page 9

227 22 12
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *9*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Binafa zama tayi dirsham ta kafe Inno da Baffa tanason ƙarin bayani game da wannan matar, Inno tace "Kinga Binafa wannan maganar bata shafeki ba, babu ruwanki, ita matar da kike gani tana ɗaya daga cikin Family ɗin Hajjah mahaifiyata ne"
  Shiru Binafa tayi itadai bata gamsu da hakan ba, amma ganin tana ƙoƙarin ɓatawa mahaifiyar tatane yasata tashi ta nufa bedroom ɗin zuciyarta babu ɗaɗi.
Tana zama saiga wayar Safwan ta shigo ɗauka tayi cike da sanyin Jiki yayinda ya sanar mata yana ƙofar gida, sanar dashi tayi gatanan zuwa, ta ɗauki Veil ta yana kanta ta fito.
Baffah ne yaga zata fita yace "Ƴar lele sai ina kuma?"
Murmushi tayi tace "Baffah Safwan ne yazo"
Tuni ya ɓata fuska yace "Yaka mata ki dakatar da wannan yaron zuwa wajanki tunda naga alamun babu abunda zai tsinana mana"
Marairaice Fuska tayi tace "Amma Baffah Safwan yana da ƙoƙari daidai shi...."
Ba tare data ƙarasa ba taga Baffah yayi hanyar waje, cikin sarsarfa itama tabi bayanshi, ganin ƙofar gida zai fita yasata ɗanyin gudu ta cin masa tace "Baffah ina zaka?"
Cikin ɓacin rai yace "Tunda har bazaki iya amso komai a wajansa ba to yau zan dakatar dashi akan karya ƙara zuwa ƙofar gidannan in ba haka ba naci mishi mutunci"
Yana gama faɗan haka ya doshi ƙofar gida, yayinda Binafa tashin hankali ƙarara ya bayyana a fuskarta, cikin zafin nama ta mara mai bayyana danta dakatar dashi amma ina, har yaje inda Safwan yake.
Safwan ganin Baffah ya gaho gareshi yayi saurin tsugunnawa yana gaidashi amma Baffah bai ansa ba sai ce mishi yayi "Tashi abunka ba saima ka gaishe dani ba, shin maiyake kawo ka wajan wannan yarinyar?" ya faɗa yana nunamai Binafa, yayinda Binafa Idanunta suka sauya kala tashin hankali ƙarara a fuskarta, cikin rawar murya tace "Baffah dan Allah..."
Bai bari ta ƙarasa ba ya daka mata tsawa yace "Dallah rufemin baki, sakara kawai wacca batasan ciwon kanta ba"
Shiru tayi ta rakuɓe gefe guda tana sauke ajiyar zuciya.
Safwan murmushi yayiwa Baffah yace "Baffah ina zuwa wajan Binafa ne saboda inaso zan aureta"
A birkice Binafa ta ɗago da kanta tana kallanshi, murmushi yayi mata haɗe da lumshe idanuwansa itama batasan lokacin data sakin mai murmushi ba dukda hawayen dake fita daga idanunta, share hawayanta tayi haka kawai ta tsinta kanta da yin murmushi, annurin fuskarta ya gaza ɗaukewa.
Yayinda Baffah ƙwaƙwalwarsa ta daina aiki na ɗan wasu lokuta, cike da tashin hankali yace "An faɗa maka aurar da ita zamuyi ko muna nema mata miji ne?, ka adana kalamanka akan auranka tun wuri kafin Baffah ya fito maka da kalarsa ta ainihi"
Safwan ya buɗe baki zayyi magana kenan Binafa tasha gabansa tace "Dan Allah Safwan kayi haƙuri ka tafi gida zamuyi waya zuwa anjima"
Kafeta yayu da mayun idanunsa yace "Kin tabbata zaki kirani?"
Murmushi taimai tace "Insha Allahu"
Wani Ashar Baffah ya mulmulo tare dayin ƙwafa ya shiga gida, gabaki ɗaya binsa sukai da kallo har saida ya ɓacewa ganinsu, sauke ajiyar zuciya sukayi lokaci ɗaya.
Cike da sanyin murya Binafa tace "Yau ran Baffah ya ɓaci kafi ya sauko wani uban tashin hankali ne, Safwan ban gane kalamanka ba akan Baffah da kace aurena kakeson kayi, alhalin nasan bamu taɓa furtawa kowa kalmar so ba, ko zaka iya yimin bayani domin zuciyata ta gamsu?"

Sauke ajiyar zuciya yayi yana kallanta yace "Tabbas Binafa zuciyata ta daɗe da kamuwa da sonki, ban gano hakan ba sai randa kikai fushi dank, ranar na shiga ɗimuwa da tashin hankali, a zahirin gaskiya zuciyata ta daɗe tana ƙaunarki saidai kuma.." yayi shiru ya kafeta da manyan idanuwansa, yace "Randa naji labarinki a zahiri na tsorata na kumaji ina shakkarki, kuma zuciyata tamin gargaɗin da in fita harkarki saidai na kasa hakan, saboda na ga tsantsan nadama da dana sani a ƙwayar idanunki shiyasa nai alƙawarin canza miki sabuwar rayuwa ta hanyar auranki"
Kallanta ya ƙarayi yace "A zahirin gaskiya Binafa ina miki son da bansan addainsa ba, saidai ina tsoron faɗa miki karkiƙi yadda da buƙata"

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now