Page 26

199 21 12
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *26*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Safwan ganin Binafa bata da niyyar amsa mishi yasashi cewa "Muje to",  jikinta a matuƙar sanyeye ta shiga, tana shiga ta kalli Office ɗin Mahbub, aiko sai suka haɗa ido yana tsaye hannunsa cikin aljihun wandansa yana jifanta da wani irin kallo, cike da tsoro fargaba ta sadda kanta ƙasa Allah-Allah take Safwan yabar makaranta.
Bayan Safwan ya daidaita Motarsa akan Titi ya kalli Binafa yace "Wai meke damunki ne?, naga duk kin wani firgicemin ne"
Hawayan data maƙalene suka sauko mata kan kuncinta, share hawayan tayi ba tare datace dashi Uffan ba, wayarta na hannunta tana gwada layin Ahmad amma har yanzu No Answer, kallan screen ɗin wayarta kawai take, domin ta ƙosa ta ganta a gida.
Sun ɗauki lokaci mai tsayi kafin su isa gida, yana zuwa ƙofar get ɗin gidan ya fara danna Horn, daidai lokacin da Ahmad shima ya danno tashi motar, kamar ance Binafa ta ɗaga ido ta hango motar Ahmad tana tahowa garesu gabanta ne ya tsananta faɗuwa, idanunta suka ciko da ƙwalla, batason Safwan ya gane halin datake ciki na ganin Ahmad shiyasa ta sadda Kanta ƙasa tana wasa da wayarta.
Safwan kuwa ganin Ahmad ne yasashi tsuke fuska tare dayin gajeren tsaki, ganin yadda Binafa ko kallan inda Ahmad batai ba yasashi jin daɗi a zuciyarsa tabbas ya yadda da Binafa Ahmad baya gabanta, shine dai birnin zuciyarta, ganin an buɗe get ɗin gidan ya kunna kan motarsa ya shiga, haka zalika Ahmad shima ya mara musu baya.
Safwan yana gama Parking ya fito zai wuce inda Ahmad ke tsaye, murmushi Ahmad yayi yace "Haba Abokina,ba faɗa maiya kawo gaba, na ɗauka komai aiya wuce"
Jin haka Safwan sai yayi tunanin wataƙil Ahmad ya haƙuda da Binafa ne shiyasa yace haka, murmushi ne ya suɓucewa Safwan yace "Aina ɗauka kana fushi danine shiyasa nakejin kunyar yi maka magana abokin ƙwarai"
Murmushi Ahmad yayi, sai yanzu ya tabbatar da maganar Binafa na cewar Safwan yabar mishi Binafa.
Suna cikin maganane saiga Alhaji Modibbo ya fito ganin Safwan ya kirashi tare da aikenshi wani gun tunda Mahmud bayanan ya tafi wajan aiki, kaɓar saƙon yayi cikin girmamawa, kallan Ahmad yayi yace "Ka shiga ciki bari naje na dawo Alhaji ya aikeni"
Ɗaga mishi kai yayi ya nufa part ɗinsu Mahmud kasancewar shima Ahmad yanaso ya zama tamkar ɗan gidan bashi da shamaki da wani abubuwan gidan da dama.
Binafa tana zaune cikin mota ta kasa fitowa dan ba ƙaramin kunyar Ahmad takeji ba, ga tsoro da fargaba da suka shigeta farat ɗaya.
Cikin tafiyarshi ta ƙasaita yazo saitinta, ganin tana kuka sai tausayinta ya dirar masa a cikin zuciyarsa, kauda kanshi yayi gefe ɗaya yace "Ki sameni ɗakinsu Mahmud" yana gama faɗa mata haka yayi gaba abunshi.
Binafa binshi tayi da kallo har saida ya ɓacewa ganinta, Handbag ɗinta ta ɗauko ta nufa part ɗin Mahmud, tana zuwa ta tura ƙofar ɗakin.
Ahmad ta hango zaune kan 3 seaters ya ɗaura hannu aka yana tunanin wani abu, cikin sanyin murya tai mishi sallama, saman leɓansa ya amsa sallaman yana kallanta, kanta a ƙasa ta ƙaraso inda take, muryarta na rawa tace "Ya...Ah..mad gani" ta ƙarashe faɗa jikinta na rawa.
