*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*10**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Tana fitowa ta hango Baffah a ƙofar gida a zaune, cike da fargaba ta ƙarasa wajan, gefe ta raɓa zata wuce ya tashi a fusace yace "Gidan Ubanwa zaki?"
Idanunta a runtse ganin yayo kanta tace "Zanje shago ne zan siyo Pad"
Harara ya maka mata "Yace ki maza kije ki dawo"
Ɗaga kai tayi tai saurin barin wajen ba tare data ƙara waiwayarsa ba, ganin ta ɗanyi nisa kuma Baffah bai ganinta yasata ɗaukar wayarta ta kira Safwa, kwatancan inda yake yayi mata tai maza ta ƙaraso kusa dashi, waige-waige ta farayi tai wuf ta shiga motarshi tana maida numfashi, kallansa tayi tai mai murnushi, shima mayar mata yayi, cikin muryar shagwaɓa tace "Na dawo dakai ko?"
Lumshe ido yayi yace "Karki damu ai kinfi haka"
Murmushi tayi ba tare data ƙara cewa komai ba ta ɗauko ƴar purse ɗinta ta ciro ATM ɗin tace "Gashi, kuɗin ciki zasuyi 80 Millions please ka kulamin dasu kafin Baffah ya dauko saika bani"
Safwan bayyi mamakin jin kuɗin sunkai haka ba, ATM ɗin ya ansa yanata faman jujjuyashi.
Katse mai hanzari tayi tace "Saidai inason ka ban koda dubu ɗari biyar ce saboda hidindumun yau da kullum gashi kuɗin hannuna bai wuce dubu hamsin ba"
Ƙara kallanta yayi yace "Gaskiya babu kuɗi a hannuna, but bari naje Bank na ciro miki"
Kallanshi tayi da fararan idanunta tace "Ai yanzu sun tashi koka manta?, duba lokaci yanzu biyar da rabi na yamma"
Dafe goshinsa yayi yace "Ouch wallahi na manta sam, but menene Pin ɗinki gobe da sassafe sai naje na ciro miki"
Ba tare da tunanin komsi ba tace "2222, zakasa guda huɗu"
Murmushi ne ya suɓucewa Safwan, itama ganin yayi murmushi yasata maida mishi, fita tayi tace "Bari naje kar Baffah ya nemeni dan yaga fitowa ta"
Hannun ya saka a aljihunsa ya ciro bandir ɗin ƴan dubu ɗaya ya miƙa mata yace "Ungo wannan"
Kallan kuɗin ta tsayayi, tare da kallan gashin hannunsa daya kwanta yayi luf, girgiza kai tayi tace "Ni ba kuɗinka nakeso ba, kai nakeso, dan haka bana buƙatar kudin nan"
Safwan wani irin kallo ya jefeta dashi wanda ya sakar mata kasala yace "Nasan ba kuɗina kikeso ba, domin kuwa nine shaida, wannan kuɗin na baki sune halak malak, kuma zai miki amfanin da zakiyi mamaki, dan haka ki ansa domin idan na ciro kuɗi bana ƙara maidasu cikin aljihuna"
Hannu biyu ta amsa tai mishi godiya, yayinda haka kawai ta tsinta kanta da faɗuwar gaba dataga Safwan zai tafi, murmushin yaƙe tayi tare da ɗaga mishi hannu ta juya ta tafi.
Tana zuwa ƙofar gida taga Baffah yanata faman safa da marwa, yana hangota yayi hanzarin tahowa yana faɗin, "Ya najiki shiru, sai yanzu zaki dawo?"
Jikinta na rawa tace "Safwan ne ya tsaidani...."
Bai bari ta ƙarasa ba ya ɗaga hannu zai mareta, tuni ta matsa gefe ya mari iska, hannunta na rawa ta miƙa mishi kuɗin da Safwan ya bata, amsa yayi yana washe baki yace "A'a inash shi Malam Safwan ɗin yake?"
Ɗan sakin jikinta tayi tace "Ya tafi, dama ba daɗewa zayyi ba"
Faɗaɗa far'arsa yayi yace "Haba yanzu naji batu, shiga ciki Allah yayi miki albarka"
Itama murmushi tayi tace "Ameen"
Shiga ciki tayi fuskarta shinfiɗe da fara'a, tana shiga ɗaki ta kwanta tai rubda ciki tare da lumshe idanu, batai aune ba bacci yayi awon gaba da ita.Safwan kallan Ahmad yayi yace "Gashi, amma yaka mata a ciro mata dubu ɗari biyar ɗin ko zata rage zafi, saboda a gaskiya yarinyar babu kuɗi a hannunta"
Ahmad miƙewa yayi tare da ɗaukar ATM ɗin yace "Kai ka damu da rayuwarta, nidai burina na maidawa wanda ta gudu da kuɗaɗansu, dan haka insha Allahu a week ɗinnan kowa zan damƙawa kuɗinsa, yanzu Bank zan tafi su tattaramin kaf kuɗaɗan Account ɗinta su naida a nawa"
Jiki ba ƙwari Safwan shima ya tashi yace "Ka taimaka a bata kuɗin data buƙata inba haka ba zata iya faɗawa cikin mawuyacin hali, don iyayanta basu damu da halin da zata faɗa ba inhar zata biya musu tasu buƙatar, a ciki kuwa har karuwanci zata iya inhar zata samu kuɗi, kuma ka sani inhar ta shiga wani hali mara kyau akan rashin kuɗi to tabbas muna da namu kamason a wajan Allah..."
