*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*30**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_**Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanaso hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1QSosai Familyn Alhaji Modibbo suka shiga tsananin damuwa na rashin ganin Binafa, Alhaji Modibbo dakewa kawai yake a matsayinsa na namiji, Safwan kuwa ya rasa inda zai saka kanshi yaji daɗi sosai yake cikin tsananin damuwa, daƙyar ya samu ya isa Parlourn Alhaji Modibbi ya zauna, shiru yayi can kuma yace "Daddy dan Allah a faɗawa Binafa na janye auranta zanje na auri Husna, nidai burina ta dawo gida kar taje ta saka kanta a halaka"
Murmushin manya Alhaji Modibbo yayi yace "Safwan karka damu kanka a kan haka, domin na gama yanke hukunci sati uku nayi za'a ɗaura maka aure da Binafa koda kuwa bata dawo ba"
Shiru Safwan yayi dan bayaso yayi musu dashi, miƙewa yayi jiki ba ƙwari Alhaji Modibbo yace "Kana da Numbern Ahmad ko?"
Ɗaga kanshi yayi alamun "Eh"
"Bani numbern nasa"
Safwan jim yayi naɗan wani lokaci yace "Daddy dan Allah karkai mishi rashin mutunci, ka ƙyalesa ba laifinsa bane"
Ba tare da Alhaji Modibbo yace komai ba ya ciro wayarsa ya miƙa masa yace "Ungo, kasamin Numbern tasa"
Hannu yasa ya karɓa,ya fara saka mishi Numbern, yana gamawa ya miƙa masa, karɓa yayi yace "Zaka iya tafiya"
Jiki ba ƙwari haka yabar Parlourn yana mai tunanin Allah yasa ayi komai cikin lumana.Fitar Safwan a Parlourn yasa Alhaji Modibbo kiran Ahmad, gaisawa sukai cikin mutunta juna tare da tambayar mutanan gidan, bayan sun gama gaishe-gaishen ne Alhaji yayi gyaran murya yace "Ahmad inaso ka saurareni dakyau ka kuma fahimci abunda zan faɗa maka"
Gaban Ahmad ne yayi mummunan faɗuwa yace "Inajinka Daddy"
Daddy yace "Kana da labarin an tsaida auran Binafa da Safwan?"
Cikin tashin hankali da ruɗu yace "Ban sani ba Daddy"
Numfasawa yayi yace "To bikin Safwan da Binafa saura satika, dan Allah Ahmad ina kai shawartarka daka rabu da Binafa kai nesa da ita, domin mun daɗe muna jiran wannan lokacin nida Ƙanina, Ahmad kayi haƙuri ka nemi wata insha Allahu, Allah zai masanya maka da mafi alkhairi wacca kuma tafi Binafa"
Cikin rawar murya Ahmad yace "Shikenan Daddy, Allah ya tabbatar da alkhairi yasa hakan shine mafi alkhairi a garemu baki ɗaya, nagode"
Katse kiran yayi jikinsa yahauyin rawa, Contact ya shiga yana neman Numbern Binafa yana gani yahau gogewa hannunsa na faman yin rawa, Text ɗin fatan Alkhairi da taya murna Ahmad yayiwa Safwan yana ganin Message ɗin ya shiga ya kashe wayar tashi gabaki ɗaya, ya rasa meke mishi daɗi a duniyar, ƙanƙame jikinsa yahauyi jin wani irin sanyi da yakeji, daƙyar ya samu zummar ɗauko Blanket ya rufa ya kwanta yana lumshe ido gabanshi na daɗa tsananta faɗuwa, wayarsa ya lalubo ya ƙara kunnawa, Numbern Uncle Lukman ya kira, ringing ɗaya aka ɗauka, cike da girmamawa Ahmad ya gaishe da Lukman, shiru ne ya biyo ba, yayinda cikin sigar zolaya Uncle ɗin ke cewa "Ango ansha ƙamshi, wannan kiran fa?"
Murmushi kawai Ahmad yayi masa, yace "Uncle dan Allah inaso ka saurareni kuma inaso ka fahimceni, banaso kaimin wani kallo na daban, maganar auran Binafa da nace zanyi na fasa saboda wani ƙwaƙwƙwaran dalili da nake dashi, mahaifina ya barmin Nasiha akan yanaso na auri ƴar ƙanwarsa, sai yanzu ake shaidamin, dan Allah kayi haƙuri nasan ban kyauta maka ba, ina mai matuƙar baka haƙuri Uncle nagode ƙwarai da karamcinka a gareni, sao anjima" cikin sauri ya katse kiran dan bayaso yaji wani abu game da Binafar kuma, sosai zazzaɓi ya fara yin galaba akanshi, lumshe ido kawai yayi hankalinsa a matuƙar tashe.
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
خيال (فانتازيا)Binafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...