Page 38

268 25 13
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *38*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1Q

Bayan su Safwan sun gabatar da sallah shida amaryarsa, kayan maƙulashe da gashashshiyar kazarta ya tasa mata a gaba akan dole sai ta cinyeshi tas, Husnah badan ranta yaso ba ta fara tusashi kaɗan kasancewar cikinta a cike yake, ƙadan ta samu taci ta haɗa da Drink ta tashi ta Nufa Bathroom danyin wanka saboda wani irin zafi takeji.
Bayan ta fito ne Safwan shima ya shiga ya watsa ruwa, yana fitowa yaga har Husnah ta kwanta, kallanta yayi yay murmushi yace "Yaka mata ki canza kaya wannan kayan sun miki nauyi bakiji garin da zafi bane?"
Shiru Husnah tayi ƙirjinta na faman bugawa da ƙarfi da ƙarfi, Safwan akwatinta ya zuge ya firo mata da wata doguwar rigar Night Gown yace "Tashi kisa"
Jin Voice ɗinsa babu alamun wasane yasata tashi ta samu Hijab ta shiga ta canza kayanta, abun ba ƙaramin dariya yaba Safwan ba amma saiya maze.
Tana gama sakawa ta rarrafa ta haye gado ta kwanta, kasa guntse dariyarsa yayi yahau yinta ba ƙaƙƙautawa ganin yadda take abu kamar ba wayayyiya ba kamar ba ƴar Kaduna ba.
Girgiza kai yayi murmushi shinfiɗe a fuskarsa ya tashi yaje ya kashe musu Bulb ya dawo shima ya kwanta tare ta rungumo ƴar amaryarsa, tuni labari ya fara canza salo a wajan Safwan, Husnah kuwa ta gama tsorata sai kyarma kawai takeyi, yayinda Safwan baima san tanayi ba dan ya fita daga hayyacinsa.
_Ba shiri na fito daga ɗakin nabarwa amarya da ango ɗakinsu domin suyi nasu sirrin_

*Agurguje*
Binafa daƙyar takejan cikinta saboda tsananin girman da yayi haihuwa ko yau ko gobe, sosai Ahmad ke tsananin tausayinta ganin yadda cikin ya canzata kamar ba ita ba gashi tai wata irin ƙiba wacca ko kaɗan batai mata kyau ba, daƙyar take tafiya ta kalleshi tace "Ya Ahmad na shirya"
Cike da tausaya mata yace "Binafa kodai zaki haƙura da zuwa sunan Lanika ne?, nai miki alƙawari bayan kema Allah ya saukeki lafiya zan kaiki Kano kiyi sati biyu acan"
Tuni ran Binafa yayi matuƙar ɓaci dama tunda cikinta ya tsufa abun kaɗan ke ɓata mata rai, tashi tayi daƙyar tabar wajan tare da yarda jakarta ta shiga ɗaki ta fara rusar kuka da kusan kullum ya zame mata jiki, data share hawayan da wani ya biyo baya, Ahmad biyo bayanta yayi yace "Tashi muje"
Banza tai dashi tare da gyara kwanciyarta ta cigaba da kukanta, Ahmad kafeta yayi da kyawawan idanunsa yace "Kiyi haƙuri nace ki tashi mu tafi ɗin"
Daƙyar ta tashi ta shiga Bathroom ta banko bayin ji kake "Gagaaam" girgiza kai kawai Ahmad yayi ganin yanzu ba wuya Binafa tahau dokin zuciya dashi, tashi yayi ya nufa Office tare da ba wata ƴar tsohuwa da aka kawowa Binafa saboda anga cikinta ya tsufa yace "Baaba dan Allah da kinga yanayin Binafa ba daidai ba ki kirani, cikin kullum sai ƙara girma yake amma haihuwa shiru"
Dariya Baaba tayi tace "Idan lokaci yayi sai kaga anyi an gama harta haihu, mudai fatan mu Allah ya sauketa lafiya"
Ahmad cike da sanyin jiki yace "Ameen Baaba, bari na tafi Office anjima insha Allahu zan leƙo"
Baaba tace "A'a kun fasa zuwa Kanon ne?, naga tun jiya mutuniyata take taimin zancan zuwa Kano"
Ahmad yace "Baaba nace ta haƙura dama a cikin garin nanne da sauƙi zan iya kaita, Kano da Adamawa fa da nisa ba kaɗan ba"
Baaba tace "Kaima kai ganganci Amadu, tayaya zakai mata alƙawarin zuwa suna har Kano gata da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe, Allah yasa mutuniyar batai fushi dakai ba, domin kwana biyu da an mata abu datahau kamar wata bread"
Dariya kawai Ahmad yayi ya fita daga Parlourn ba tare dayace uffan ba.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now