*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*19**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Maryam rufa mata baya tayi ta shiga ɗakin Binafar tace "Tashi dan Allah muyi magana"
Ko kaɗan Binafa bata kulata ba ta cigaba da rera kukanta kaɗan-kaɗan, waige-waige Maryam ta fara kamar mara gaskiya tace "Ki tashi muyi magana inada mafita, kuma inaso ki natsu dakyau in miki bayani"
Binafa kanta a kife batace mata ƙala ba, Maryma fa ta ruɗe kar Binafa tayi gigin faɗawa wani a cikin gidan ta banu, ruƙe ƙugu tayi ta bushe da dariya tace "Kai anyi matsoraciya anan wallahi, daga na tsokaneki sai ki zauna kiyita kuka, to tashi wallahi wasa nake miki"
Binafa ɗago da kanta tayi tana kallanta tace "Wallahi fa kikace?"
Murmushi Maryma tayi tace "Eh, so nake naga girman soyayyar da kike nunawa Ya Safwan"
Murmushi Binafa tayi tare da share hawayan fuskarta tace "Nikam dan Allah banason irin wannan wasan ko kaɗan ba girman ki bane"
Ƙoƙarin fita Maryam ta farayi tace "Kece dai baki lura ba amma ai kinsan wasa nake miki" fita tayi tare da bango ƙofar tana harararta, parlour taje ta zauna ta rafka tagumi tana tsakin ƙinyin nasarar da batai ba a wajan Binafa, tasan inhar tabar Binafa tana kuka dole sai an tambayeta dalili kuma tasan dole zata faɗa abunda ke faruwa, da shikenan ta shiga uku ta jawa kanta musiba da kanta, lumshe ido tayi tana tunanin hanyar da zata raba duk wani saurayi dazai runƙa zuwa wajan Binafa itadai burinta Yayanta ya auri Binafa ko Allah zaisa su lasa dukiyar da mahaifin Sultan ɗin ya tara, dan taga zazzafar soyayyar Binafa a zuƙatun ƴan gidab, hakan na nufib zasu bata duk abunda takeso kuma take ƙaunarsa, rausayar da kanta tayi tare da sakin murmushin mugunta ta tashi tayi hanyar waje ba tare datayi sallama da mutanan gidan ba ta kama hanyar komawa nata gidan.Binafa kallan ƙofar data banko mata take, haka kawai hankalinta bai kwanta da Maryam ba, kuma maganar ɗazu tabbas bada wasa ta faɗeta ba saboda taga yanyinta, lallai akwai wani abu a tattare da wannan matar Yayan nata, kuma zatayi bincike zata gano gaskiya.
Wayarta ce ta fara ringing, kallan wayar tayi taga babu suna saita basar ba tare data ɗauki wayar ba, ganin har anyi 2 missed calls yasata ɗaukan na ukun tare da kara wayar a kunnanta tayi shiru.
Cikin sassanyar muryarsa yace "Ko ki kirani kiji ya na sauka lafiya ko, saboda baki damu dani ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tace "Ya Ahmad tunda ka tafi na kasa samun natsuwa dan Allah kayi haƙuri da abunda ya faru wallahi bansan ranka zai ɓaci ba, kuma Ya Safwan yazo yana ta tambayata akan maiya faru ka tafi...."
Katseta yayi da cewar "Me kikace masa?"
Shiru tayi sannan tace "Na kasa faɗa masa gaskiyar lamarin.."
Ƙara katseta yayi da cewar "Mai yasa?"
"Hmm" kawai Binafa tace , numfasawa tayi kaɗan tace "Ina fatan ka koma gida cikin ƙoshin lafiya"
"Lafiya ƙalau"
Kowa shiru yayi yana tunani a cikin zuciyarsa, Binafa ganin an turo ƙofarta yasata saurin cusa wayar a pillow tana mazurai.
Safwan ne ya shigo yace "Sorry na shiga no excuse ko"
Murmushi kawai tayi tana sosa kanta, kallan idanunta yayi yace "Mai yasakaki kuka?"
Hannu ta sa tana goge fuskartata tace "Babu komai wallahi, kawai ƙwaro ne ya shiganmin ido"
Safwan ganin kamar Binafa duk a tsorace take yace "Binafa me kike ɓoyewa naga duk kin tsorata" kusa da bedside drawer ɗinta ya zauna yana kallanta, yayinda ita kuma ta zauna a gefen gadonta ƙirjinta na bugawa.
Cikin ƙarfin hali tace "Kai Ya Safwan, babu komai fa kaine dai kawai kake tunanin wani abun".
Shiru yayi yana kallanta yana nazari.
Cikin shagwaɓa tace "Ya Safwan wannan kallan fa?, sai kace yau ka fara ganina"
Murmushi yayi yace "Ina wayarki" gabanta ne yayi mummunan faɗuwa ita sam tama manta da Ahmad da suke waya.
Tashi tayi ta fara dube-dube tana faɗin, ni banma san inda na sakata ba.
Ba tare dayace uffan ba ya zaro wayarsa a aljihunsa ya fara kiran wayar.
Kallanta yayi yace "Naji Call waiting" a tsorace tace "Call waiting kuma?" ta faɗa tana dafe ƙirjinta, can kuma ta saki yaƙe tace "Nifa sam nama manta Mommy tace na bata wayata zatai amfani da ita"
Ta faɗa tana lumshe ido dan tasan inhar ya kalli ƙwayar idonta zai iya gane cewar ƙarya take, kwanciya tayi tare da janyo blanket tace "Ya Safwan inna tashi daga bacci mayi maganar, wallahi nagaji yanzu haka" tana gama faɗan haka ta tusa kanta cikin Blanket ɗin tana sauke ajiyar zuciya, tana tunanin duk abunda ya faru Ahmad yanaji kenan, da biyi yaƙi kashe wayar kenan, shiru tayi tana lumshe ido tana jiran Safwan ya fita ta janyo wayarta ta kashe gabaki ɗayama ta huta.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
خيال (فانتازيا)Binafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...