*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*11**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Ahmad runtse idanu yayi yanajin sautin kukanta har cikin ransa, cikin daddaɗar muryarsa yace "Binafa!"
Binafa gabanta ne yayi mummunan faɗuwa dan zata iya rantsewa babu wanda ya iya kiran sunanta saishi, saidai tagaji wannan ba muryar Safwan bace shiru tayi bata amsa ba, sai sautin kukanta dake fita kaɗan-kaɗan.
Ahmad shiru yayi yanajinta, ya rasa mema zaice mata wanda zai kwantar mata da hankali, shi kwata-kwata hankalinsa ma ba'a jikinsa yake ba, cikin ƙarfin hali yace "Dan Allah Binafa ki daina kukan nan..."
Bata bari ya ƙarasa ba tace "Ina mai wayar?"
"Ya fita"
"Dan Allah kuna ina yanzu?"
Ahmad duba ɗakin da yake yayi, ganin a cikin ɗakin Hotel yake, shiru yayi yace "Muna wani wajene, kuma bai kamata kizo wajan ba..."
Katse mai magana tayi ta hanyar faɗin "Kai wanene?"
"Wani ne...."
Ƙit yaji an kashe wayar, bin wayar yayi da kallo, haka kawai ya tsinta kanshi dayin murmushi, ajiyar wayar yayi, wayarsa ya ɗauko ya fara copy ɗin Numbern Binafa a wayarsa, yana gamawa ya maida wayar ya ajiye tare da lumshe idanu.*Gidan Sultan ɗa ga Alhaji Madibbo*
Hannu ya ɗaura aka ga dukkan alamu yana cikin tsananin tashin hankali, yayinda wasu mutane a ƙalla zasukai uku suna zaune, kana kallon fuskarsu zaka tabbatar da zallar rashin mutunci ne a tattare dasu, yayinda matar kuma tana gefe a rakuɓe ga dukkan alamu bata da gaskiya a cikin zaman da ake, Sultan ne ya ɗago da fuskarsa ko kaɗan babu fara'a yana duban matarsa, ga idanunsa sunyi jajir yace "Wai Maryam yaushe zaki daina janyomin magana?, ace yanzu kowa yasan ke Munafukace, ace Family ɗina tun daga kan maza har mata ansan ke Munafuka ce dan Allah ribar me kikeci idan kikayi munafunci?, yanzu abun naki harta kai har a Media baki bar yin ƙarya da gulma ba, yanzu maye amfanin haka kinsan mutane sunzo sun tsaya akanmu suna faɗan abubuwan da sukaga dama, gaskiya ki kiyaye na gaji da wannan gulmammanki da kikeyi, ni wallahi bansna haka kike ba sai yanzu, ke ko kunya bakya ji"
Shiru tayi kanta a ƙasa tamkar wata mumina, yayinda wata tayi caraf a cikin mutanan da sukazo tace "Wallahi taci darajarka daba haka ba da sai mun saka an kulleta a Police station gobe koda ance tayi gulma bazata yiba"
Sassauta muryarsa yayi yace "Dan Allah kuyi haƙuri zan ɗauki mummunan mataki akan haka, ku yafe mata insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba"Shiru sukai, domin ba haka sukaso ba, wata budurwa a cikinsu tace "Ai wallahi kinci darajar masu daraja kuma kinci darajar Ya Sultan, amma kinga wannan ɗan mitsitsin ƙugun naki wallahi yau da saina ɓallashi, banza munafukar banza munafukar hofi" hand bag ɗinta ta ɗauka, tayi waje a zuciye dan ba haka taso ba, taso ace basu samu Sultan ba suyi mata shegen duka.
Suma sauran bayanta sukayo, yayinda Sultan yabi bayansu yana ƙara basu haƙuri, daƙyar ya samu suka haƙura, ya juya ciki ransa ko kaɗan babu daɗi, dan yaga alamu Maryam tanaso girmansa ya zube a cikin jama'a, haka kawai baiji bai gani ba.
Me gadi girgiza kai yayi yace "Alhaji ya aurowa kanshi bala'i da masifa ace kullum shine bada haƙuri, matarshi ita kuma itace mai haɗa gurmi, kai Allah ya kawowa Alhaji agaji"Yana shiga cikin gidan tai sauri ta miƙe tanaso ta kare kanta kamar yadda da saba ta kissa da kisisina, ganin ranshi a ɓace, yasata ƙoƙarin saita kanta tace "Baban Ishaq, ka saurareni wallahi sharri sukaimin ƙaryane..."
Dakatar da ita yayi da hannunsa yace "Ya isa Haka Maryam, na gaji wallahi idan bakiyi gaggawar dainawa ba gab nake da rabuwa dake dan bazan iya cigaba da zama da munafuka ba kuma makira, kafin na fargaba da uban waye baki haɗani faɗa ba, haffa ƙannina da ƴan uwana nasha yin faɗa dasu akan yadda zaki ƙirƙiri labari ki faɗa kuma na yadda dake, dan haka daga yanzu komai ya ƙare kiyi karatu tanatsu, mai yasa da suka faɗa agabanki baki musa ba sai yanzu da kikaga sun tafi, kuma kiyi gaggawar bani wayarki daga yau babu ke babu hawa Online, sai ki zaɓa auranki ko hawa online" bai jira cewarta ba ya fice daga gidan gabaki ɗaya ranshi babu daɗi.
Maryam kuma babu nadama a tattare da ita ƙwafa tayi ta juya ta nufa ciki ranta sam babu daɗi ganin wannan karan batai nasara akan Mijin nata ba.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasiBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...