*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_Mum Irfaan_*
*7**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Ringing ɗaya Alhaji Mansur ya ɗauki kiran tare dayin sallama.
Ahmad bai amsa ba yace "Kawu, how?, tayaya zaka aikata hakan?"
Murmushi Alhaji Mansur yayi yace "Yaro, yaro ne, yaro man kaza, kai bakasan maina hango ba, da kasan maina hango ina mai tabbatar maka kaima daka shiga wannan tsarin"
Runtse idanu yayi tare da furzar da iska yace "Kawu yarinyar daka ba kuɗinka ƴar dambara ce, kayi gaggawar nemanta inba haka ba kuɗinka yabi ruwa" kashe wayar yayi gabaki ɗaya ba tare daya jira amsar da zai bashi ba.
Alhaji Mansur tuni cikinsa ya ɗuri ruwa jin abunda Ahmad yace, lambar Binafa ya lalubo ya danna kira jin wayar a kashe yasashi tsurewa, ba tare daya duba lokaci yaja ba na dare ya ɗauki Makulin motarsa ya figa sai anguwar Rimi, yana zuwa ƙofar gidan yaga an saka ƙaton makulli a gidan, tuni zufa ta fara wanke mai fuska tare da cire hula yana kallan ƙofar gidan, ba abunda yake faɗa sai "Innalillahi wa inna ilayyir-raju-un" zuwa ƙofar gidan yayi ya fara knocking amma shiru kakeji, jikin Alhaji Mansur sai rawa yakeyi saboda tsabagin tashin hankali da firgici, zama yayi dirsham a ƙasa yana waige-waige amma babu kowa a anguwar, tashi yayi a zabure ya shiga motarshi ya tayar da ita ya nufa Hotel ɗin daya fara ganin Binafa, yana zuwa yayita faman yi musu kwatancansu ko sunzo sukace su basu ga kowa ba, direct gida ya koma tashin hankali yayi ma ƙwaƙwalwarsa yawa, ɗakinsa ya wuce ba tare daya nema matar gidan ba, wayarsa ya ɗauko ya kira Ahmad ya jita a kashe, wayar mahaifiyarsa ya kira ringing ɗaya ta ɗauka tana faɗin "Allah yasa lafiya Yaya naga ka kirani wajan 12 na dare ne"
Kanajin muryar Alhaji Mansur zaka tabbatar da yana cikin tashin hankali mara misiltuwa, cikin dakiya yace "Ina Ahmad na kira wayarsa a kashe"
Numfasawa tayi tace "Yana ɗaki ya kwanta kasan lokaci yaja"
Alhaji Mansur cikin rawar murya kamar zayyi kuka yace "Dan Allah ki tasheshi zamuyi magana mai muhimmanci dashi ne"
Jin muryarsa wata iri ta tabbatarwa da kanta ba lafiya ba, shiyasa ta katse kiran ta nufi sashen Ahmad, knocking ta farayi sai gashi ya buɗe jikinsa sanye da singlet da boxer, kana kallanshi kasan ba bacci yake ba, da mamaki ya kalla mahaifiyarsa yace "Mom lafiya na ganki da daddare?"
Mahaifiyarsa tace "Ba lafiya ba yanzu Yayane ya kirani yanaso yayi magana dakai" jin ta ambata Yaya yasa gabanshi faɗuwa kardai abunda yake zargi ya tabbata.
Ƙarfin hali yayi ya miƙa hannu ya amsa yace "Inna gama zan kawo miki, ciki ya shiga ya zauna akan 3 seaters ɗin ɗaki yana ƙoƙarin dailing Numbern kawun nasa.
Ringing ɗaya ya ɗauka cikin tashin hankali yace "Ahmad tayaya kasan Binafa ƴar dambara ce?"
Runtse idanuwansa yayi da ƙarfi yace "Ta gudu ko?"
"Eh ta tafi, ta gudunmin da kuɗina masu yawan gaske miliyan 50 fa Ahmad, wallahi yarinyar nan sai tayi nadamar damfarata datayi a rayuwarta saina lalata mata rayuwarta"
Ahmad cikin sanyin murya yace "Kawu kabar komai a hannuna nai maka alƙawari kuɗinka zasu dawo hannunka da yardar Allah"
Shiru yayi ya kasa yadda da hakan, Ahmad yace "Please ka yadda dani"
Cikin tashin hankali yace "Shikenan nabar maka wuƙa da nama"
Murmushi kawai Ahmad yayi kashe kiran, wayarsa ya janyo ya kunnata, wata number ya kira ya kara a kunnansa yace "Kana ina?, hop dai ka shigo garin Kano?"
Shiru yayi yana sauraran na cikin wayar, numfasawa yayi yace "Shikenan ka zauna kusa da wayarka zan turo maka wani abu ka tabbatar kayi yadda yaka mata, nasan zaka iya amma please ka jajirce ta wannan fannin nasan zakaci wuya amma kayi ƙokarin ganin komai ya zamar mana abunda kakeso", shiru yayi yana sauraranso can kuma yace "Saida safe" katse kiran yayi, yay rufda ciki tare da lumshe idanuwansa yana mamaki da ƙarfin hali irin na Binafa, murmushi yahi ya gyara kwanciyarsa ya kwanta.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...