*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*18**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Safwan ne yazo yaga Binafa ita kaɗai, kallan inda yabar motar Ahmad yayi yaga babu ita, kallanta yayi yace "Ina Ahmad ɗin?"
Ko kaɗan Binafa bata masan yazo ba balle har taji abunda yake faɗa, sunanta ya kira da ɗan ƙarfi, a firgice ta juyo taga Safwan ne, murmushi tai masa tace "Wallahi banji ba Ya Safwan, muje ko"
Kallan tuhuma yayi mata yace "Ina Ahmad ɗin?"
Muzurai ta farayi tare da in-ina tace "Am...umm... Auh...." kwata-kwata ta rasa mema zatace ma Safwan, kallanta yayi yace "Ki saurara Binafa ki faɗamin maiya faru, naga duk kin wani firgice ne"
Sosa ƙeya tayi tace "Wallahi Ya Safwan bansan maiya faru ba kawai naga ya tafi ne yace in faɗa maka zakuyi waya"
Safwan yace "Binafa ko kin mishi laifine?, nasan akwai abunda ya faru a tsakaninku haka kawai Ahmad bazai kama hanya ya tafi har Adamawa ba, ba tare da yayimin sallama ba"
Shiru Binafa tayi tanaso ta nemo kalmar da zata kare kanta, ta buɗe baki zatayi magana kenan saiga su Alhaji Lukman, sassanyar ajiyar zuciya tayi, kallansu tayi tana duƙar da kanta ƙasa.
Waige-waige Alhaji Modibbo ya farayi yana faɗin "A'a ina Amadun yake?"
Murmushi Safwan yayi yace "Wani kiran gaggawa akai mishi shine ya tafi tare da baku haƙurin cewar inya gama abunda yake zai leƙo Kanon"
Alhaji Lukman ne yace "Allah ya taimaka" kallan Alhaji Modibbo yayi yace "Yaya muje", jerawa sukai suna tafiya suna hira irinta Yaya da ƙani.
Murmushi Safwan yayi yace "Shiga ciki zamuyi waya anjima..."
Kasa ƙarasawa yayi ganin Maryam matar Sultan tazo gidan tana tafiya tana yauƙi sai ka rantse cewar itaɗin ƴar shugaban ƙasa ce, cikin ƙasan maƙoshi Safwan yace "Ga munafuka nan"
Binafa kallanshi tayi tace "Ya Safwan me kace?"
Kallanta yayi da sexy eyes ɗinsa yace "Babu komai, wannan itace matar Sultan babban yayanku"
Kallanta tayi, haka kawai taji bata kwanta mata arai ba, yatsina fuska tayi tace ma Safwan "Ya mu shiga ciki" suna ƙoƙarin tafiya ne Maryam tai saurin shan gabansu tana wani washe haƙora kamar wata sauna tace "Ya Safwan ina ƙanwar tawa take ne?, kardai kacemin itace wannan" ta faɗa tana nuna Binafa.
Binafa fuskarta babu yabo babu fallasa tace "Ina wuni?"
Washe baki tayi tace "Lafiya ƙalau, ya baƙunta?, kai ai nayi farin cikin ganinki da akayi yadda bakya tsammani"
Safwan ne yace "Bari nai gaba" ɗaga mishi kai kawai tayi tare da bin bayanshi da kallo.Maryam kama hannunta tayi tana murmushi tace "Allah ya tabbatar mana da alkhairi"
Sadda kanta ƙasa tayi tana murmushi, a haka har suka ƙarasa cikin main parlour ɗin ɗakin.
Tunda Mommy ta hango Binafa da Maryam hankalinta bai kwanta ba, amma yaya zatai, Maryam tazo har inda Hajiya Hauwa take ta tsugunna tace "Ina wuni?"
Fuskarta a sake tace "Lafiya ƙalau ina Mijin nawa yake?"
Murmushi tayi tace "Yana gida na baroshi wajan Daddy ɗinsa"
Gyaɗa kanta tayi tace "Inkin koma ki gaishemin dashi" tashi tayi ta hau Upstair tana waiwayansu dan ita harga Allah bataso Binafa da Maryam su keɓe waje guda.Maryam cike da zumuɗi ta zauna kusa da Binafa tace "Soyayya kuke keda Ya Safwan?"
Kallan mamaki Binafa tabita dashi tace "Eh"
Murmushi Maryam tayi tace "Amma dana shigo naga kamar ranshi a ɓace wani abun yayi miki?"
Girgiza kai Binafa tayi tace "Ko kaɗan, akan wani abokinsa ne Ahmad yace yana sona, ni kuma abun ya bani mamaki, sai yayi zuciya ya tafi, shine fa yazo yana tambayata ko naimishi wani abune yayi zuciya ya tafi"Maryam girgiza kanta tayi tace "Ahmad dai wanda nasani Best Friend ɗinsa?"
Ɗaga kai tayi alamun "Eh"
Numfasawa Maryam tayi tace "Kinsan mai yasa yakejin tsoron ko yayi miki wani abune?"
Girgiza kanta tayi alamun "A'a"
Maryam cike da jimami tace "Yana tsoron karya lalata ki kamar yadda suka saba ɓata ƴan matan su, shiyasa yake tsoro, kinsan fa Ya Safwan da Ahmad mugayan bunsurayene shegen bin matane dasu"
A zabure Binafa ta tashi jikinta na rawa tace "Ya Safwan ɗin"
Miƙewa Maryam tayi tace "Ƙwarai kuwa, kuma zaki gani nan bada daɗewa ba, shawarar da zan baki kiyi shiru da bakinki zaki ga komai nina faɗa miki, amma dan girman Allah karki faɗawa kowa"
Hawayene suka wanke fuskar Binafa ta tashi a aguje tabar parlourn.*Yau banda caji wallahi, kuyi mugun maneji da babu gwanda ba daɗi*
*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes**Follow me on Wattpad-MumIrfaan*
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...