page 15

212 22 19
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *15*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Ahmad kallan Hajiya Hauwa yayi cikin dakakkiyar muryarsa yace "Inada hanyar da za'a ganta cikin sauƙi"
Gabaki ɗaya tsayawa sukai cak jin abunda Ahmad yace, lumshe idanu yayi yace "Ƙwarai kuwa, domin ta hanyar nan ne  na sameta cikin sauƙi"
Alhaji Lukman ne yace "Ko zakai mana ƙarin bayani?"
Kallan Safwan yayi sannan ya kalla Hajiya Hauwa yace "A yau idan kuna da buƙatar ƴarku zaku ganta, saidai wani hanzari ba gudu ba, dole abun a sannu ni jikina ya bani Baffah ba haka suka bar Binafa ba"
Shiru akai ana sauraransa, miƙewa yayi yace ina zuwa, ɗakin su Mahmud ya nufa kasancewar kayanshi nacan, kwalin wayar ya ɗauko ya miƙa ma Alhaji Modibbo yace "Da wannan wayar take amfani, wannan kwalin wayar ne, yanzu za'a iyayin tracing wayar dan asan inda take"
Gaba ɗayansu babu wanda baiyi ajiyar zuciya ba, Hajiya Hauwa kuwa saboda farin ciki kasa magana ma tayi.
Sai kallo kawai databi Ahmad dashi tana mishi murmushi.
Safwan kuwa danƙar hannunsa yayi da ƙarfi, Ahmad yana juyowa ya kallesa yayi mishi murmushi tare da jinjina mai.
Alhaji Lukman ne ya amsa kwalin wayar, yayinda taron ya watse kowa zuciyarsa wasai, Ahmad da Safwan ma fitowa sukai wajan Balcony, Safwan kallan Ahmad yayi yace "Abokina banda bakin da zan gode maka nagode ƙwarai da gaske Allah yabar zumunci"
Murmushi kawai Ahmad yayi zuciyarsa sam babu daɗi, yasan inhar Binafa ta dawo Familynta to tabbas ko kallo bai isheta ba saboda yadda yasan tanason Safwan so mai zafi, kallan Safwan yayi yace "Abokina saboda kai nai hakan, domin kuwa tun muna Secondary School kake yawan yimin maganar Binafa, in baka mallaketa ba kai a tunaninka wazaka mallaka?" ya ƙarashe faɗa cikin ɗacin rai tare da haɗiye wata Saliva daƙyar daga maƙogaransa.
Safwan dafashi yayi yace "Bazan manta dakai ba abokin ƙwarai tabbas kai abokine nagari"
"Hmmm" kawai Ahmad yace, yayinda ya juya ya nufa ɗakin Mahmud ya ɗauko trolley ɗinsa, kallan Safwan yayi yace "Yau fa zan wuce, saboda wani uzuri ne ya tasomin cikin gaggawa"
Safwan cike da rashin jin daɗi kalmansa yace "Kamar yaya, bafa yau mukai dakai zaka tafi ba"
Yaƙe yayi mishi yace "Nasani, na faɗa maka uzirina"
Safwan yace "Toya maganar case ɗin Binafa?"
Murmushi Ahmad yayi yace "inta dawo gida ka kirani kawai" inda yayi parking ɗin motarsa ya nufa, tare da buɗe boot ya saka trolley ɗinsa, zuciyarsa sam babu daɗi, waigowa yayi yaga Safwan yana nan inda ya barshi tsaye, murmushi yayi mishi yace "Ka kulamin da kanka" bai jira cewarsa ba, ya tada motarsa yayinda Getman ya wangale mishi get ya fita daga cikin gidan, zuciyarsa Sam babu daɗi.

Tunda Alhaji Lukman ya fita ya samu akaimai bincike akan inda su Binafa suke yasa hankalinshi kwanciya, da farin ciki ya shigo gidan, yayinda Safwan yabi bayanshi cike da ɗokin jin abunda zaice, saida aka kira mishi Yayansa sannan ya sanar dasu duk abunda ya faru, nan yace yau zasu tafi, Alhaji Modibbo ne ya dakatar dashi yace a bari sai zuwa gobe, sannan bazamu tafi mu kaɗai ba, dole sai mun tafi da hukuma"
Safwan ne yace "Babu damuwa, idan zamu wuce zan kira Ahmad sai ince mu haɗu tacan"
Kowa saida yayi na'am da maganar, yayinda Hajiya Hauwa farin ciki ya cika zuciyarta, bayan kowa ya watse ta zauna ta fara tunanin yadda abunnan ya faru shekarun baya masu yawa.

