Page 37

163 20 1
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *37*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1Q

Ƙarfe biyar na Yamma Binafa ta tashi, ganinta a asibiti sai abun yayi matuƙar bata mamaki, Husnah ce ta fara zuwa inda take tace "Sannu Aunty ya jikin?"
Ɗaga kanta kawai tayi alamun da sauƙi ta maida kanta kan Pillow ta kwanta tana mamakin abunda ya kawota Hospital, mahaifiyar Ahmad ce ta shigo bakinta ɗauke da Sallama, ganin Binafa ta farka yasata ƙarasawa tana mata sannu ji take kamar ta maidata ciki don ƙauna, sosai take tarairayar Binafa abun kuwa ba ƙaramin mamaki ya bata ba taga kowa sai nan nan da ita ake, ganin har yanzu bataga Ahmad ba yasata ɗan damuwa ko ina ya tafi kuma oho, Mahaifiyar Ahmad ce ta ɗauko Flask tace "Tashi ki daure kisha Tea ɗinnan Ahmad yace ba abunda kika sha"
Ba musu Binafa ta tashi ta jingina da Gadon tare da lumshe idanunta, gabaki ɗayansu sai sannu kawai suke mata, Tea ɗin tasha kaɗan ta aje tace ya isheta.
Doctor ne yazo ya duddubata tare da bata magunguna, nan take aka rubuta mata takaddar sallama.
Direct gidanta suka nufa nan su Haajara sukai mata ayyuka mahaifiyar Ahmad kuma ta tafi gida.
Ahmad tarewa yayi a Bedroom ɗin Binafa datayi motsi sai yace mata "Akwai abunda kike buƙatane ko kike sha'awar ci?"
Saidai kawai Binafa tai murmushi, ganin jikinta ya warware yasashi tashi ya nufa Office yace su Husnah su zauna su tayata hira idan ya dawo zai kaisu gida.

*Bayan Sati Uku*
Shirye-shiryen Bikin Husnah da Safwan ya kankama matuƙa domin yau biki bai wuce kwana biyar ba, yayinda Binafa Allah ya taimaketa cikinta ba mai laulayi bane, tun randa ta samu sauƙi har yanzu bata ƙara kwanciya rashin lafiya ba, komai ci takeyi, haka zalika bata tare miyau a bakinta irin na masu ciki, saidai ta ƙara haske matuƙa tamkar ba ita ba tayi wani ƙiba gwanin ban sha'awa, tarairaya kuwa Binafa na shanshi tun daga kan Ahmad, Mahaifiyarsa dasu Husnah duk abunda sukason mai ciki tanaso to insha Allahu za'ayi ƙoƙarin siya mata, shiyasa hankali Binafa a kwance yake.

Binafa tana zaune gefen Ahmad yayinda ta tuno baki tamkar zai faɗo ƙasa, cikin muryar shagwaɓa tace "Dan Allah Ya Ahmad ka bari naje bikin Ya Safwan mana, inaso mu fara shirye-shirye da wurine shiyasa"
Ahmad hankalinshi nakan Laptop ɗinsa yace "Na faɗa miki bazaki ba, ki bari idan za'a kai amarya saina kaiki da kaina inyaso ko kwana ɗayane sai muyi mu dawo...."
Bata bari ya ƙarasa ba ta daka ƙafarta ƙasa tare da juya mai baya tana ƙoƙarin yin hawaye tace "Ya Ahmad dan Allah karkaimin haka nidai sai naje"
Ta faɗa tana murguɗa mishi, rufe Laptop ɗin yayi ya janyota jikinsa yace "Sweetheart kiyi haƙuri ki bari sai ranar da  za'a kai Husnah, kinsan Babyna bayason yawan zirga-zirga yanzu sai kiga ya fara wahalarmin dake, nifa da so samu ne bikin nan baza kije ba sai kin haihu sai kije musu da Baby"
Zaro idanu waje Binafa tayi can kuma saiga hawaye tace "Haba Ya Ahmad, bikin Ya Safwan ɗin guda yaka mata ace basai nai maka magana ba tun yau zakaje na shirya ka kaini"
Murmushi yayi mata tare da yi mata Peck yace "Karki damu ana gobe biki zamu tafi inyaso sai sai mu wuce Kd da ango in an ɗaura auran sai nazo mu tafi kinji Babyna"
Duk da Haka Binafa bata gamsu ba, goge hawayan fuskarta tayi ta buɗe baki zata ƙara yi mishi magana kenan sai taji bakinsa cikin nasa, lumshe ido tayi tare da ƙoƙarin maida mishi da martaninsa.
Batasan Ahmad ya lura da itaba tun lokacin data samu ciki yaga tana matuƙar son keɓewa dashi, hakan na nufin nata cikin da jarabar kasancewa da Mijinta yazo mata.
Nan fa labari ya sauya salo,  a take a wajan Binafa ta fita daga hayyacinta don ga dukkan alamu nata cikin da kwaɗayin hakan yazo mata, ganin suna ƙoƙarin faɗuwa ƙasa Ahmad ya gyara mata kwanciyarsa cikin faffaɗan ƙirjinsa,ba tare da sunyi aune ba suka raba kansu da kayan jikinsu.
_Nan fa na gudo ganin idanuna sun fara yin dishi-dishi_
Bayan awa ɗaya Ahmad ya taimakawa Binafa suka shiga Bedroom direct Bathroom suka shiga nan sukai wankan tsarkinsu suka fito, Binafa ita ta shirya Ahmad tsaf ya fita don siyo musu kayan maƙulashe, yayinda ita kuma ta zauna ta fara ɗanɗarawa kanta kwalliya ta kece raini.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now