Safwan kasa ƙarasa faɗan maganar yayi ganin Ahmad ya doshi motarsa ya wuce ya barshi a wajan.
Safwan girgiza kanshi yayi ganin babu abunda ya ragu a cikin miskilanci Ahmad, tausayin Binafa ne ya ziyarce sa tare da tunanin halin da zata shiga inhar ta tabbatar da yaudararta yayi, shima motarsa ya shiga ya tayar ko kaɗan baya cikin nutsuwa.Tunda Ahmad yaje Bank ɗin suka gama duk wani abu daya kamata kuɗin su dawo Account ɗinsa, kasancewar ya nuna musu I.D card ɗinsa, ko kwabo ɗaya ba barwa Binafa ba, haka ya fito daga Bank ɗin tare da kiran Kawunsa dan yi mishi Albishir.
Alhaji Mansur tunda yaji labarin kuɗinsa ya dawo yayita faman farin ciki da Annashuwa tare da shima Ahmad Albarka.
Haka ya kira Alhaji Aminu, nan shima yayita faman yimai godiya tare da addu'ar samun nasara da ɗaukaka, cikin zumuɗi yace "Yaushe zanzo naamsa?, sannan saina haɗa nayi belin Matata" ya faɗa yana washe baki.Abunma yaso ya bawa Ahmad dariya amma saiya dake, yana mamakin duk uban damfafar datai mishi amma yake ƙoƙarin maida ita ɗakinta, murmushi yayi yace "Bamu kamata ba tukun, kuɗinku ne ya farayin gaba kafin ita, sannan maganar cewar matarka ce yanzu bata taso ba, ko kana da labarin bayan kai akwai wanda suka aureta ba mutum ɗaya ba, ba mutum biyu ba, wannan maganar dole zamu miƙata kotu, dan kotu ce zata fidda duk wani abu dake cikin duhu, koti ce zata ƙara muku haske, so yanzu dai ka turomin da Account Number ɗinka na maida maka da kuɗaɗanka"
Cike da rashin ƙwarin gwiwa yace "Tom shikenan bari na turo dashi yanzu" katse kiran yayi yana tunanin maganganun Safwan.
Tuni ya manta da maganarsa, ya ɗauki wayarsa dan kiran Prof Sunusi dan shaida masa abunda ya faru.
Shima sosai yayi farin ciki dajin wannan batun, tare da yi masa godiya.Ana kiran Sallahr Magrib Binafa ta tashi, a razane ta farka ganin lokaci yaja, tashi tayi ta nufa bayi ta ɗauro alwala dan gabatar da Sallah, tana idarwa ta hango wayarta nata haske kasancewar a Silent take, ɗauka tayi taga alert ne daga Bank, duk da Binafa batajin turanci amma ba laifi takan karantawa kuma takan gane wani saboda darajar ƙamus ɗinta tare da taimakon Allah.
Murza idanu tayi dan ganin Account ɗinta 0.0 babu ko sisi, kafe wayar tayi da idanun dan ganin kamar bata gane me suke nufi ba, ganin tabbas babu ko sisi a wayarta yasata shiga ɗimuwa da tashin hankali tana tunanin garin yaya haka ta faru, tuno da Safwan datayi ta bashi ATM ɗinta kuma ta faɗa masa Pin ɗinta yasa gabanta mummunan faɗuwa, hannunta na rawa ta ɗauki waya tana neman layin Safwan, ringing take amma no answer sosai jikinta ke tsuma ga tashin hankali ƙarara ya bayyana a fuskarta, tunani take kawai yadda zata ƙare da Baffah dan tasan tabbas bazai lamunta wannan asarar ba, kafin kace me gumi yayi sharkaf a fuskarta ga idanunta sun sauya kala alamun so take tayi kuka.Safwan kuwa tunda yaje masaukin da Ahmad yake ya manta ya saka wayarsa a silent ya fita dan ganawa da wani abokinsa, wayar tana kusa da Ahmad duk kiran datakeyi yana gani, ganin bazata daina kiran ba kuma ga dukkan alamu tasan maiya faru da Account ɗinta na Bank yasashi yin ƙaramin tsaki ya ɗauki wayar danjin me zatace, shiru yayi baice mata uffan ba.
Binafa kuwa jin an ɗauki wayar anyi shiru sai kawai ta fashe da wani irin kuka mai ɗaga hankalin mai sauraranta, cikin kuka tace "Safwan ya zakaimin haka?, kasab wani irin hali zaka jefani kuwa?, yanzu yaya zanyi da Baffah inhar yasan yaudarata kayi ka kwashe kuɗin Account ɗina, Safwan ka tausayawa rayuwata wallahi Baffah zai iya illatani a rayuwa, Baffah baisan ƙaddara ba, ba damuwarsa bace koda zanyi yawo tsirara inhar zan biya mishi buƙatarsa" cikin sassauta muryarta tace "Dan Allah Safwan ka rufamin asiri ka dawo da kuɗinnan, kaga ni macace bansan waca hanya zanbi na ƙara samu kuɗi kamar haka ba, gashi Baffah yasan kan kuɗinnan, wallahi kasheni zayyi" ya faɗa hawaye nabin fuskarta.
Ahmad runtse idanu yayi yanajin sautin kukanta har cikin ransa, cikin daddaɗar muryarsa yace.....
*Kuyi maneji yau ina busy ne*
*#Comments*
*#Shares*
*#Votes*
*#Likes*
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...