Page 29

154 17 3
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *29*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Alhaji Modibbo saurin dakatar dashi yayi ganin zayyi magana ranshi a ɓace, cikin sanyin murya yace "Tunda nake dakai Lukman baka taɓa yimin musu ba, dan haka banaso akan yaran nan ka fara yimin, na yanke shawarar dawo da bikin nan da wata ɗaya za'ayi tare dasu Mahmud dan haka kaje kayi shirye-shiryen biki"
Lukman tausasa zuciyarsa ya farayi sannan ya kalli Yayan nashi yace "Ka gafarceni Yaya, domin na amsawa iyalan marigayi Alhaji Yusha'u Mai Goro akan su turo gashi Safwan yaje ya faɗawa wata yarinya akan zai turo magabatansa ya kakeso nayi da wa ƴannan mutanan?"
Alhaji Modibbo kallan Lukman yayi na ɗan wasu daƙiƙai sanna yace "Shi Safwan ɗinne yace zai turo magabatansa gidan budurwarsa?"
Ya faɗa yana kafe Alhaji Lukman da ido saboda gano gaskiyar lamarin"
Jinjina kai Lukman yayi yace "Tabbas Yaya domin munyi magana da mahaifin yarinyar idan kuma kana tantama ka kira Safwan ɗin ka tambayesa da kanka"
Shiru yayi naɗan wani lokaci sannan ya numfasa yace "Lukman kasan darajar alƙawari kuwa?, to kasani Auran Binafa da Safwan babu fashi saidai in dukkaninsu ne suka amsa da basason auran, amma idan ɗaya yanaso ɗaya bayaso to ina mai tabbatar maka tabbas sai an ɗaura aurannan, dan haka ka tashi ka tafi kawai, domin naga tsantsagwaran son da Safwan yakema Binafa, babu mamaki Binafar ce takeso ta rusamin komai kuma zan sameta"
Ya faɗa yana hura hanci saboda tsananin ɓacin rai.
Lukman dawowa yayi ya zauna yace "Ko kaɗan babu ruwan Binafa domin Binafa batama san meke faruwa ba, karka ɗauki haƙƙinta Yaya dan Allah"
Alhaji Modibbo yace "Shikenan, tashi ka tafi"
Alhaji Lukman yana fita, Alhaji Modibbo ya ɗauko wayarsa nan take yayi umarnin da Safwan da Binafa suzo Parlournsa.
Cikin girmamawa Safwan ya amsa, kallan Ahmad yayi yace "Ina zuwa Daddy ke kirana,ka shigo ciki mana inba damuwa"
Ahmad haka kawai yaji kiran da Alhaji Modibbo yakema Safwan yasa gabanshi faɗuwa, gashi yaga sanda Uncle Lukman ya fito ranshi sam babu daɗi harda hararan Safwan ɗin, kasa zama yayi ya shiga cikin gidan, yana shiga yaci karo da Binafa itama tana ƙoƙarin shiga part ɗin mahaifin nata, cikin sauri-sauri ya isa gareta yajata wani ɗan lungu hannunsa kan kafaɗarta yace "Please ki faɗamin wai meke faruwane?, naga Safwan yanzu ya shiga kema naga zaki shiga" kallanta yayi ido cikin ido tare da sauke hannayansa ƙasa yace "Dan Allah!" sai kuma yayi shiru, wani irin saƙo ya cilla mata cikin ƙwayar idonta, cikin muryarsa mai daɗi yace "Binafa dan Allah karki bari a rabani dake dan Allah, inna rasa ki bansan a wani irin hali zan shiga ba"
Binafa gyara Veil ɗin kanta tayi ganin yana ƙoƙarin zamewa tace "Ya Ahmad!, dan Allah ka runƙa sakawa ranka cewar insha Allahu ni mallakinkace, karka damu kamar yadda koda yaushe zuciyata ke tunaninka haka ma yanzu zan shiga cikin ɗakin Daddy da ruhinka ne in runƙa gani ina matuƙar samun ƙwarin gwiwa, ka sani gangar jikinka ce kawai a waje" takunta ta farayi cikin ƙasaita ta waigo ta kalleshi tace "I love you" da wani irin salo ta faɗa kalmar wanda saida numfashi Ahmad ya ɗauke na hucin gadi.
