*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*31**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_**Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason haɗa akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1QƘarasawa inda Ahmad yake yayi a kwance rai a hannun Allah, cikin tsananin tashin hankali ya kalli Ahmad da mahaifiyarsa na ruƙe dashi yana fitar da wani irin numfashin wahala, ganin Safwan yasata fashewa da kukan data maƙale tace "Shikenan zan rasa ɗa ɗaya tilo na, Safwan Ahmad yaƙi ya tashi a tafi dashi Hospital, yau kimanin kwananshi shida kenan yaƙici yaƙi sha"
Safwan runtse idonshi yayi ganin yana ƙoƙarin zubda ƙwalla, cikin ƙarfin hali ya kama hannun Ahmad yace "Haba Abokina, ya kake wani abun kamar ba namiji ba?, koka manta kaiɗin wanene na tuna maka?, please ka daure ka tashi, Mama na buƙatarka, Husnah, Haajara na buƙatarka haka zalika Binafa tana tsananin buƙatarka, dan Allah ka yarda a kaika Hospital, uhum Be a Man, my Man"
Kallan wani matashi yayi ga dukkan alamu ƙanin mahaifiyar Ahmad ne, yace "Please tayani mu fitar dashi"
Ba musu yazo ya tayashi, ganin Ahmad ya yadda a kaishi asibiti kowa na gidan fuskarsa ta cika da annuri.
Abun kamar wasa tunda suka dira asibiti likitoci suka fara yi musu faɗan gaske akan sakacin da sukayi har saida mara lafiya ya galabaita, domin kuwa Ahmad babu abunda yakeyi sai suma, da zaran ya farfaɗo saiya koma saboda tsananin ciwon da yakeji da kuma yunwa data addabeshi.
Daƙyar aka samu numfashinsa ya daidaita, dare da saka mishi drip ɗin cin abinci da duk wani maguna da yake buƙata, a iya binciken likitocin sun gane Ahamd yana cikin damuwa mai tsananin gaske tare da fargaba, nan suka kafa kashedi akan lallai idan Ahmad ya tashi ayi ƙoƙarin kawar masa da damuwar datake damunsa, sosai Mahaifiyar Ahmad tayi mamakin jin cewar yana cikin damuwa, don koda wasa bata taɓa kawo hakan ba dangane da ciwon da Ahmad ɗin yake, han Safwan gefe tayi dan tana da tabbacin bazai rasa sanin abunda ke damun Ahmad ɗinba, kallan Safwan tayi dakyau tace "Safwan inaso ka faɗamin gaskiya damuwar me Ahmad yake ciki ni mahaifiyarsa ban sani ba?, yanzu har zurfin cikin Ahmad yakai ya ɓoyemin babban abunda ke damunsa a rayuwa har yana ƙoƙarin illatashi, dan Allah Safwan ka taimakeni ka faɗamin menene wannan"
Numfasawa Safwan yayi yace "Mama a zahirin gaskiya bansan taka maimain abunda ke damun Ahmad ba, amma nai miki alƙawarin inhar ya farfaɗo zan tambeyasa koma menene, kuma inada tabbacin zai faɗamin, dan haka ki kwantar da hankalinki"
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Safwan tana nazari, tace "Amma ɗazu naji ka ambata sunan wata mace wacece ita a wajansa?"
In-ina Safwan ya farayi yace "Mama ƙanwatace, idan yazo suna ƴar zolayar juna shiyasa na tuna mai da ita"
Ɗaga kanta kawai tayi badan ta yadda da abunda Safwan yace ba"
Kallan ƙofar da aka kwantar dashi tayi taga jami'an tsaro duj sun gewaye ɗakin, ga uban bindiga a hannunsu, kallan Safwan tayi tace "Yau zaka tafi ne?"
Zaro idanu waje yayi yacs "Ina zani Mama?, Alhalin kinsan Ahmad bashi da lafiya"
Murmushin jin daɗi tayi tace "Shikenan, ka zauna nan bari naje gida na haɗo muku Dinner"
Safwam yace "Mama da kin barshi inyaso sainai mana Takeaway"
Girgiza kanta tayi tace "A'a baza ai haka ba, ai koba komai yaka mata naje naga yarana"
Gyaɗa kanshi yayi, ba tare daya ƙara cewa uffan ba, ya rakota waje har bakin motarta sannan ya juya ya shiga ciki.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...