Miƙewa yayi ya kamo hannunta ta fara ƙoƙarin janyewa, wani kallo ya wurgeta dashi tai sauri runtse idonta, zaunar da ita yayi kan 3 seaters ɗin daya ke zaune shima ya zauna gab da ita, ƙoƙarin matsawa ta farayi amma ta kasa ganin tana ƙarshen kujeranne.
Hannunta ya ruƙo ya fara murza mata cikin wani irin salo, gabaki ɗayansu saida tsigar jikinsu ta tashi, Binafa idanunta suna rufe ruwan hawaye na yawo kan kuncinta.
Jikinta rawa ya farayi ganin irin abunda Ahmad ya farayi mata, takurewa tayi waje ɗaya ta rushe mai da kuka tace "Dan Allah ka saurareni, karka yankemin wani hukunci na daban, bazan iya jura ba wallahi, dan Allah karkaimin wani irin kallo"
Ta ƙarashe faɗa numfashinta na barazanar ɗaukewa.
Shi kanshi Ahmad ɗin saida ya shiga cikin tashin hankali, abunka da baka sababa, cikin wata irin murya wacca Binafa bata sanshi da ita ba yace "Na kasa Binafa, na kasa yin fushi dake, na rasa dalilin hakan, tunda na barki a makaranta hankalina yaƙi kwanciya, idan na tuno cewar na ganki kwance a ƙirjin...." runtse ido yayi ya kasa ƙarasawa idanunsa sunyi jajir, kallanta yayi ido cikin ido Binafa tai saurin runtse ido dan bazata iya cigaba da kallanshi a haka ba.
Cikin sanyin murya yace "Binafa bazan iya barikin cigaba da zuwa wannan makarantar ba, saboda nasan waye Mahbub, tunda ya ƙyalla ya ganki to tabbas sai ya samu abunda yake buƙata daga gareki sannan zai ƙyaleki, nidai alfarma ɗaya zakimin shine ki yarjemin na turo magabatana"
Hawayan fuskarta ta goge murmushi yayi nasarar bayyana a fuskarta tace "Nima Ya Ahmad makarantarnan ta fitanmin arai, wallahi dama na gama ayyanawa bazan ƙara zuwa wannan makarantr ba, domin na lura tas za'a iya yiwa student fyaɗe babu abunda mutum zai iya"
Kallanta yayi da idanunsa da har yanzu sunƙi washewa yana murmushi yace "Tabbas hakane, barin irinsu Mahbub a doron ƙasa tashin hankaline ma"
"Uhmm" kawai Binafa tace, ta fara ƙoƙarin gyara ɗan kwalin kanta saboda yaɗan zame.
Tashi tayi tace "Bari na shiga ciki, domin Mommy ma batasan na dawo ba"
Shima miƙewar yayi yace "Nima tafiyar zanyi, don inaso naje gida ayau da yardar Allah, inaso zan faɗawa ba Umma nane kinsan Allah yayiwa mahaifina rasuwa".
Kallanshi tayi cike da tausayinsa tace "Ayya Allah ya jiƙansa ya gafarat masa"
Murɗa handle ɗin ƙofar tayi, yayi saurin saka hannunsa kan nata, waigowa tayi da alamun tambaya sai kawai ta tsinta bakinsa cikin nata, zaro idanu tayi gabanta na tsananta faɗuwa amma ta kasa hanashi saboda ganin yadda ya firgice mata.
Ya ɗauki lokaci mai tsayi sannan ya saketa shi kanshi kunyar haɗa ido yakeyi da ita ya rasa meke damunshi haka, juya mata baya yayi baison ya kalleta dan ba ƙaramin kunyarta yakeji ba a halin yanzu, ya rasa mai yasa bayyi controlling kanshi ba akan haka.
Binafa ganin yaƙi juyowa kawai sai abun yaso bata dariya namiji da kunya, duk da itama bazataso ta haɗa idanun dashi ba, cikin saur ta murɗa handle ɗin ta fita tana sauke ajiyar zuciya, yaudai ta rasa waca rana zata kirata, lokacin da suke tare da Mahbub ta shiga cikin tsoro da tashin hankali, amma yanzu da ta kasance da Ahmad ta tsinci kanta cikin matsinanciyar sha'awa, cikin sauri ta ƙarasa parlour sallama ɗauke a bakinta, ganin ba kowa ma'aikatan gidanma suna nasu part ɗin yasata ƙarasawa ɗakin mahaifiyarta.

