page 17

206 27 12
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *17*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Gabaki ɗaya parlourn an taru Binafa kaɗai ake jira, Binafa kuwa tsoron fitowa take saboda kar Baffah ya kasheta kamar yadda taji yana ikirari, Mommy kallan Safwan tayi tace "Jeka taho da ita"
Ba musu ya tashi ya shiga Bedroom ɗin datake yayi Knocking, a ɗan razane ta kalli ƙofar tace "Waye?"
Safwan cikin sanyin muryarsa yace "Binafa ki buɗe Safwan ne"
Tashi tayi jiki babu kuzari tazo ta buɗe mai, kallanta yake haka itama kallansa takeyi idanunta cike da ƙwalla tace "Please bazan iya fitowa ba tsoro nakeji"
Cikin muryar kwantar da hankali yace "Ki saurara Binafa babu abunda zai sameki insha Allahu, kuma hannun Baffah da kike tunani a kulle yake da handcuff dan haka ki kwantar da hankali ke kaɗai kawai ake jira"
Gyaɗa kanta tayi tare da share hawayan fuskarta da suka zuba, ta janyo Veil ɗinta ta yana tace "Muje" a jere suka shigo parlourn kan Binafa a ƙasa, ɗaga idonta tayi suka sauka akan na Lanika cikin a zama ta ƙarasa wajanta ta zauna, kana kallanta zaka tabbatar da akwai tsoro a tattare da ita.
Babu abunda kakeji a parlourn sai ƙarar A.C, wajan yayi tsit, yayinda Baffah yayita faman kallan Binafa tamkar wani tsohon maye, a tsakanin kwanakin nan kuwa Baffah ya yabawa aya zaƙinsa dan ba ƙaramin wuya sukasha ba a hannun kwalawa, Inno kuwa ba baka sai kunne, dan ita tama rasa a wata duniya take lahira ce koko duniya saboda bugun da sukasha akan su faɗin gaskiyar lamarin.

Alhaji Lukman ya watsawa Baffah kallan ƙasƙanci yace "Uhum muna jinka, ka faɗa mana gaskiya inba haka ba wallahi yau ayi gidan yari dakai"
Baffah wani Saliva ya haɗiye daƙyar daga maƙogaransa yana kallan Binafa cike da ƙaunarta yace "Nidai kuyi haƙuri ku yafemin, wallahi duk abunda Binafa tayi tun daga kan Damfara da aure-auren datake ba'a hayyacinta takeyi ba, a zahirin gaskiya mun haɗa baki da malaminmu ne akan ya rufe mata baki akan duk abunda mukace eh to eh ɗinne a wajanta koda kuwa a'a ne, kuma nayi haka ne domin ita, domin gina rayuwarta cikin farin ciki da annashuwa, naso ta tara wasu kuɗaɗan dana ɗiba zata tara sannan na yanke shawarar auranta, nasan bazata taɓa maraicin kuɗi ba, kuma a zahirin gaskiya na daɗe da kamuwa da son Binafa tun tana ƴar ƙaramarta, nasha yunƙurin yin lalata da ita amma hakan yaƙi yuwuwa na rasa dalilin haka, shiyasa na yanke shawarar maida ita aure jali, sannan daga baya na aureta, ko tanaso ko bataso, balle nasan zataso saboda kulle bakinta zan saka ayi"

Babu abunda kakeji a parlourn sai salati, yayinda Binafa kanta a ƙasa babu abunda takeyu sai zubda hawaye ta kasa yadda cewar Baffah ke wannan maganar da bakinsa.
Inno kuwa kallanshi tayi cike da tsantsan tsana tace "Allah ya tona maka asiri baƙin mugu azzalimi"

Mommy hamdala kawai takeyi a ranta jin batun Baffah, cike da jimami da al'ajabi tace "Tabbas Allah yayi gaskiya, ninasan insha Allahu yarinyar dana haifa bazata taɓa aikata zina ba, domin tun randa na haifeta na karanta mata wannan surar *Bismillahir rahmanir raheem, Wa maryamabnata imranallati ahsanat farjaha fanafakna fihi min ruhina wa saddaqat bi kalimati rabbiha wa kutubihi wakanat minal qaniteen* ƙafa uku na tofa mata a farjinta, sannan na kan karanta na tofa a cikin ruwan zam-zam ɗinta tasha wannan surar tana cikin *Suratul Tahriim ayar ƙarshe tun daga farkon ayar zuwa ƙarshenta*, kafin a ɗaukemin ita, lallai Allah abun godiya ne, yana dakyau iyaye su runƙa karantawa ƴaƴansu saboda yadda duniyar tamu ta lalace ta fyaɗe-fyaɗe da zinace-zinace, Allah yasa mu dace.

Kabbara aka hauyi yayinda soyayyar Hajiya Hauwa ta ninku a zuciyar Alhaji Modibbo da Binafa, nan take aka yanke hukunci makasu Baffah akotu akan duk abunda sukayi, sannan an tabbatar da Binafa bata da wani laifi tunda duk abunda ya faru ba'a hayyacinta take yinsa ba, ajiyar zuciya Mai ƙarfi Binafa ta sauke tare da hamdala, tana ɗaga ido taga Ahmad ita yake kallo, saurin sadda kanta tayi tana yiwa Allah godiya da wannan ni'imar da yayi mata.
Nan take aka tafi dasu Baffah gidan da suka koma wato Cell, Inno kuwa ba abunda takeyi sai kuka tare da faɗin Baffah ya cuceta ya lalata mata rayuwa.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now