Murmushi kawai yayi mata duk da hankalinshi ko kaɗan bai kwanta ba, yana kallanta harta shiga Part ɗin.
Ajiyar zuciya ya sauke ya nufa inda motarsa yake domin yasan idan ya tsaya jiran Binafa ƙiris zuciyarsa zata buga,
Jiki a sanyaye ya tuƙa motarsa yabar cikin gidan yana maijin tausayin kansa.

Binafa da Safwan ne durƙushe wajan Alhaji Modibbo, kallansu yayi dakyau sannan ya dawo dubansa ga Safwan yace "Da gaskene kunyi magana da wata akan zaka turo magabatanka?"
Ya faɗa yana mai kallan Safwan ɗin.
Safwan sosa ƙeya yayi yace "Daddy lokacin kafin aga Binafa ne, kuma ni tunda aka ganta na manta da zancan yarinyar"
Kallanshi yayi dakyau yana nazari yace "To Mahaifin yarinyar ya Kira Uncle ɗinku akan maganar da kukai da ita, mai yasa tun farko baka sanar da ita ba?"
Kan Safwan a ƙasa yace "Wallahi Daddy sam na manta ne shiyasa amma dan Allah ayimin afuwa"
Shiru Daddy yayi yace "Yanzu tsakanin itada Binafa wa zaka aura?"
Safwan yace "Daddy Ni Binafa kawai nakeso, dan Allah aba mahaifin yarinyar haƙuri"
Wani banzan kallo Binafa ta jefeshi dashi tareda taɓe bakinta, maida kanta tayi tana sauraransu.
Daddy kallan Binafa yayi fuskarsa ko kaɗan babu fara'a yace "Kece kika turomin da Uncle ɗinku ko?"
Ganin yanayin mahaifin nata ko kaɗan babu fara'a yasat daburcewa tace "Daddy nifa bansan meke faruwa ba, nidai nasan Ya Ahmad yace nayi muku magana yanaso ya turo magabatansa, daganan kuma ni bansan komai ba......"
Saukar marin dataji a kuncintane yasata kasa ƙarasa maganarta, cikin tsananin fushi Modibbo ya nunata da yatsa sai kuma ya kasa cewa Uffan, kauda kanshi gefe yayi yace "Tashi ki bani guri, kuma ki sani aure babu fashi tsakaninki da Safwan, mutuniyar banza kawai da ita"
Binafa tashi tayi hannunta dafe da kuncinta tabar ɗakin a zuciye.
Safwan sauri yayi zai bita Alhaji Modibbo yace "Zauna, kana jina, kayi shiru da bakinka akan maganar auranann ko Uncle ɗinku kar in sake inji ka faɗa mishi, nan da sati uku ka fara shirye-shirye na fasa wata ɗayan ma"
Sosai Safwan yayita mishi godiya farin ciki kamar zai shiɗe.
Fitowa yayi cikin sauri sai kuma ya tsaya jin kukan Binafa da yayi a wani corridor na cikin gidan.
Jiki ba ƙwari ya ƙarasa inda take yaga kuka take haƙiƙan, cikin sanyin murya Safwan yace "Binafa dan Allah..."
Kallanshi tayi da idanunta wanda sukayi jajir saboda kuka tace "Ya isa, wallahi ko zan mutu bazan aureka ba, kai koda an ɗaura mana aure wallahi saidai na shekara da auranka akaina amma ban zama a cikin gidannan guduwa zanyi, ina mai shawartarka tun wuri ka janye wannan maganar auran nan wallahi bana ƙaunar zama dakai da aure"
Tana gama faɗan haka ta bar mishi wajan ta nufa bedroom ɗinta ta fara rera kuka mai ban tausayi.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now