*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*28**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Binafa direct ɗakin Lanika ta shiga tare da rufe bakinta kar kuka ya suɓuce mata, Lanika tana tare da Mahmud ganin Binafa a irin wannan halin yasata saurin bin bayanta.
Tana zuwa tace "Sis lafiya kuwa?"
Ba tare da Binafa ta tanka mata ba ta raɓa ta gefenta zata wuce, Lanika janyo da ita baya tayi tace "Magana nake miki kinyi banza dani"
Hawayan data maƙalesune suka sauka akan kuncinta tace "Inaso zanyi magana da Uncle ne banajin daɗin jikina, ina zuwa yanzu zan dawo"
Bata jira cewarta ba tai saurin barin ɗakin tana murmushin jin daɗi domin tabbas Planning ɗinta yana tafiya yadda ta tsara.
Tana shiga Parlourn Alhaji Lukman tai sallama, izini ya bata ta samu guri ta zauna ganin Mahaifiyar Lukman na ɗakin yasata yin shiru tana kallan ƙasa.
Alhaji Lukman ganin yanayinta yace "Lafiya Auta na ganki haka"
Muryarta na rawa kamar zatai kuka tace "Uncle wajanka nazo"
Kallan matarsa yayi suka haɗa ido, tashi tayi tabar musu ɗakin domin su zanta.
Binafa tana kallan ta fita ta matso kusa da Alhaji Lukman saita rushe mai da matsanancin kuka.
Sosai hankalinshi ya tashi yana tambayarta meke faruwa, amma Binafa tai burus dashi ta cigaba da rera kukanta.
Ganin hankalin Uncle ɗin nata yana ƙoƙarin tashi yasata cewa "Uncle ka kira Ya Safwan"
Ta faɗa numfashinta na barazanar ɗaukewa.
Abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba yace "Me Safwan ɗin yayi miki?"
Ganin bata da niyyar bashi amsa yasashi saurin ɗauko wayarsa dan kiran Safwan.
Tunda yaji muryar Safwan ɗin shima ya tabbatar da akwai matsala, cikin muryar bada umarni yace "Kazo ɗakina ka sameni"
Shiru yayi yana nazari, kallan Binafar yayi yace "Ki kwantar da hankalinki yanzu Safwan ɗin zaizo" sosai yayita faman rarrashinta amma Ina kamar ana kara mata Volume ɗinsa.An ɗauki lokaci mai tsayi kafin Safwan yazo domin har saida Alhaji Lukman ya ƙara kiransa sanna ya samu ya rarrafo ɗakin daƙyar dan bayajin daɗin jikinsa.
Tunda ya hango Binafa gabanshi yayi mummunan faɗuwa ga idanunta yadda sukai luhu-luhu, fuskarta kuwa tayi jajir.Cikin tashin hankali yayi saurin ƙarasowa yazo inda yake yana faman yin salati.
Binafa wata irin harara ta zabga mishi ba tare da Alhaji Lukman ya lura da hakan ba.
Kallan Safwan yayi yace "Me kai mata?"
Safwan shiru yayi yana in-ina.
Waigowa yayi wajan Binafa yace "Ga Safwan ɗin yazo me kikeso kice?"Hawaye ne masu ƙarfin gaske suka sauka akan kuncinta, tana sharewa wasu na kwaranyowa, cikin muryar kuka tace "Ya Safwan ne yace ua fasa aure akwai wacca yakeso sannan kuma inhar na kuskura aka ɗaura mana aure tare to yana mai tabbatarmin saina lahira yafini jin daɗi, harda yiwa wani abokinsa talla na wai inya naso ya bashi ni ya turo magabatansa kawai, sannan a gabana ya ɗauki wayar budurwa sukaita soyayya harda yi mata kisssssssss" taja kalmar Kiss ɗin domin kukane yaci ƙarfinta.
Safwan kuwa hangame baki yayi yana kallan ikon Allah ya rasa shin mafarki yakeyi koko ba mafarkoi yake ba...
Binafa ce ta ƙara katse mishi tunaninsa tace "Harda cewa wai mai zayyi da Bazawara shifa cutarshi kuke ƙoƙarin yi dan haka tun wuri na kiyayesa, abunda ya ƙara bani takaici shine ya ɗauki Numberta yaba Abokin nasa, sai gashi ya kirani wai zai turo magabatansaaaaaa" ta ƙarashe faɗa tana wage baki tana kuka.Ran Alhaji Lukman yakai ƙololuyar ɓaci jin abun da Safwan yace game da Binafa, cike da tsantsan ɓacin rai yace "Au har talla ma kakeyi da ƙanwar taka saboda kai bakayi ko?, to ka sani bazata aureka ba haka zalika bazata auri abokin naka ban, ni Alhaji Lukman zan nemawa Binafa mijin nunawa a duniya, mijin da za'a runƙa kwatance dashi"
Binafa jin kalaman Uncle ɗin nata yasata fara tari ba ƙaƙƙautawa, yanzu gani take basirar tata a halin yanzu ta ƙare.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...