*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*12**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Getman ɗin tsayawa yayi yana kallan ikon Allah, ganin kamar babu alamun numfashi a tattare da ita yasashi nufar motarsa ya ɗauko, yayi parking kusa da ita, yana zuwa wajanta ya tsaya yana tunanin yadda zayyi ya sakata cikin motor ɗin, Safwan ne ya dafashi ya miƙo mishi ruwa a jarka, amsa yayi ya yayyafa mata a fuskarta, yayinda ya kafeta da idanu yana kallanta.
Ajiyar zuciya tayi, tare da buɗe idanunta, ganin Ahmad da Safwan tsaye akanta yasata saurin runtse idanu, tare da kawar da fuskarta, yunƙurin tashi tayi ta miƙe tare da kakkaɓe jikinta, ta dafa bango, daƙyar ta samu ta isa bakin titi tana neman abun hawa.
Safwan ne yace "mu tafi ko"
Inda take yake kalla yace "Safwan ko zamu kaita gidane, kaga fa yanayin jikin nata babu ƙwari"
Safwan yace "Babu damuwa, muje mu kaita ɗin"
Kiran waya Safwan yayi akan azo a tafinmai da motarsa tare da miƙawa getman ɗin key ɗin motar, ya sanar dashi za'azo a ansa, haɗe da bashi wasu ƴan kudaɗe, sosai ya amsa yayita faman yi musu godiya, shiga motar Ahmad yayi suka fita dan zuwa inda Binafa take, tana tsaye jikin bango tana neman abun hawa, duk da yanzu rana ta farayi abubuwan hawan sun fara ɗauke ƙafa.
Ahmad ne yayi parking motarsa gab da ita, tare da zuge glass ɗinsa ƙasa, Safwan ne yayi ƙarfin halin faɗin "Shigo mu kaiki gida"
Wani irin kallan tsana ta jefeshi dashi tare da kawar da kanta gefe wani baƙin ciki na tururuwa a ƙasan maƙoshinta, ganin zasu ɓata mata lokaci kuma bata hango abun hawa saboda sun kare mata yasata matsawa gefe dan ta samu ganin Titi dakyau.
Ahmad ƙara matsawa yayi kusa da ita, Safwan yace "Binafa dan Allah ki shigo mu kaiki gida man, jikinki babu ƙwari fa"
Harara ta maka mishi haɗe da jan dogon tsaki ta harɗe hannayanta waje guda zuciyarta na tafarfasa, ATM ɗin da ya bata ta ɗauko tare da wurga musu tace "Gashinan mai zanyi dashi kuma" tana gama faɗan haka ta fara sauri-sauri dan barin wajan.
Ahmad kuwa hankalinshi nakan Titi, fita yayi a motar yace ma Safwan "Dawo nan"
Ba musu ya koma wajan driver seat, shi kuma ya dawo wajan Safwan, ba tare daya kalli Safwan yace "Muje wajanta"
Safwan kallanshi yayi yace "Yarinyar nan bazata shiga ba wallahi, mu rabu da ita muje muyi abunda ke gabanmu, dan taga muna lallaɓatane shiyasa"
Ahmad shiru yayi bai ce komai ba, yayinda Safwan yanata faman yin mita, haka harya cin mata ya ƙara parking a daidai inda take.
Binafa ganin sun ƙara yin parking yasata kallan motar tun daga sama har ƙasa tare da maka musu harara dukansu.
Batai aune ba taga Ahmad a gabanta ya buɗe ƙofar baya ya tura ciki ya kulle, sannan ya shiga seat ɗin gaba ya rufe Safwan ya tada motar suka tafi.
Binafa bubbuga murfin motar ta farayi tana faɗin "Dallah Malamai ku buɗemin in fita, ko ana dolene, ku ƙyaleni mana ina ruwanku da rayuwata, ni ku ƙyaleni nai tafiyata"
A cikin Ahnad da Safwan babu wanda ya kalleta bare su tanka mata.
Ganin sunyi banza da ita yasata fashewa da kuka tare da ƙudundune jikinta.
Tana cikin kukanne tani ƙarar shigowar message a wayarta, dubawa tayi taga an mata transfer ɗin 10 millions, ɗago da kanta tayi ta dubi Safwan taga driving ɗinsa yake hankalinsa kwance, ta mayar da idonta kan Ahmad taga idanunsa a lumshe ga dukkan alamu ma bacci yakeyi.
Mamakine ya kamata wanene wannan yayi mata transfer, jin bata da amsar tambaya yasata maida wayarta jikin jaka tare da goge fuskarta ta jinginar da kanta a jikin window tare da lumshe idanu.
Batai aune ba bacci yayi awon gaba da ita.Knocking ɗin da akema saitin windown datake kwance yasata buɗe idanunta, idanuntane ya sauka akan na Ahmad tai saurin kawar da nata idon, tare da janyo jakarta ta fito ganinta a ƙofar gidansu.
Tana fitowa taga ansha gabanta, kanta a ƙasa tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta tafi taji hannunta cikin nasa, da sauri ta ɗago da idanunta a ruɗe jin wani irin shocking daya ziyarceta, hannunta har rawa ya farayi ganin ATM ɗinta ne ya bata yasata saurin shiga gida saboda tsabagin tsoron dataji a tattare da ita.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...