page 13

196 20 10
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *13*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Tunda Binafa ta shiga gida ta ruga ɗaki da gudu tare da sakawa ƙofar key ta faɗa kan gado ta fara rusa uban kuka, tunaninta ɗaya shine kar Safwan ya rabu da ita, dan ita kanta batasan wani irin so take mishi ba, ta yadda ta rasa kowa amma banda shi, tayaya zata iya koyawa zuciyarta rashinsa, kuka takeyi sosai tamkar ranta zai fita.
Wayarta ce ta fara ruri ta kalla taga no name, banza tai da wayar ta cigaba da kukanta maicin rai, hannunta ta kalla tana tuna abunda ya faru lokacin baya daya wuce.
Ganin baza'a daina kiran ba yasata ɗauka ba tare da tayi magana ba, cikin zazzaƙar muryarsa yace "Please ki daina kukan nan haka, tun ɗazu kikeyi yaka mata ki daina dan Allah" ya ƙarashe faɗa cikin wata irin murya, shiru tayi batace komai ba, domin batasan mai maganar ba, kuma tana mamakin yadda yasan kuka take, Ahmad ne ya faɗo mata arai, cikin dashashshiyar murya tace "Wanene?"
Ahmad yace "Bai zama dole kinsan waye ba, amma ina roƙonki da ki manta da komai ki manta kin taɓayin rayuwa da Safwan"
Kukane ya suɓuce mata tace "Tayaya?, kasan wani irin so nake mishi kuwa?, bansan ina ƙaunarsa haka ba saida ya furtamin kalmar rabuwa, bazan iya ba, zuciyata ɗaci takemin da raɗaɗi"
Ahmad kasa jurar maganganunta yayi ya kashe wayar yana saukar da ajiyar zuciya tare da furzar da iska mai zafin gaske, ya rasa ta ina zai fara, tayaya yayi saken da zuciyar Binafa tai mugun kamuwa da son Safwan har haka, runtse idanunsa yayi ya buɗe yayinda har sun sauya kala, Saliva ya haɗe mai ɗacin gaske daga maƙogaransa, ƙirjinsa ya dafe ganin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, yanzu burinshi tayaya zai cire son Safwan daga zuciyar Binafa.

Kande kallan Hajiya Hauwa tayi tace "Wallahi Hajiya Inno nagani da idona zata shiga wata mota itada mijinta Baffah da wata budurwar yarinya, ga dukkan alamu itace Binafa, kuma na kira sunanta ta ganni na ganta, naso mai motar danahau ya tsaya amma yaƙi tsayawa ƴan cikin motar sukayi caa kaina akan su sauri suke"
Shiru tayi yayinda Alhaji Modibbo, Hajiya Hauwa da ƴaƴansu sukai jugum-jugum suna saurarin babbar ƴar aikinsu wanda suka kwashe shekara da shekaru suna tare da ita, Alhaji Modibbo ne yace "Yaushe kika gansu?"
Kande tace "Randa na tambayeka zanje ƙauye ganin Kakata da akace jikin yaƙi daɗi"
Sultan yace "Da gaske kin tabbatar da Inno kika gani Baba?(Kasancewar haka yaran gidan suke kiranta dashi saboda girmanta da matsayinta)"

Murmushi Kande tayi tace "Haba Inno ce bazan iya ganeta ba Sultanu, wallahi itace, suna nan cikin garin Kano, saidai bansan inda suke ba gaskiya, nima ganinsu nayi sun shiga cikin wata mota mai kyau, ita kuma Binafa tana jikin window ni wallahi sai naga taimin kama da Lanika  inba kallan tsoro nai mata ba"

Kowa shiru yayi, kowa da abunda yake tunani a cikin ransa, Alhaji Modibbo ne yace "Bari na kira ƙanina Lukman, (Mahaifin Safwan), na sanar dashi abunda ke faruwa ko menene ma zan sanar daku" tashi yayi ransa sam babu daɗi abubuwan da suka faru shekarun baya da daɗewa suka fara yimai yawo a ƙwaƙwalwarsa.