Tana shiga ta canza fuska, mahaifiyarta kallanta tayi tace "Lafiya Autata?"
Binafa kamar zatai kuka tace "Nifa Mommy daga yau bazan ƙara zuwa jami'a ba na haƙura"
Cike da mamaki ta kalleta tace "Kamar yaya?"
Shiru tayi tana tuno mata baki, tace "Jami'ar da duk ƴan iskane"
Shiru Mommy tayi tana nazarin maganarta tace "Shikenan tashi ki tafi idan mahaifinki ya dawo zamuyi magana, sannan ki daina yiwa jami'a ƙudin goro domin akwai nagari akwai ɓata gari"
Tashi tayi a gajiye ta nufa ɗakinta.
Tana shiga bayi ta shiga danyin wanka, tana fitowa ta canza kaya tare dayin sallah, tana idarwa ta kwanta tare da rungume pillow tana tunanin Moment ɗinta da Ahmad, murmushi kawai tayi tanaso itama tai aurannan taji ya akeji, shiru tayi sai kuma murmushi shinfiɗe a fuskarta tare da tusa kanta cikin pillow.

Ahmad tunda yabar gidan ya kasa samun sukuni domin bayason Binafa tai mishi wata irin fassara ta daban, so biyar yana ɗaukar wayarsa yanaso ya kirata amma yana fargabar kiran, kallan wayarsa yayi screen ɗin wayar hoton Binafa ne a ciki wanda ita kanta Binafar batasan yana da hoton ba, tayi matuƙar kyau yadda mai karatu baya tsammani, wajan message ya shiga yana tunanin saƙon da zai tura mata, shiru yayi yana tunani, duk da yasan bazawarace tasan maza da dama amma ai bai kamata yayi mata haka ba sai kimarsa ta ragu a idanunta kuma zargi ya shiga tsakaninsu, duk da ita yana ganin hakan ba komai bane a wajanta a matsayinta na wacca ta taɓayin aure da dama amma shifa?, zatai tunanin ko yanabin ƴan matan banza ne, shiru yayi yana tunanin abunda zai rubuta mata, can ya tura mata da saƙo kamar haka _"Bansan da wani irin baki zan baki haƙuri ba, nasan nai miki laifi mai girma amma dan Allah kiyi haƙuri dan Allah karki zargeni wallahi ba haka nake ba ko kaɗan, sonki ne ya jani da aikata hakan amma insha Allahu hakan bazata ƙara faruwa ba, please i apologized"_

Ƙarar shigowar message ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga, tana ganin taga Ahmad ne ya turo buɗewa tayi ta karanta, dariya abun ya bata, dan tasan tabbas wannan ne karo na farko da Ahmad ya kasance da mace domin taga alama, ƙara nanata text ɗin tayi saita tura wayar ƙarƙashin pillow tana dariya ƙasa-ƙasa, tana sane taƙi  yimai replay dan kawai ta ɗaga mishi da hankali.

Ahmad kuwa yana ta jiran tsammani harya gaji ya kwanta yana tunanin wani irin hukunci Binafa ta ɗauka akanshi, sannan wani irin kallo zata runƙa jifanshi dashi, tsaki yayi yana mai danasanin aikata abunda yayi mata.

Mahbub lumshe ido yayi tunanin Binafa ya cika mishi ƙwaƙwalwarsa yana tunanin mai yasa zuciyarsa bata yanke shawarar marinta ba ta ɓage da shafan shashin jikinta wanda har yanzu ya kasa manta jikin nata, tsaki yayi yana ganin tabbas yanzu zuciyarsa ta zama raguwa dahar mace zata maresa ya kasa ramawa, shiru yayi yana tunanin wata yarinya data mareshi a take a wajan ya lalata mata budurcinta shine sanadiyarsa na maida yarinyar tantagararriyar karuwa harta tattara tabar gidan iyayanta duk da sun kasance masu arziki.
Ƙwafa yayi tare da busa shisha ɗinsa yana faɗin "Tabbas kinyi kuskure da kika ɗaga hannu kika mareni, wallahi tallahi marin da kikaimin bazai tashi a banza ba"
Wayarsa ya ɗauka ya kira wata matashiya, tana ɗauka yace "Inaso na sakaki wani aikine, idan har kikaimin to ina miki albishir da kin samu Mahbub Madaki kin gama"
Ciki da ɗoki da zumuɗi wannan yarinyar tace "Ka faɗamin koma menene nai maka alƙawarin aikatashi"
Murmushi yayi yace "Naga wata Beb mai zafin gaske, saidai haƙona bazai taɓa cinmata ba domin yarinyar daga ganinta ƴar gidan manya ce, inhar nace zan yagata da ƙarfin tsiya to tabbas zan samu matsala duk da nasan wanene ni, saidai inaso malaminki yayimin aiki akanta"
Taɓe baki tayi tare da hararar wayar, abu ɗaya ta tuna na cewar zai mallaka mata kanshi, cikin dakiya da ɗacin kishi tace "Shikenan baka da damuwa, anjima zanje kusfa zanje nai mishi bayani, saidai kaimin alƙawari kamar yadda inka ɗandana mace so ɗaya baka maimaici haka nakeso ka rabu da ita da zaran ka sameta, domin naga alama yarinyar ta tafi dakai tunda baka taɓa neman abu ka rasa ba a gun ɗiya mace"
Murmushin rainin hankali yayi mata yace "Baki da damuwa, nidai burina yarinyar ta kawomin kanta"
Nan ta tabbatar masa da aikin gama ya gama, sallama sukai ya ajiye wayar, tashi tsaye yayi yana safa da marwa tare da furta "Fatima Madibbo" murmushin gefen baki yayi tare da harɗe hannayansa ta baya.

*More comments more typings*

*#Team Ahmad and Binafa*
*#Team Binafa and Safwan*

*#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*

_Ƴar gafai_

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now