page 4

270 29 1
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)'''

*~Na Mallakin~*
              *Mum Irfaan*
     A.k.a   *_Er-gafaii_*

*Follow me on Wattpad-Mumirfaan*

My Gmail Account
Www.mumirfaan77@gmail.com

                             *4*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Sai yamma lik'is Binafa suka dawo, tana shigowa gida ta yadda ledar dake hannunta tana fad'in "Wash nagaji Wallahi, Kai Inno haka Kaduna take dakyau da tsari, Kai ai yau Nasha yawo"

Inno ce Tace "Kinga rufamin asiri wa Kika sani anan dahar Zaki fita tun safe sai yanzu, kin sakamu cikin zullumi hankalin mu ya gaza kwanciya"

Dariya Binafa tayi tace "Kai Inno sai kace wata k'aramar yarinya, Wallahi D'azu Ina fita Nayi babban kamu wasu 'ya'yan masu kud'i nai Karo dasu muka k'ulla k'awance, in tak'aice Miki su suka Jani mukasha yawo Kinga Wannan ledar" ta fad'a tana janyo ledar Tace "Ko Sisi na babu a ciki su suka siyamin komai" ta fad'a tana washe Baki.

Inno shiru tayi tana nazari Tace "Kinga Binafa ki kiyaye mutane, Haka kawai daga ganinki zasu kashe Miki Wannan uban kayan kud'in, waya fad'a Miki Yanzu ana yadda da Mata Suma"

Dariya Binafa tayi Tace "Inna Kenan, ai ba Dan Allah suka taimakamin ba, K'arya na banka musu nace a London muke zaune business ne ya kawo mu Nan, so ga dukkan alamu sunaso su runk'a mu'amala da masu kud'in gaske shiyasa na fad'a na maze" matsowa kusa da Inno tayi tace "Ba Wannan ba Inno Yanzu abunda ke gabana shine School Dan Wallahi inaso Naga na k'ware da turanci, Yanzu ba laifi tunda Ina duba k'amus nasan wasu abubuwan da dama, Ni dai Yanzu Ina Baffa yazo a dandale Zan shiga wata makaranta naji su Azeeza sunce turawane ke koyarwa ma, Amma tana da tsada, Ni ban damu ba inhar buk'ata ta zata biya"

Baffa ne yayi gyaran murya lokacin daya nufo inda suke yace "Wacece Kuma Azeeza dahar ta fad'a Miki makarantar datafi ko wace makaranta kyau a Kaduna"

Murmushi Binafa tayi tace "Yar ministern Ilimi ce kagako zatasan makarantu da dama, Yanzu idan na samu nai registration sai na siyo dogon Hijab yadda baza'a runk'a ganin Uniform d'ina ba, Kar a rainani"

Inno Tace "To kinada takaddun Primary ne?".

Murmushi Binafa tayi tace "Inno Kenan, ai yanzu inhar kana da kud'i komai zaka iya siya a rayuwa, Zan biya aimin komai harda certificate d'in J.S.C.E, Yanzu kawai Zan fara daga S.S 2 ne yadda zanyi wuf na zana WAEC"

Jinjina Kai sukayi, Nan suka hau lisaafin nawa zasu kashe, Nan aka ware kud'in da Binafa zata fara zuwa makaranta.

Murmushi Alhaji Mansur yayi yace "Shikenan Nagode Ahmad, karka manta inkaje gida ka gaishemin da k'anwata"

Murmushi yayi yace "Insha Allahu Kawu, Nagode a gaida mutanan gidan" motarshi ya Shiga ya tayar ya nufa Jahar Adamawa, sosai Binafa ta tsaya mishi arai kwana biyu yadda case d'inta ke yawo jaha-jaha, murmushin gefen Baki yayi Yana tunanin yadda zai Mata kaca-kaca duk Randa Allah yasa ya  kamata dumu-dumu da damfarar wasu, k'arawa motar speed yayi Dan yanaso ya Isa gida da wuri.

Kana kallanta zakasan a gajiye take, gashi fuskarta ta canza kala ta koma ja saboda zafin da aka kwad'a, hannunta ruk'e da form ta shigo gidan, Zama tayi kan kujera da6as tana faman lumshe idanuwa, ganin Inno na jera abinci saman Dinning yasata fad'in "Kai Inno yau Nasha kwa-kwa, Dak'yar na samu suka bani Form d'insu Wai ban iya komai ba, aini bansan ana wani interview fa nasa a sakamin A, A a fake results d'innan, uhm sai gashi sun fara cillamin turanci Mai mugun wuya, ai Wallahi tuni na baje a k'asa na fara musu borin K'arya nace ai aljanuna basusan a Sakani a gaba a tambayeni saidai in za6a Wanda zaimin su barmu tare, to dama akwai wani tunda naje yayita kallona nasan ko Bai fad'a ba nai masane, shine fa na tashi na kakka6e jikina na nunashi nace shine zaimin, Ashe assistant Director ne, aiko muna Shiga Office d'in ban 6oye Masa komai ba na fad'a Masa, ai Wallahi Inno tuni yacemin babu damuwa ai Angama inhar Zan soshi, in tak'aice Miki yace naci interview ranar Monday Zan fara zuwa"

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now