*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*36**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_**Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1QMurmushin manya Alhaji Modibbo yayi yace "Wata ɗaya kacal aka saka, dan haka sai kaje kaita shirye-shiryen biki"
Sosai Safwan yaji daɗin haka, sosa ƙeya yayi yace "Allah ya saka da Alkhairi Daddy, Allah yasa kafi haka, Allah kuma ya ƙara maka nisan kwana"
Cike dajin daɗin addu'arsa yace "Ameen thumma ameen, tashi kaje Allah yayi maka albarka"
Tashi Safwan yayi farin ciki fal cikin zuciyarsa shima ya kusan zama ango insha Allahu.Abun nema ya samu wunin ranar Safwan sai kiran ƴan uwa da abokanan azziki kawai yayita yi yana shaida musu sa ranar bikinsa, tsiya wajan Mahmud da Ahmad kuwa ba'a magana, saidai yayi musu murmushi kawai ya kashe wayar.
Binafa kallan Ahmad tayi cike da zumuɗi tace "Ya Ahmad ina matuƙar godiya da irin wannan kulawar taka a gareni, Allah ya barmu tare har ƙarshen rayuwa, Allah kuma ya kaɗe fitina a tsakaninmu"
Lumshe ido yayi yace "Ameen thumma ameen, ai duk abunda nai miki kamar naima kainane Matata"
Murmushi kawai Binafa tayi tana ɗaga kanta sama tanaso ta hango su Baffah da suke ƙoƙarin nufosu, domin kuwa Ahmad yayi duk wani iya bakin ƙoƙarinsa dan ganin su Baffah sun fito kamar yadda Binafa ta buƙata, bayan ƴan rubuce-rubuce da kuma signing ɗin da sukai aka sallamesu suka nufo inda aka nuna musu inda su Binafa ke tsaye suna jiransu.Binafa ganin Inno yasata rugawa da gudu tai hugging ɗinta tana mai matuƙar jin daɗin ganinsu, saidai duk sun lalace sun fita hayyacinsu kamar ba Inno da Baffah ƴan gayu ba masu ji da kuɗi duk da suna da haske amma saida hasken nasu ya dishashe saboda horuwar da sukai.
Inno cike da sanyin jiki da matuƙar dana sani a tattare da ita itama ta rungume Binafa hawayan na dama suka sauka akan kafaɗun Binafa, tace "Lallai Binafa ke ɗin ƴar halak ce wacca bata manta alkhairi, ban taɓa tunanin zaki ƙara waiwayanmu ba a rayuwarki, sai gashi da kanki kinsa Mijinki yabi duk wata hanya da yasan za'a sallamemu cikin sauƙi, mun gode Allah ya biya muku buƙatunku na alkhairi ya baku zuri'a ɗayyiba, Allah ya saukeki lafiya Allah yayi miki albarka"
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...