page 6

211 21 3
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_Mum Irfaan_*

 
                               *6*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Binafa ganin tabbas da gaske kiran Police zayyi su tafi da ita yasata ƙarfin halin faɗin "Dakata, basaika kiramin hukuma ba, muje kawai can" ba tare data jira abunda zai faɗa mata ba ta zagaya ta buɗe motarsa ta shiga ta zauna, bin ta yayi da idanu, ba tare daya furta komai ba ya shiga ya tayar ya kama hanyar headquarter, hankalinta naga wayarta ta cigaba da chatting saika rantse babu abunda ke damunta alhalin tsoro ne fal cikin ranta.
Ahmad ba tare daya kalleta ba yace "Ki saida wayar nan, ko ki kashe ki daina amfani da ita"
Ɗagowa tayi ta kalleshi taga hankalinshi naga Titi tai banza dashi.
Ya buɗe baki zayyi magana kenan wayarshi ta fara ruri, duba wayar yayi yaga ba suna, ganin yana tuƙi yasa wayar a handsfree yana sauraron na cikin wayar, muryar Alhaji Aminu ita ta doshi kunnan Ahmad da Binafa, Binafa batasan lokacin da ta dafe ƙirjinta ba tana faɗin "Na shiga Uku", wani kallo Ahmad ya jefeta dashi batasan lokacin datayi gum da bakinta ba gabanta na tsananta faɗuwa.
  Muryar Alhaji Aminu ce ta katse musu hanzarinsu yana faɗin "Ranka ya daɗe shin har yanzu ba'a ga shegiyar yarinyar nan ba ko, mai zai hana ayi tracking wayar data ɗauka tunda inada komai na wayar, shine zai tai maka mana wajan inda take cikin sauƙi"
  Cikin Binafa ne yayi wani ƙugi har saida Ahmad ya ji, murmushi kawai yayi ba tare daya kalleta ba ya maida hankalinsa ga wayarsa, gyaran murya yayi yace "Alhaji inaso ka turomin da komai na wayar domin musan inda take ɗin, kuma insha Allahu za'ayi nasarar hakan, yanzu dai karka ba kowa ka sakomin shi a motor, yarinyar kuma karka damu domin na kusan kamata insha Allahu"

Binafa batasan lokacin data sauke nannauyar ajiyar zuciya ba tare da hamdala cikin ranta, lumshe idanuwanta tayi yayinda gabanta na tsananta faɗuwa, tasan in kowa yana barinta Alhaji Aminu bazai taɓa ƙyaleta ba, buɗe idon da zatayi taga Go Slow ga cunkoso na wajan, kallan Ahmad tayi taga hankalinshi naga Titin, waigawar da zatai ta hango gidan wanka can nesa dasu, ruƙe cikinta tayi ta saki wata ƴar ƙara kaɗan tana faɗin "Wayyo cikina, dan Allah in ba damuwa zan shiga gidan wankan can"
  Ba tare da Ahmad ya kalleta ba yace "Me zakiyi a gidan?"
Tuno mai baki gaba tayi tace "Me akeyi a gidan wankan?, ni dan Allah ka barni naje na dawo"
Ba tare daya kalleta ba yace "Ki maza kafin Go Slow ɗinnan ya ragu, kuma saura ki gudu"
Bata tsaya bashi amsa ba ta banko mai murfin motar tana sauri-sauri kamar gaske.
Ahmad tunda yaga ta fita yayi murmushin gefen baki yace "Guduwa zaki"

Binafa kuwa tunda ta tabbatar Ahmad bai ganinta ta ɗauki waya ta kira Hamida tai mata kwatancan inda take dan tazo ta tafi da ita.
Ba'a ɗauki lokaci ba saiga Hamida  tazo, waige-waige Binafa ta farayi ganin babu mai ganinta tayi wuf ta shiga cikin motar tana sauke numfashi, Hamida kallanta tayi tace "Beb daga ina haka na ganki a nan gurin alhalin bakisan garin ba?"
Furzar da iska Binafa tayi tace "Bazaki gane ba, yanzu dai bi damu ta cikin G.R.A kar mubi Titi zan baki labari"
Ba musu Hamida ta kutsa ta cikin G.R.A tana mamakin maiya kawo Binafa wajan itada ba tasan gari ba.
Murmushi Ahmad yayi ganin Binafa ta gudu ɗin da gaske, motarsa ya tayar ya nufa hanyar Adamawa kar yayi dare a hanya.

Tunda Hamida tazo ƙofar gidansu ba tare da Binafa ta jira ta gama parking ba tayi wuf ta sauka tace "Zamuyi waya, Thank you", bata jira amsarta ba ta shiga cikin gidansu, tana shiga ta zube a tsaƙar ɗakin tana maida numfashi, kallan Inno da Baffah take ganin sun zuba mata idanuwa, idanunta ne suka ciko da ƙwalla tace "Inno mun shiga uku, ashe ƴan sanda nemanmu suke ruwa a jallo bamu sani ba, wallahi yau an kamani guduwa nayi"
Gabaki ɗayansu saida suka tsorota da kalaman Binafa barinma Inno akwai ta da tsoro, Baffah ne yayi ƙarfin halin faɗin "ban fahimceki ba, maiya faru?"
Ba tare da ɓata lokaci ba ta kwashe komai ta faɗa musu, ta ɗaura da cewa "Baffah wallahi jaha-jaha ake nemana ni na shiga uku" ta faɗa tana fashewa da kuka, cikin kuka tace "Wallahi Baffa suka kamani baza suyimin da sauƙi ba, kuma kotu za'a kaini" ta faɗa tana goge hawayan fuskarta.
Inno shiru tayi hankalinta a tashe, Baffah ma haka, Baffah ne yayi ƙarfin halin cewa "Yanzu kinga zaman Kaduna bai ganmu ba, saidai mu canza wata Jaha ɗin"
Inno tace "Tabbas kuwa, yau kuwa zamu bar Kaduna ba sai gobe ba, tunda har hukuma tasan kina cikin garin nan"
Baffah yace "Wani hanzari ba gudu ba, yanzu Alhaji Mansur ɗinnan haka zamu rabu dashi ba tare da muci sisin sa ba?"
   Inno tace "So kake a cafke ɗiyar da muka mallaka guda ɗaya tal a duniyar nan?"
Baffah yace "Amma fa kinga yadda yake da tarin dukiya, kamata yayi ko yayane mu yaga"
Binafa tuni ta lula duniyar tunani ta zabga uban tagumi, taɓata Inno tayi tace "Shawarar me kika yanke ɗiyar albarka?"
Numfasawa tayi tace "Inno kawai shawarar da na yanke zan kirashi anjima ince akwai wani harƙalla da zamuyi da wasu maƙudan kuɗin idan zai zuba hannun jari, in kasa miliyan ɗaya zaka samu miliyan uku, ina ganin wannan itace hanya mafi sauƙi da zamu karɓa kuɗaɗansa ta cikin sauƙi tunda naga ɗan san banza ne"
  Sosai Baffah yayi farin cikin mara misltuwa ganin an samu maslaha cikin sauƙi, Inno ma ta gamsu da bayaninta, tashi Binafa tayi duk da babu kuzari a jikinta ta nufa bedroom ɗinta danyin wanka.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now