Hajiya Hauwa ma tashi tayi sam babu kuzari a jikinta ta ɗauki wayarta dan kiran Hajiya Nafeesa ta sanar mata abunda ta sani.
Kowa watsewa yayi, yayinda Mahmud shima ya fita ya ɗauki wayarsa dan kiran Safwan, ringing ɗaya ya ɗauka yace "Friend kasan meke faruwa kuwa?"
Shiru yayi yana sauraran abunda yake cewa, Mahmud yace "Matar da zaka aura fa tana nan a doron ƙasar nan, hasalima tana cikin garin nan saidai ba'asan inda suke ba"
Sosai hankalin Safwan ya tashi yace "Kana nufin Fatima tana raye?, dan Allah friend da gaske kake?" hawayene suka sauka akan kuncin Safwan saboda ganin yana ƙoƙarin zaucewa.
Mahmud ne yace "Cooldown mana friend, ka daina damuwa man, yanzu dai Daddy yace zai ɗauki mataki, yanzu hakama maganar da nake faɗa maka, ya kira Small Dad (Mahaifinsa kenan) za'ai bincike tunda Baaba ta tabbatar da suna cikin garinann"
Shiru yayi, zuciyarsa na bugawa yace "Allah yasa, amma dan Allah kar a faɗawa Lanika hankalinta zai tashi kasan yadda ta damu da Twins Sis ɗinta duk da bata santa ba"
Murmushi Mahmud yayi yace "Haba ainima bazanso hankalin gimbiyata ya tashi ba, ai mana buƙulun yin birthday, kasan nine babban baƙo" ya ƙarashe faɗa da sigar zolaya.

Murmushine ya suɓucewa Safwan yace "Shikenan, yanzu kaida Mommy saiku daina takuramin akan na nemo mata, tunda yanzu an tabbatar da Fatima na raye"
Dariya Mahmud yayi yace "Nafa manta kaine ɗan raino lokacin" ya faɗa yana mai dariya ƙasa-ƙasa
Murmushi kawai Safwan yayi yace "Ba damuwa, nima ina nan zuwa gidan inna gama abunda nakeyi" katse kiran gabaki ɗayansu sukai, kowa da tunanin dayake fama dashi a cikin ransa.

Binafa kallan wayar tayi jin a katse kiran, taɓe baki tayi ta zauna ta fara zurfafa tunaninta akan Safwan, ganin in bashi ba bazata taɓa sauraran kowa ba, shiru tayi tana nazari, bisani daga baya ta tashi ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta tada Sallah.

Gabaki ɗaya Familyn Alhaji Modibbo sun tashi tsaye wajan neman Inno da Baffah, amma ina babusu babu labrinsu, hatta inda Kande tagasu Baffah saida ta kaisu amma basu samu abunda suke nema ba, sosai aka dage wajan addu'o'i domin kuwa an tabbatar musu Binafa tana kusa dasu, saidai yace su kwantar da hankalinsu tana cikin ƙoshin lafiya.

Baffah ne ya kalli Binafa ganin kwana biyu duk ta lalace ta fita hayyacinta, ga wata ƴar rama datayi kwana biyu, Kiran sunanta yayi tazo inda yake kanta a ƙasa tace "Baffah gani"
Baffah kallanta yayi yace "Ƴar leleta meke faruwa ne naga kin rame?"
Kasa bashi amsa tayi ta fashe da kuka, ganin tana kuka yasa hankalinshi tashi yana tambayarta maiya sameta, saida taci kukanta ta ƙoshi sannan tace "Baffah, Safwan ne yace wai bayasona"
Baffah tamƙe fuska yayi yace "To saime idan baya son naki?, an faɗa miki yanzu nai niyyar aurar dake ta gaskiya ne da kika damu kanki akan wani Safwan, kinga Binta ki fita idanuna in rufe inba hakaba naci miki mutunci wallahi, dan haka ki sani aure ba yanzu ba ko kinaso ko bakya so"
Tasho tayi a fusace tabar wajan ta nufa hanyar waje, tana fita ta saki kuka tare da dafe zuciyarta saboda raɗaɗin datakeji tana mata.

