page 16

207 21 7
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *16*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Cike da ruɗu da tashin hankali aka ɗauki Ahmad da Binafa sai asibiti mafi kusa dasu, cikin gaggawa aka ba Ahmad gado, Binafa kuwa tuni ta farfaɗo sosai abunda yake bata mamaki akan abunda ya faru da ita, a wannin baya da suka wuce, tana kwance a gadon da aka bata saboda ta samu damar warwarewa, duk da batasan abunda yake faruwa game da Ahmad ba, kallan Hajiya Hauwa tayi tace "Inno fa?"
Hajiya Hauwa murmushi tayi mata tace "Kwantar da hankalinki yanzu dai inane yake miki ciwo?"
Girgiza kanta tayi tace "Babu, saidai wajannan da akaima dressing ɗinsa" ta faɗa tana nuna wuyanta, cikin lallama Hajiya Hauwa tace "Karki damu insha Allahu zakiji sauƙi Very Soon"
Binafa tace "Allah yasa, saidai nifa kun sakani a duhu wai Ina Baffah da Inno na suke?"
Murmushin takaici Hajiya Hauwa tayi tace "Zan miki bayani ki kwantar da hankalinki, kinsan dai bazan cutar dake ba ko?, to ki kwanta ki huta"
Lumshe idanu Binafa tayi bata ƙara cewa komai ba.

Safwan ne ya shigo ɗakin fuskarsa sam babu annuri, kallan Hajiya Hauwa yayi yace "Mommy an shigar da Ahmad ɗakin theater"
Dafe ƙirjinta tayi tace "Maiya faru?"
Wallahi Baffah ne daya caka mishi wuƙar saida ya murɗata kuma tsinin ya shige cikin jikinsa dole ayi mishi aiki a cire inba haka ba likitoci sunce nan da a wanni kaɗan zamu iya rasa ransa.
Salati Hajiya Hauwa kawai take cike da tashin hankali da fargaba, tace "Allah ka dubemu ka tashi kafaɗun wannan bawan naka"
"Ameen" ya furta saman leɓansa, sannan ya duba Binafa data lumshe ido kamar mai bacci yace "Mommy har yanzu bata tashi bane?"
Hajiya Hauwa kallanta tayi tace "Babu mamaki bacci ne ya ƙara kwasheta dan yanzu ta tashi nace ta koma ta huta"
Gyaɗa kai yayi yace "Bari naje gunsu Daddy dan suna tare dasu Ahmad"
Fatan nasara tai mishi ta zauna ta zabga tagumi tana tunanin bawan Allah.

Cikin awanni ƙanƙani aka fito da Ahmad daga ɗakin theater idanunsa a lumshs saiya ƙara wani kyau na musamman, gabaki ɗayansu gadon da aka gunguro da Ahmad suka nufa suna tambayan likitocin akan ko an samu nasara, nan suka shaida musu anyi aiki cikin nasara, saidai suyi mishi fatan samun sauƙi.
Kowa hamdala ya farayi annuri cike da fuskokinsu suna addu'ar ƙara samun lafiya a gareshi.

Wunin ranar dai a asibiti sukayishi, Binafa kuwa Sosai ta warware ta Samu sauƙi, wata irin shaƙuwa ta musamman ce ta shiga tsakaninta da Safwan soyayyarshi sai ƙara ninkuwa take a cikin zuciyarta, ita tunda ta tabbatar da Safwan shima yana sonta tuni ta manta da wasu Baffah, sun yanke shawara gobe da safe zasu tafi, shi kuma Safwan zasu barshi shida Ahmad har sai randa aka sallameshi.
Washe gari da sassafe su Binafa suka shirya zasu tafi, suna tare da Safwan a balcony ɗin Hospital sai faman shagwaɓa take mishi, shi kuma sai wani lallaɓata yakeyi kamar wata jaririya, iyayansu suna can nesa dasu suna kallansu suna jin daɗi dan ga dukkan alamu burinsu yana gabda cika.

Safwan kallan Binafa yayi yace "Please idan kun tafi ki kulamin da kanki sosai fa, banso wani abu ya sameki"
Murmushi tayi tace "Karka damu, insha Allahu zan kula maka da kaina tamkar kana kusa dani" tafiya suka farayi yace "Shin har yanzu akwai wannan ƙaunar da kikemin kuwa?".
Fari tayi da idanunta tace "Baka ga alama ba kenan"
Murmushi kawai yayi mata sa'ilin da suka nufa ɗakin da aka kwantar da Ahmad, kallan Safwan tayi tace "Ina zamuje?"
Kallanta yayi cike da kyakykyawar kulawa yace "Saidake zanyi"
Dariya tayi tace "Shikenan ai inka saidani kaine da asarar yin haka...."
Bata ƙarasa ba taga ya buɗe wani special ɗaki suka shiga, mutum kawai ta hango a kwance yana bacci, kallan Safwan tayi taga ita yake kallo, rausayar da kanta tayi suka ƙarasa wajan, kujera Safwan yaja mata ta zauna saitin fuskar Ahmad tana kallan fuskarsa datayi haske tai fiyau da ita, Safwan ne ya kama hannun Ahmad yace "Friend sannu, ya jikin naka?"

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now