ta girme mata ba...

Tun ina k'arama ta Allah ya d'ura min k'aunar karatu, Allahmdulillahi ina shekara goma cif-cif na sauke alkur'ani me girma, inda Baba na ya taka rawar gani wajen yi min walima dai-dai k'arfin sa, kawu na yazo da matar sa shi ma yayi k'ok'ari domin dinki yayi min har kala biyu, matar sa kuma ta siyo min takalmin me kyan gaske, Anty tana bala'in sona sosai ta kan nuna min k'auna a gaban iyaye na musamma gaban k'awu na, kwanan su biyu suka koma...

Nan na mayar da hankali na akan karatuna na boko da had'ar alkur'ani da muke yanzu a makaran ta , iyayen na suna alfahari dani sosai  shi yasa duk abinda suka samu MUNIBBAT duk da k'arancin shekaru na wani lokaci har tausayi suke bani, ina da shekara goma sha uku cif-cif, Anty ta haihu ta samu 'yar budurwa, gaba d'ayan mu muje sunan ta kano, inda tun kallon farko na k'walla rai akan yarinyar ranar sunan  aka rad'a mata SUNA BISHIRA abin gwani ban sha'awa, washe gari SUNA muka dawo garin mu kaduna zuciya ta cike da soyayyar Bishira....

******

Shekara ta goma sha shida yanzu na san koma na san yanda rayuwa take tafiya, na iya duk wani aikin gida kuma haka bai hanani karatuna ba, ina da k'ok'ari a makaranta  a yanzu ina JS3 abu na, hata malaman makarantar suna alfahari dani gaskiya,  a lokacin ne ANTY ta sake haihuwa inda ta samu d'a miji murna a wajen iyaye na ba'a cewa komai, lokacin Bishira tana da shekara shida a duniya, har anyi mata k'anwa me suna fiddusi, yanzu kuma ga yaro an sake samu, gaskiya iyaye na suna k'aunar k'awu na da matar sa sosai su kayi musu siyayya ta ban mamaki zuciyoyin su cike da murana a suna saura k'wana biyu da yake ranar alhamisi ta haihu muka d'auki hanya muka tafi, dama mun samu hutu a makaranta...

Anty tayi muryar ganin mu har da kuka lokacin da su Mama na ta bata  abinda mu kazo dashi, washe garin suna kamar yanda aka sab'a muka tashi tafiya...

*****

Tunda gari Allah ya waye Anty ke had'e rai, ko yan uwan ta sun kasa gane kan ta bare kuma mu haka bai hana mu fasa shirin mu ba, k'awu ne zaune a gaban Mamana cikin nuna kulawa gare ta, yace " wai ni kam dole ne sai kin tafi a yau ne?.."

Cikin murmushin da bai rabuwa da fuskar tace" to kafi so na zauna a nan na bar mijina a can shi kad'ai a gida..?" ita ma ta fad'a cikin zolaya..

Murmushi yayi yace" a'a ni na isa! kawai haka nan  naji bana son tafiyar taki ne me zai hana ki bari zuwa gobe, in yaso sai mu wuce tare tunda duk hanya d'aya ce.."

Cikin girmamawa tace" gaskiya bana jin tafiyar mu za tazo d'aya domin nayi wa malam alk'awari washe garin suna zamu dawo, in yaji shiru ran shi bazai ba mai dadi ba, a yau zan wuce gaskiya..." ta fad'a cike da damuwa...

WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCEWhere stories live. Discover now