*TUNA BAYA, MAFARIN CHAKWAKIYA*

Gabaki ɗaya gidan Alhaji Modibbo a ruɗe yake, musamman Alhaji Modibbi dayake ganin gab yake da rasa matarsa kuma uwar ƴaƴansa, yayinda kaf yaranta hankalinsu a tashe yake ganin wannan karan, haka Safwan shima gabaki ɗaya baya cikin hayyacinsa, ganin yadda kusan kullum sai Mommy tace, Abunda zata haifa inhar macace to ta zama tashi, kasancewar Allah bai taɓa bata ƴa mace ba, kowa kuka yake, Alhaji Modibbo ne kawai ke dauriya, daƙyar aka samu aka fitar da ita aka sakata a mota aka nufa da ita Private Hospital ɗib datake awo, asibitine mai kyau mai kuma tsada, tunda suka kaita suma likitocin suka kasa taɓuka komai duk da ƙwararrune a fannin, shiyasa suka bada shawara akan a nufa da ita General Hospital, suna zuwa akai Emergency da ita ganin yadda ta wahala sosai, ganin inhar ta cigaba dayin naƙuda za'a iya rasa ran uwar kona ƴar shiyasa, suka buƙaci Baffah daya saka hannu, babu ɓata lokaci ya saka hannu domin shima ya fison matarsa ta samu sukuni.
Basu ɓata lokaci ba suka shiga da ita ɗakin theater, cikin ikon Allah suka ciro mata kyakykyawar ƴarta ƙin kowa wanda ya rasa, basu ɗauki awa guda ba sai gashi an fito da ita, hannunsu ruƙe da Baby, tunda suka taho Safwan ya hangosu yayi saurin miƙa hannunsa dan a bashi Babyn, cike da farin ciki yace "Nasan mata aka haifamin"
Gabaki ɗaya dariya sukayi, suna tsokanansa, Alhaji Modibbo kuwa hankalinshi nakan matarsa, yayinda Hajiya Nafeesah hannunta ruƙe da itama tata Babyn mai suna Laninka wacca ta ɗanyi wayo.
Mahmud ne ya kalli Binafa yace "Umma yarinyar nan fa Matata ta biyo"
Kowa saida ya dara, nan sukabi bayan Doctor ɗin dan ganin inda aka kwantar da Mommy.
Suna zuwa aka basu gado kusa da wasu fulani, itama matarshi haihuwar tayi, kuma ga dukkan alamu C.S ɗin itama akai mata, kowa saida yayiwa Inno sannu da jiki, yayinda Inno ta amsa cike da farin ciki tana miƙa hannunta tana cewa "Muga jinjirar"
Bata sukayi tana fadin "Masha Allah sai kace nina haifeta itama kyakykyawa da ita"
Murmushi sukai, Hajiya Nafeesah ce tace "Me muka samu kema"
Miƙa musu Binafa tayi tace "Wallahi nima ɗiya macace" karɓanta tayi tana mata addu'a, kafin kace me fira tsakaninsu dasu Inno ta ɓarke, kasancewar Kande ce a wajan Hajiya Hauwa, sosai suka shaƙu da juna har Inno take labarta musu bata taɓa haihuwa ba sai akan Binta kasancewar sunansu ɗaya da Binafa, kuma ta shaida musu ance bazata ƙara haihuwa ba saboda mahaifarta, sosai Su Hajiya Hauwa suka tausaya mata, Kande tace "Allah ya rayata, ai in Allah ya baka mai albarka sai kiga kamar ka haifi dubban al'umma"
"Ameen" Inno tace, kasancewar safiyar ranar gabaki ɗaya jikinta yayi mugun sanyi ta rasa dalilin haka, wunin ranar dai sukuku tayi shi.
Ana kiran sallahr ishsha zata ɗauki ƴarta ta bata Nono taji jikinta ya saki, sosai cikinta ya kaɗa, ta fara dubata nan take ta tabbatar da Allah ya karɓi ranta, komar da ita tayi ta kwantar tamkar mai rai, ta nufa inda Baffah yake kwanciya a asibitin, nan ta shaida masa cewar ƴarsu ta rasu, gabaki hankalinsu ya tashi musamman Baffah daya ɗaurawa ɗiyar son duniya, cikin tashin hankali yace "Kinsan me zamuyi?"
Girgiza kai Inno tayi yace "Ki lallaɓa ki kwanta idan har kin tabbatar wa ƴannan masu kuɗin sun kwanta ki maida musu da ɗiyarmu ki ɗauko tasu ki fito ki sameni nasan yadda zamuyi mu fita daga cikin asibitin nan"
Inno cike da fargaba tace "Baffah kana ganin babu matsala?"
Kallanta yayi yace "Haka nakeji a jikina Inno, ace shekararmu goma sha uku da aure baki taɓa haihuwa ba, yanzu kuma Allah ya bamu ya karɓa abunsa gashi an tabbatar mana bazaki kuma haihuwa ba maiya kamata muyi inba muyi musaya ba, ko so kike na ƙara aure?"
Tuni Inno ta tsuke fuska tace "Ka jirani nan da ƙarfe goma na dare"
Tashi tayi tana ta ƙiyasta abubuwa da dama a cikin ranta ranta.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now