*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*27**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Binafa safa da marwa kawai takeyi a cikin ɗakinta, tunani take tayaya zata ɓullowa al'amarin Ahmad, wazai saurareta game da wannan maganar, tabbas tana da gagarumin aiki agabanta, Mahaifin Safwan ne ya faɗo mata cikin rai, batasan lokacin da murmushi ya suɓuce mata ba, zama tayi akan Stool tana jujjuya maganar da zata faɗawa Alhaji Lukman danya aminta da maganarta, kallan agogon ɗakin tayi taga ƙarfe uku da rabi, gyara zama tayi tanaso da la'asar saita tafi daganan saita kwana wajan Lanika, jin motsin wajan ƙofarta yasata ɗan ɓata rai, a tunaninta Safwan ne, cikin sanyin murya tace "Waye?"
Mahaifiyarta ce ta turo ɗakin tace "Kizo mahaifinki na kiranki"
Ba musu ta miƙe tare da ɗauko Veil ɗinta cikin wardrobe tabi bayanta.
Cikin ƙawataccan parlournsa ta shiga sallama ɗauke a bakinta.
Yana kishingiɗe kan wata shu'umar dadduma hannunsa nakan Tuntu tamkar wani basarake, amsawa yayi fuskarsa a sake yace "Auta zonan" ganin ta zauna can nesa dashi.
A hankali ta taso tazo inda yake domin tasan maganar da zai mata bazata wuce taƙin makarantar datayi ba.
Gaishe dashi tayi ya amsa, kallanta yayi dakyau yana nazari yace "Autata!, shin wani abune ya faru a makarantar dahar kikace bazaki ƙara zuwa ba?"
Ɗaga kanta tayi sama ba tare datace Uffan ba, wasa ta farayi da gashin gefen daddumar tace "Ni Daddy na haƙura da jami'ar nan, da tun farko haka ake fuskantar matsaloli da dama a ciki da ban ansa cewar zanyi karatu a cikinta ba"
Numfashi yaja mai ƙarfin gaske zuciyarsa na bugawa domin baisan maiya faru da Binafar ba dahar ta faɗa hakan, domin yasan Binafa yarinyace mai burin cigaba da makaranta, amma lokaci ɗaya aka samu wani ya rusa mata burinta.
Cikin tattausar murya yace "Binafa ki faɗamin abunda ya faru, ni kuma nai miki alƙawarin bi miki hakkinki koda kuwa Governor ɗin Kano ne"
Murmushi maganar ta bata, zuciyarta na mata gargaɗi akan karta faɗa, numfasawa tayi tace "Daddy nida wani lecturer ne, daga zuwana ko zama banyi ba ya fara ƙoƙarin ɓatamin tarbiyata" tana ƙarashe faɗan haka ta sadda kanta ƙasa.
Tuni Alhaji Modibbo ya gane zancan da Binafa take mai, nan take ranshi yayi mummunan ɓaci yace "Wanene shi?, wanene Ubanshi a faɗin Kano?, muke da Kano muke da jama'ar dake cikinta bamu takurawa mutane ba shine ni za'a takurawa tawa ƴar"
Binafa tace "Allah ya huci zuciyarka mahaifina, amma ga dukkan alamu yadda yake wasu abubuwan tabbas ya samu ɗaurin gindi daga samane, domin Izzarsa ta nunamin haka"
Furzar da iska yayi mai ɗumin gaske yace "Ya sunanshi?"
Maganar Ahmad ta tuno lokacin da yake faɗan sunanshi, kallan Mahaifinta tayi tace "Naji kamar ana ce mishi Mahbub Madaki"
Maimaita sunan Alhaji Modibbo yayi, can kuma sai yayi murmushi yace "Jeki abunki, gobe ki shirya kije makarantarki babu abunda zai faru"
Binafa a ɗan tsorace ta kalli mahaifin nata tace "Daddy tsoronsa nakeji wallahi, nikam na yafe da karatun" ta faɗa kamar zatai kuka.
Murmushin manya yayi yace "Daga yau shine zai runƙa jin tsoronki bake zakiji tsoronsa ba, koda kuwa Izzarsa tafi ƙarfin Nigeria"
Gyaɗa kanta kawai tayi badan ta gamsu ba ta miƙe cike da rashin kuzari ta fita.
Mahaifiyar Binafa kallan Mijinta tayi Bayan Binafa ta fita.Cike da ɓacin rai tace "Alhaji Wallahi wannan yaron ko kaɗan bashi da kirki, anya yasan ɗiyarka ce kuwa?"
Murmushi Alhaji Modibbo yayi yace "Yasani tas, akuyanci da akace yanayi yakeso ya tabbatar min da hakan, domin tare da Safwan sukaje kuma yasan ko wanene Safwan a wajena"
Jinjinawa tayi tace "Lallai yaron nan, ka faɗa mishi in bai fita harkar ɗiyata ba, wallahi tun daga kan sarautar da suke tunƙaho dashi har zuwa lecturer ɗin da yake zan saka a soke tunda bashi da mutunci"
Alhaji Modibbo yace "Barni dashi, koda wasa karki sake ki faɗawa mai martaba inba haka ba kince masane ya sauke Madaki a matsayinsa, kuma kinga hakan zai janyo miki baƙin jini wajan kishiyar mahaifiyarki tunda mahaifin Mahbub ƙaninta ne"
Taɓe baki tayi tace "Kana kallo yaro yanaso ya lalata yaran al'umma, yanzu idan ya samu mara gata fa?, shikenan ya lalata rayuwar yarinyar da bataji bata gani ba ta sanadiyyar zuwa jami'a an lalata mata rayuwa, dole a taka mishi birki, nida kaina zan kira mahaifinsa akan yaronsa ya fita daga harkar ɗiyata, inba hakaba duk abunda nai masa shiya janyowa kanshi"
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...