*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*23**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_**Bani da bakin yi muku godiya matuƙa, nagode ƙwarai da irin kulawarku a gareni, tabbas naji daɗin ta'aziya ɗin da akai taimin nagode sosai, Allah ya barmu tare, ina mugun ƙaunarku much, much🥰*
*Allah ya gafarta miki Aunty Fhaty yasa Aljannace makomarki, Allah ya raya miki zuri'a*Safwan yana zuwa gidansu Ahmad ya kirasa yake sanar dashi cewar gashi a ƙofar gidansu, ko kaɗan Ahmad bai yadda da hakan ba, amma ya fito ƙofar gidan ganin shin da gaske yake masa koko wasa yake masa, yana fitowa yaga motar Safwan, murmushi ne ya suɓucewa fuskarsa ya ƙaraso inda Safwan yake yace "Abokina wannan Surprises Visiting ɗin fa?" ya faɗa yana kallanshi cikin jin daɗi da kulawa.
Safwan Harararsa yayi yace "Naga alama kamar ma bakaso zuwana ba"
Zaro idanu Ahmad yayi tare da rufe bakinsa yace "Dan Allah rufamin asiri kar wasu suji su ɗauka da gaske kake, aini yau ina tunanin yau babu wanda ya kaini farin ciki wallahi"
Kallanshi yayi ya shiga seat ɗin mai zaman banza yace "Mu shiha daga ciki"
Ba musu Safwan ya doshi tamfatsetsen get ɗin gidan, aka buɗe masa, ya samu ya aje motar a parking Space"
Suna fitowa daga mota Ahmad ya ƙara cewa "Wallahi Abokina ka shammaceni, shine ko waya bakaimin ba kace kana hanya"
Safwan ƴar dariya yayi yace "Na rama ne, ka manta kamin haka babu adadi"
Murmushi Ahmad yayi yace "Aiko saidai ka rame"Su Haajarah ne suka fito daga Main Parlour itada Husnah zasu fita, inda motocin gidan suke suka nufo dan ko kaɗan basu lura dasu Ahmad ba har saida sukazo Gab dasu, Husnah ganin Ahmad ya sakata ɗan ruɗewa, yayinda Haajarah ta gaishe da Safwan tare da Ahmad.
Daƙyar Husnah itama ta nemo mazantaka ta fara gaishe dasu kanta a ƙasa dan bazata iya ɗaga kai ta kalli Ahmad ba, domin kuwa ba ƙaramin kwarjini yayi mata ba" inda motar Haajarah take suka nufa.Safwan kuwa tunda ya hango su Husnah idanunsa na kanta, Ahmad ganin har yanzu hankalinsa bashi a jikinsa yasashi zungurin Safwan yace "Wannan kallan fa?"
Sosa ƙeya Safwan yahau yi suka fara tafiya, Ahmad ruƙe da jakarsa, cikin wayancewa Safwan yace "Wa ƴannan fa?"
Ahmad kallanshi yayi ta gefen ido yace "Me sukai maka?"
Murmushi ne ya bayyana a fuskar Safwan yace "Ɗayace ta tafi da zuciyata"
Ahmad kallanshi yayi da Mamaki yace "Ina zaka kai Binafa?"
Waro idanu waje Safwan yayi tare da rufe bakinsa kamar Binafar ya gani yace "Na banu, sorry bansan ya akai hakan ta faru ba"
Taɓe baki Ahmad yayi tare da buɗe ɗakin nasa suka shiga ciki babu wanda ya ƙara cewa kowa komai, yana shiga ya shiga Bedroom ɗinsa, Direct Toilet ya nufa ya haɗawa Safwan ruwan wanka, yana gama haɗawa yazo ya samu Safwan yace "Ka shiga ciki kayi wanka" yana gama faɗa masa hakan yabar masa ɗakin.
Safwan binsa yayi da kallo harya fice, wata nannauyiyar ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe ido yana tunanin tabbas yayi ba daidai ba, maiya kaisa irin wannan suɓutar bakin alhalin yana da wacca zai aura kuma Ahmad shima yasanda haka, jiki babu ƙwari ya tashi ya shiga Bedroom ɗin dan shiga Toilet.Ahmad ɓangaran mahaifiyarsa yaje yana tambayanta ko zai samu abinci mai zafi, nan ta sanar masa ba'a daɗe da gama abinci ba, wayarta ta ɗauka tare da bada Umarnin a kawo mata abinci a cooler.
Ba'a ɗauki lokaci ba saiga ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan sunyi mata knocking.
Ahmad ne da kanshi ya tashi yaje ya amsa, dawowa yayi ya zauna kusa da Mahaifiyarsa yace "Mom, baƙo nayi, Safwan ne yazo"
Murmushi tayi tace "Masha Allah, ina mai sannu da zuwa"
Murmushi kawai yayi, canza fuska tayi tace "Shine baka faɗamin zaizo ba sai bayan yazo"
Hannunta ya ruƙo yace "Afuwan Uwa ta gari, wallahi bansan da zuwansa ba nima, sai kirana yayi yace "Yana ƙofar gidanmu"
Murmushi tayi tace "Babu komai yaran kirki, Kawunka fa yace baya samun layinka komai yasa?"
Kallan wayarsa yayi yace "Babu mamaki sharrin Network ne"
Tashi yayi dan bayason maganar ta tsawaita, binshi tayi da ido dan ta gano kamar bashi da gaskiya game dashi da Kawun nasa, ganin ya fita ta sauke ajiyar zuciya, tare da gyara zamanta ta kwanta.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasiaBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...