page 8

259 24 16
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_Mum Irfaan_*

 
                               *8*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Suna gama parking ɗin kayansu a cikin gidan, Binafa ta kallesu tace "Bari na fita inaso mu siyo funitures ne"
Gyaɗa mata kai kawai sukai saboda suna cikin ruɗani.
Binafa harta kai baƙin ƙofa ta dawo tace "Inno wai wacece matar nan data nuna sani ƙarara akanki, gashi kuma ni bansan ta a ƙauyan Kurfi ba"
Wata zufa ce ta karyowa Inno tace "Idan kin dawo zamuyi maganar"
Ba musu ta kama hanyar fita zuciyarta cunkushe da zullumi.

Basu ɗauki lokuta masu tsawo ba sai gashi sun dawo da motar Funitures masu daidai su, shigar da kayan aka runƙa, set ɗin kujeru ne sai set ɗin gado guda biyu, sai kayan kitchen ɗin da zasu buƙata, saisu bedsheet, duk wani abinda tasan zasu nema saida ta siyo hatta kayan abinci saida ta siyo, tsayawa wajan Safwan tayi tace "Nagode sosai da wannan zirga-zirgan daka tayani"
Murmushi yayi yace "Kinfi haka"
Shiru ne ya biyo baya cikinsu babu wanda ya ƙarayin magana, Binafa ce ta katse musu shirun tace "Inba damuwa bari na shiga ciki ko, inaso zan ɗan watsa ruwane"
  Kallanta yayi yace "Shikenan babu damuwa, ki kulamin da kanki"
Murmushi taimai tace "Kaima haka"
Shiga motarsa yayi ya tayar yayinda ita kuma ta shiga cikin gidan taga an saka komai a mazauninsa, bedroom ɗinta ta nufa dan tanaso ta watsa ruwa.

     Ahmad zaune gaban Kawunsa duk ya fita hayyacinsa kamar ba Alhaji Mansur ba, shiru yayi yana sauraran labarin da yake bashi akan Binafa tun randa suka fara haɗuwa, jin yayi shiru alamun yakai ƙarshen maganarsa yasa Ahmad numfasawa yace "Kawu kace kaima Damfarar tasu kaso kayi Allah bai nufa ba, kawu dan Allah yaushe zaka daina irin wannan harƙallar?, duk randa hukuma ta sani bazasuyi maka da daɗi ba karkai tun ƙaho dani domin hukuma tafi ƙarfin kowa harda ni da kake ganina a matsayin Commissioner of Police" ya ƙarashe faɗa yana kafe Kawun nasa da kallo.
Shiru Alhaji Mansur yayi yace "Baka gane ba Ahmad...."
Ganin Husnah ta shigo hannunta ɗauke da jug yasashi yin shiru, tunda ta shigo idanunta nakan Ahmad ta kasa ɗauke idonta akanshi, sosai soyayyarshi ke ratsa dukkan sashi na jikinta, cikin sanyin murya tace "Ya Ahmad ina kwana?"
Amsa mata yayi fuskarsa babu yabo babu fallasa, harta tashi zata tafi Ahmad yace "Zonan Husnah" cikin rawar jiki sai gashi ta dawo ta zauna kusa dashi, kallan Kawun nasa yayi yace "Wanda Husnah suke tare suna soyayya ya nemeni akan sunaso su nemi auranta, shine nace zan sanar dakai"
  A razane Husnah ta ɗago da fuskarta tana kallanshi amma taga ko kaɗan hankalinshi baya kanta.
Cike da farin ciki Alhaji Mansur yace "Kai Masha Allah, a ina yake haka?"
Gyara zama Ahmad yayi yace "Yana zaune a garin Kano ne, yanzu izininka kawai muke nema"
Murmushin jin daɗi Alhaji Mansur yayi yace "An baku, nasan tunda harta hannunka ya biyo ina mai kyautata zaton nagartaccene shima, Allah yayi maka Albarka yasa ayi damu"
A hankali ya furta da "Ameen" yace ma Husnah "Tashi ki tafi"
Kanta a ƙasa hawaye cike da fuskarta ta tashi ta tana tafiya har takin ƙofar fita ta juyo tana kallan Ahmad kasancewar Alhaji Mansur yabawa Kofar baya, suna haɗa ido dashi hawayan data maƙale suka gangaro kan kuncinta, tare da haɗiye Saliva mai ɗacin gaske, fita tayi hawaye na kwaranya a fuskarta amma bata damu data share ba, a haka harta samu ta shiga Room ɗinta tai rufda ciki hawaye na cigaba da malala, tana tunanin mai yasa Ahmad zai mata?, mai yasa Ahmad zai juya mata baya?, mai yasa Ahmad bashi da tausayi ko kaɗan alhalin yasan tana fama da dakon sonshi tun kafin ta mallaki hankalinta, ta shi tayi ta nuca Bathroom dan ɗauro Alwala.

   Alhaji Aminu ne zaune shida matansa da ƴaƴansa a cikin makeken Parlournsa, kana kallanshi zaka tabbatar dayayi jinya saboda yadda ya ɗan rame kuma ya ɗashe, gyaran murya yayi yace "To Alhamdulillah, Allah ya bani lafiya masu fatan na mutu aci gado to ban mutu ba kwanana na gaba kuma insha Allahu bazan mutu ba sai gabaki ɗayanku kun rugani mutuwa" ya ƙarashe faɗa yana wani zaro idanuwa.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now