Page 1

1K 49 5
                                    


*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)'''

*~Na Mallakin~*
*Mum Irfaan*
A.k.a *_Er-gafaii_*

*Follow me on Wattpad-Mumirfaan*

My Gmail Account
Www.mumirfaan77@gmail.com

*1*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

_Bismillahir rahmanir Raheem_

Kana kallanta kaga sabuwar amarya fil saidai abun mamakin itada Iyayanta sai faman cin uban gudu sukeyi da sanyin asubar Nan, yayinda tana can baya kira take "Inno ku tsaya"
Ba musu suka tsaya cak, tsugunnawa tayi tana maida numfashi Tace "Inno Wai Ina sauran kud'in Dana d'ibo ne Naga ban gansu a hannnunki ba"
Inno cikin muryar wahala Tace "Tambayi Baffanki Dan kin ganni Nan gwala-gwalai ne kawai a hannuna"
Matsawa kusa da Baffanta tayi Tace "Baffa ina kud'in Dana Baku Wai?".
Ta fad'a kamar zatai kuka.
Baffa yace "Kinga Binafa kibar maganar kud'in Nan Kizo mu gudu Wallahi da zarar Alhaji ya farka yaga aika-aikan da kikai Masa sunanki sorry, kibar zancan kud'in Nan Kizo mu tafi ai kin kwaso Mana da yawa tunda a k'alla akwai dukiyar data haura sama da miliyan biyu a hannunmu"
K'ugu Binafa ta ruk'e Tace "Tab lallai Baffa kud'in fa dana Manta dasu a k'alla zasukai wajan miliyan shida, dalar amurkace fa"
A tare Baffa da Inno suka had'a Baki sukace "Miliyan shida?"
Girgiza musu Kai tayi tana fad'in "Eh Mana, gashi Yanzu munyi nisa, Kuma nasan Mai gadi ya dawo inhar na shiga to bazan fito ba Nina sani"
Inno da Baffa matsawa sukayi kusa da ita yace "D'iyar Albarka, shin bazaki iya haura katangar gidan bane?"
Binafa gwalalo idanu waje tayi Tace "Tabd'ijam Baffa waya fad'a maka irin katangar ruga ce?, Kaga wasu wayoyi kuwa Randa fa Alhaji ya nunamin da k'adangare yahau mak'alewa yayi ya kasa fitowa sai gawarsa, yaushe Zan hau na mutu kucinye Wannan kud'in ta6, ai mu tafi kawai" gaba tayi tabarsu a wajan, yayinda Iyayanta suna tsaye sun kasa tafiya saboda yawan kud'in da suka manta dasu.
Baffa ne yace "Binafa, ansa sandar Nan ki shiga ta get ki kwaso kud'in Nan, nida nakeso bana Dani za'a aikin Hajji, idan Kika fito Mai gadin yak'i barki ki kwad'a Masa sanda Nina sakaki"
Binafa tace "A'a Baffa, karfa Wannan watan shine na tonon asirinmu, kawai mu tafi Tasha, Wannan Karan wani gari Zamu nufa?"
Inno cewa tayi "Haka Zaki hak'ura kije ki kwaso kud'in Nan saboda garin da zamu nufa suna da tsadar rayuwa, ke Kanki kinsan gida me kyau Mai tsada muke Kama haya"
Binafa turo Baki gaba tayi Tace "kuje Tasha ku jirani Ina zuwa"
Ba musu suka tafi tare dayi mata fatan samun nasara.

Anguwar da aka kaita ta nufa anguwace ta keta raini, Wannan Yana wane Wannan, gidajene tsararru nagani na fad'a, tuni ta nufa gidan tafi ko wani gida kyau a anguwar, tana zuwa ta fara knocking saiga Mai gadi yazo ya bud'e, sosai yayi mamakin ganin ta a waje, had'e fuska Binafa tayi tace "Zaka matsa kabani hanya ko sainabi ta kanka ka saki Baki da hanci sai kallo na kake sai kace baka ta6ayin arba da farar mace ba" ta fad'a tana bangajeshi ta wuce.

Tsaki yaja yace "Koma menene ai Alhaji ne yaja, da girmansa zaije ya auro 'yar k'aramar yarinya wacca Bata wuce sa'ar autar 'yarsa ba yace Wai zai aura Dan ganta bafulatana, Allah yasa ba k'yalk'yal banza ya kwaso ba, jibeta sai kace ba jiya da daddare aka kawota ba saboda wauta irin tata harta fice da asubar Nan waya sani ma Wasa tajeyi da Yaran mak'ota" ya fad'a Yana dariyar mugunta.

Binafa duk ta gamajin abunda yace tuni ta kwashe da wata irin dariya, shiga ciki tayi tana fad'in "Kaga ka bani satar amsa, Wato ni akema kallon k'aramar yarinya basusan wayo na ya wuce na babbar mace ba" ciki ta kutsa kasancewar gidan ita kad'ai ce sauran matansa kuwa suna can d'ayan gidanshi, tana shiga bedroom d'in taga inda tabar Alhajin sai sharar bacci yake harda munshari, k'yalk'yalewa tayi da dariya Tace "Su Alhaji Kenan Wannan bacci Haka, Koda yake shine yafi dacewa dakai a halin yanzu, in Banda abun namiji Yanzu da na zauna saiyace zai haik'emin 'yar k'arama ta Dani daya kasheni" ta fad'a tana dariya, kallansa ta k'arayi Tace "Wai buhu Kenan..."
Ganin yayi motsi yasa cikinta k'ullewa tsoro da fargaba suka dirar Mata, ganin ya cigaba da baccin sa yasata tsallake sa ta d'ibo kud'in, harta zata fita ta hango wayarsa saman bedside drawer, tace "Hu Wannan iPhone d'in Mai kama da kwakwa bazata wuceni ba, yama sunanta ake ce Mata, uhm na Manta" Zama tayi dirsham ta cire Masa SIMs d'insa ta fito abunta hankali kwance.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now