Page 32

211 22 13
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *32*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1Q

Sosai akai ta hidimar biki bayan ɗaurin aure, Binafa tana can ƙurar ɗaki ta haɗa kai da gwiwa sai kuka take, yanzu ta tabbata Safwan shine mijin data aura, share hawayanta tayi tana ganin haka Allah ya tsara lamarin, Lanika ce ta turo ƙofa taci uban gayu kana kallanta kaga amarya, kallan Binafa tayi wacca tana kan gado tace "Me zan gani haka?, wai bazaki tashi ki shirya ba?, kinga fa lokaci nataja, kizo ance Maman Ya Ahmad tazo tanason ganinki"
Gaban Binafa ne yayi mummunan faɗuwa tace "Wani Ya Ahmad ɗin?"
Cike da ƙosawa Lanika tace "Abokin Ya Safwan mana, ki maza ke suke jira"
Jikin Binafa a matuƙar sanyaye ta tashi ta buɗe ɗan kit ɗin da aka kawo mata ta saka kaya, sosai kayan suka zauna a jikinta kuma sukai mata kyau matuƙa, powder ta shafa sai lipstick, ɗan kwalin ta ruƙe ta kasa ɗaurawa sai kawai ta yafashi akanta ta fito kanta a ƙasa.
Tana fitowa wata ƙawar Lanika ta fara buɗi nan hankulan mutane yayo kansu, murmushi kawai Binafa tayi tana mai matuƙar farin cikin wannan ranar koba komai yau tayi auran gaske kuma a cikin danginta, daƙyar ta samu ta ƙarasa wajan saboda mutanan da suka zuba mata ido, wasunsu da dama basu taɓa ganinta amma sunajin labarinta, hangosu Lanika datayi yasata saurin ƙarasawa tana ƙoƙarin faɗuwa, dafa Lanika tayi tace "Twins Sis wallahi kamar zan faɗi haka nakeji"
Cire hannunta tayi a kafaɗarta tace "Amma wallahi bako da kirki, yaufa ranace mai matuƙar muhimmanci a gareki amma ki garara yin kwalliya yadda yaka mata kamar ta amare, dan Allah jibeki ko a cikin ƙawayan nan sun fiki cin gayi nesa ba kusa ba"
Yatsina fuska Binafa tayi tace "Nifa banajin daɗin jikinane ko kaɗan wallahi, shiryawarnan danayi ma ta dolece, ina baƙin suke?"
Ta tambayeta tana faman lumshe ido kamar maijin bacci, harara Lanika ta jefeta dashi tace "A haka zankaiki?, kamata yayi kije ki ɗaura ɗan kwalin kanki kin wani ɗaurosa aka kamar kin samu gyale"
Dariya Binafa tayi tace "Sis badai daru ba, nidai dan Allah muje mu dawo koma menene saiki tayi"
Girgiza kai Lanika tayi tace "You will never Change wallahi"
Bin bayanta Binafa ta farayi tace "Naji dai"
A haka har suka ƙarasa ɗakin baƙi inda akaima Mahaifiyar Ahmad masauki.
Tana shiga ta hangota ko ba'a faɗa mata ba tabbas wannan itace mahaifiyarsa domin komi nasu sak hatta farin, da fara'a ta taresu tace "Wannan ce Binafar?"
Ta tambayi Lanika tana murmushi.
Lanika cikin zolaya tace "Kinga batai kala dasu bako"
Binafa shiru tai musu murmushi shinfiɗe a fuskarta, waje ta samu ta zauna, Lanika itama ta zauna, kallan kayayyaki da aka kawo mata tayi tace "Laa Mama ya naga bakici komai ba"
Murmushi kawai Mahaifiyar Ahmad tayi tace "Tayaya zanci alhalin banga ɗiyata ba"
Binafa Sadda kanta ƙasa tayi tana murmushi tare da jan ɗan kwalin kanta ta rufe fuskarta.
Jin an fara knocking ɗin ɗakinne yasa Lanika tashi taje ta buɗe, Umma ce tace anason ganin Binafa, ba musu Lanika taje ta shaidawa Binafa dama Binafa kamar akan ƙaya take, cikin hanzari ta tashi tabar ɗakin.
Tana fitowa Umma taja hannunta tace "Ta ƙofar baya zakibi, ga motacan Daddy ya turo yana son ganinki"
Marairaice Fuska tayi tace "Umma yanzu dan Allah gun Daddy zani?"
Murmushi tayi tace "Ai Driver ɗin zai jiraki ya maido dake nan gidan"
Murmushi tayi tace "Tom shikenan, kun gaisa da Maman Ya Ahmad kuwa?"
Umma harararta tayi tace "Nina fara ganinta kafin ke"
Murmushi Binafa tayi, tai gaba abunta, ta ƙofar baya ta nufa tana zuwa ta hango motar da zata ɗauketa, shiga tayi aka jata.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now