_WAYE ZAƁIN MUNIBAT_
(The Orphan)
*MARAINIYA*Wattpad:AbubakarUsaeena
*💫DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION💫*Written by:
*HUSAINA B.ABUBAKAR*
*(Mrs Abubakar)*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM
🅿 4⃣9⃣
" Mama ANTY MUNIB ce ta kawo mu!.." cewar Bishar..
A hankali ta ɗago ta fuskar ta har yanzu akwai murmushi tace" tana ina yaushe ta dawo?.."
Har na kai kofar fita najiyo murya ANTY tace" MUNIBBAT!.."
Cak na tsaya ina me goge hawayen fuska ta, a hankali na juyo kai na a ƙasa, naƙi bari mu haɗa ido ta saki murmushi me sauti jikin ta yayi bala'in sanyi ganin yanda na sauya na ƙara kyau da zama cikakiyar mace, cikin sanyin murya tace" a karo na farko kenan a rayuwa ta kinyi min abinda bazan manta dashi ba, na gode sanyin idaniyar Kawun ta!.."
Da sauri na dube ta jin yau ANTY ke min godeya, na sake goge hawayen fuska ta da kyau, ina murmushin jin dadi...
Hannuna ta kama har cikin ɗakin ta, ba lefi akwai komai najin dadin rayuwa, sai nan-nan take damu yara kam ko wanne ya haye mata jiki, gaskiya uwa daban take a duniya...
Kayan da muka zo dashi ta aika wasu yara ƙanwa ta, suka shigo dasu bayan komai ya lafa maman su ta shigo muka gaisa, mu danyi hira da ita kaɗai a maganar tane na gane ANTY tayi sanyi irin sosai dinan, cikin maganar ta manya taka take bani haƙ'uri a fakaice, na gane me take nufi amma nayi kamar basan inda ta dosa ba, bayan fitar tane ANTY tace" MUNIBBA yaushe kika dawo?.."
Cikin biyayya yanda ta sanin dashi nace" jiya nazo, munyi hutu ne shine bangaki ba, dana tambayi Kawu yace min kinyi tafiya ne, shine muka zo na gaisheki..."
Dadi taji har cikin ranta, gani duk ukubar data gana min ban manta da ita ba, tace" za kuyi min ƙwana biyu ko?.."
Kallon ta nayi a yanzu sai ta bani tausayi, nace" amma bamu tambayi Kawu bs kina ganin bazaiyi faɗa ba?.."
" Kina tunanin a irin soyayyar da yake miki akwai abinda zakiyi a yanzu yayi miki faɗ'a, tunda nazo gida yarana basu sake kwana a inda nake ba dan Allah kice mai zaku ƙwana biyu!..?"
Wani irin dadi nee ya sake kamani jin yau ni ANTY take roƙa, na gaza boye jin dadi na da murmushi akan fuska ta nace" ba komai ANTY zan gaya mai!..."
" Yauwa, MUNIB ina fatan gidan da kike bakya samun wata matsala ko?.."
Take yanayi fuskata ya sauya zuwa damuwa, Ina shirin yin magana waya ta ɗauki ruri cikin sauri na ciro ta Mama nace! murmushi nayi game da tashi d'aga wurin ina komawa gefe domin ganawa da ita...
Nan ta bini da ido gani na fara waya, sai ta koma kan yaran ta da tambayar lafiyar su, ko wanne su karar ANTY Rabi yake kawo mata, d'aga wannan yace tayi masa kaza sai me cewa baiyi komai ba ta dake shi, kuma a gaban Abba...
Haka dai ranta ya ɓaci amma sai ta ɗaure tuna abinda tai ne ake ramawa akan nata yaran, danasani ya taru ya cushe mata zuciya, Bishira ta matso kusa da ita murya can kasa tace"" Mama ki nemin yafiyar to ko zamu sakewa a gidan mu, kin ma san yau ANTY tayi faɗ'a akan mu, tacewa matar baba dole ta bar mu mu sake a gidan ubanmu in ba hakaba kuma ta hana ta sakatt! Mama shiru tai bata iya bawa ANTY amsa ba.."
Ƙare mata kallo tai kana tace" d'aga yau kar na sake jin kinyiwa wasu laɓe ko kin dauko zance da baa tambayeki ba kin faɗawa wani, zan ɓata miki rai mutuƙa akan wannan halin da kika d'auko sabo!.." cikin faɗ'a tai mata maganar...
YOU ARE READING
WAYE ZAB'IN MUNIBBAT BY MRS ABUBAKARCE
Short Storylabari ne da ya kushi abubuwa da dama. musamma akan marayu, soyayya butulci yaudara makirci.