Baffah kuwa bayan fitar Binafa kuwa hankalinsa yayi mummunan tashi, babu shiri ya tashi ya zaga can bayan gida dan yin kira, ya daɗe yana kira amma ba'a ɗauka ba, can kuma aka ɗauka yace "Haba Malam yaya zakaimin haka?, dakai fa mukai za'a kulle zuciyar yarinyar nan akan bazata so kowa ba, sannan ka zaka mata soyayyata amma ya haka, kaifa kasan komai, saboda hakane yasa na hana Inno shayar da ita, yanzu kana da labarin wani takeso, kuma ga dukkan alamu tana matuƙar ƙaunarsa, dan Allah ka ƙaramin aiki akanta kamar yadda ka saba, kuma ka cire mata shakku akanmu, saboda kwanaki saida ta titsemu akan anya mu muka haifeta, kuma karka manta da alƙawarinmu karka sake ka faɗawa Inno ƙudirina na auranta inba haka ba komai zai iya lalacewa" ya daɗe wayar na kunnansa yana sauraran abunda Malamin ke cewa, can kuma yace "Shikenan, inaso zanzo garin katsinan saika bugamin ƙasa a gabana naga shin meke faruwane haka" shiru yayi yana sauraro yace "Shikenan ka jirani nan da Gobe insha Allahu zan ɗauki hanyar katsina, sai anjima"
Katse kiran yayi yana mazurai, tare da waige-waige, sannan ya saka wayarsa a aljihu ya fito, yana fitowa yaga Inno ta tsaya ta tsare hanya, gabanshi ne yayi mummunan faɗuwa ganinta a tsaye yana addu'ar Allah yasa bataji ba.
Katse mai tunani tayi tace "Me kakeyi anan naji kamar muryarka?"
Murmushi yayi yace "Na kira Malam ne, domin naga abubuwa sun fara taɓarɓare mana game da waccar yarinyar shiyasa nakeso naima tufkar hanci.
Inno matsa mai tayi ta wuce tace "Yaka mata, dan naga kamar ta fara dawowa hayyacinta, gwanda ayi a koma gidan jiya kar asirinmu ya tonu"

Murmushi yayi yace "Nima haka nagani, kuma a gaskiya yaka mata muyi gaggawar barin garin nan nasan yanzu haka Familyn Modibbo suna nemanmu ruwa a jallo, kuma fa ni ina zargin yaron nan Safwan kamar ɗan gidan Hajiya Nafeesa ko baki ganesa ba?"
Taɓe baki Inno tayi tace "Nima da farko naga kamar amma saina share, gwanda muyi maza-maza mubar Kano kafin su ankara, kuma inaso a rufe mata baki kar tayi jayayya na barin garin nan kana gani kwanaki yadda mukai da ita"
Murmushi yayi yace "An gama, inaso gobe inje katsinane"
Raɓawa gefenta yayi ya wuce, hango Binafa da yayi a zaune ta saka kanta cikin cinyoyinta yasashi ƙarasawa kusa da ita, a koda yaushe ƙaunar yarinyar ƙara mamaye zuciyarsa take, cike da tausayinta da kuma tsantsan ƙaunarta yace "Haba Binafa akan yaron nan kikabi kika damu kanki?, to kiyi haƙuri zan sameshi komai zai daidaita"
Ɗago da fuskarta tayi data canza kala ta koma ja tace "Baffah da gaske kake?"Murmushi yayi yace "Ƙwarai kuwa, ai farin cikinki shine nawa"
Tashi tayi fuskarta cike da farin ciki ta ruga ɗakinta a guje tana dariya, tana shiva ta faɗa gado ta fara jifa da Pillow abun gwanin ban sha'awa.

*Kuyi maneji*
*More comment more typing*

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now