Page 33

204 19 8
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *33*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1Q

Abun dai ya faro ne lokacin da Safwan yaje dubashi....
Duk abunda ya faru lokacin da Safwan yaje duba Ahmad Daddy ya sanar da Binafa sannan ya ɗaura da cewa bayan Safwan ya dawo lokacin bikinku saura kwana uku, anan ne ya haɗamu da Uncle ɗinku yayi mana taƙaitaccan halin da Ahmad yake ciki game da hanashi auranki da mukai, nan take Safwan yace ya haƙura dake ya baiwa Ahmad sannan kuma muje mu nema masa auran ƙanwarsa mai suna Husnah, na girgiza ƙwarai dajin halin da Ahmad ya shiga lokacin danai mushi iyaka dake, ashe ban sani ba shine mijinki, na yadda da Ahmad, sannan ba yadda da tarbiyarsa, bani da haufi akanshi, dan haka shawarar da zan baki anan shine kibi mijinki, kibi dangin mijinki sau da ƙafa, Allah yayi miki albarka"
Cike da sanyin jiki tace "Ameen Daddy"
Mommy ce ta ɗaura da cewar "Ki sani zaman aure saikinyi haƙuri muddin kikace bazakiyi haƙuri ba to tabbas kina tare da aiki ba ƙarami ba, ki kyautatawa mahaifiyarsa da ƙannansa sannan ki zama mace ta gari mai yawan Ibada mai saka mijinta akan hanyar gaskiya, Allah ya albarkaci rayuwar auranku ya baku zuri'a ɗayyiba"
shiru tayi batace komai ba, ji take kamar ta fasa ihu tai kuka ta ƙoshi haka takeji.

Miƙewa mahaifiyarta tayi tace "Tashi muje"
Ba musu tabita a baya suka bar ɗakin, wasu sirrikan magungunan mu na mata ta bata tare da ƙara yi mata nasiha, domin duk a tunanin Mommy ƴar tata tasan maza, Bathroom ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka wanda yaji turare taje tai wankanta ta fito, wasu fitinannun kaya masu kyau da tsada Mommy ta ɗauko mata ta saka, Mommy tsayawa tayi akanta tare ta tabbatar datayi kwalliya, tana gamawa suka fito tare Part ɗin Daddy suka ƙara komawa tace "Kai mata addu'a zata tafi"
A ɗan razane Binafa ta ɗago da kanta tana kallan Mahaifiyar tata.
Murmushi yayi tare da dafa kanta ya fara kwaranyo addu'o'i, cike da ƙarfin hali yace "Allah ya kiyaye hanya ya sa gidan zamane"
Wasu zafafan hawayene suka sakkowa Binafa bata damu data goge ba, daƙyar ta samu damar barin ɗakin, Still ta ƙaramin Get Mommy tabi da ita, itama cikin dakewa tace "Allah ya bada sa'a yasa gidan zamane, sai kinyi haƙuri Binafa ki zama mai kawaici, kiji kiƙi ji, ki gani kiƙi gani"
Sosai Binafa ta fara kuka kamar wacca akace mata bazata ƙara ganinsu ba.
Mommy tai ƙaramin halin cewa "Ki tafi Uncle ɗinku na jiranki, ki gaidamin da Umman taku" tana gama faɗan haka ta juya ta fata tafiya tana goge hawayan daya zubo mata.
Binafa tana tsaye har saida ta ɓace mata sannan ta sauke ajiyar zuciya ta fita.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now