*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*21**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_**_Ina matayan da sukeso su cancaɗa kansu wajan kwalliya ga atamfofi dasu laces, domin burge mai gida?, ƴar uwa maza garzayo kamfanin Mrs Maidala's Collections domin samun kayanmu mai sauƙi akan farashi mai rahusa, matso kusa ga dama ta samu wajan siyan takalman yara, takalman uwargida na kece raini, atamfofi, laces, jakunkuna, kayan kitchen da sauransu, siyan ɗaya ko sari muna aikawa ko ina dake faɗin duniyar nan bama a Nigeria kaɗai ba, domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓemu ta wannan Numbern kamar haka 08162943828_*
*Domin samun shiga group ɗinmu wanda zaku runƙa ganin abubuwan da muke posting maza shigo cikin wannan Link ɗin, please bama bukatar namiji duk namijin daya shigo Allah ya isar mana*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gvu1O311g6pGZXFmwYiTuJBinafa kallan Ahmad tayi sannan ta kalli Safwan tace "Ya Safwan"
Sai kuma tayi shiru tana wasa da hannunta kanta a ƙasa.
Safwan kallan Ahmad yayi ta gefen ido yace ma Binafa "Muje waje"
Cikin sauri ta tashi tabi bayansa ko kaɗan batai gigin kallan Ahmad ba.
Gabaki ɗaya ran Safwan a jagule yake, kallan Binafa yayi yace "Binafa menene bana miki dahar wani yayi miki irinsa yakeson tafiya da zuciyarki?, shin kin daina sonane?, koko bana baki kulawar da kike buƙatane?, dan Allah ki faɗamin nai miki alƙawarin zan gyara Binafa"
Kallanshi tayi shima ita yake kallo da Sexy Eyes ɗinsa, zoben hannunta ta murza tace "Ko kaɗan Ya Safwan baka gazamin a komai ba, kanamin abunda duk wata ƴa mace zataso ace ana mata, nidai kawai ya faɗa maka hakane danya shiga tsakanina dakai"
Idanun Safwan a idon Binafa yanaso ya gane gaskiyar lamarin, cikin sanyin murya yace "Binafa wanene wannan?"
Runtse idanunta tayi dan bazata iya cigaba da kallanshi ba, cikin in ina tace "Naa...fa...ɗa...maka....kawai..so....yake...ya haɗamu faɗa"
Murmushin gefen baki Safwan yayi yace "Binafa ki faɗamin wanene wannan da yakeso ya ƙwacemin abu mafi muhimmanci a rayuwata, Binafa wani sake nayi har haka naga kina ƙoƙarin yin fatali da tawa soyayyar?, ni menene aibuna?"
Girgiza kanta tayi tace "Ya Safwan ba haka bane, dan Allah ka daina tunanin wani abu daban..."
Katseta yayi da hannunsa zuciyarsa na tafarfasa yace "Kije kiyi tunani, ki tsaya da zuciyarki waje ɗaya, nai miki alƙawarin fahimtarki Binafa, domin cigabanki shine cigabana a rayuwa"
Juyawa yayi zai tafi tai saurin ruƙo hannunsa tace "Ya Safwan.."
Yatsunsa ya saka mata akan laɓɓansa tare da sakin mata murmushi mai tsadan gaske yace "Kiyi abinda na sakaki, banaso na tauye miki hakki a rayuwarki, zan iya sadaukar da komai na rayuwata domin in ganki cikin walwala, amma inaso ki sani ina ƙaunarki, tun kan nasan menene so kike cikin zuciyata, Binafa inada kishi, bansan inada kishi har haka ba saida aka dangantaki da ɗa namiji, naji babu daɗi naji zuciyata tamkar zata faɗo na taketa na huta, zanso ace nine zan zama mallakinki Binafa, da a lokacin zaki gane irin ɗunbin ƙaunar da nake miki a rayuwata"
Kasancewar sun kusan mannewa da juna yasa ko wannansu yanajin bugun zuciyar waninsu, lumshe ido Binafa tayi saiga wasu siraran hawaye sun zubo mata, a hankali ta furta "Nima ina Son...."
Jin gyaran murya yasasu saurin matsawa daga junansu.
Ahmad ne hannunsa rungume a ƙirjinsa yana kallan Safwan yana murmushi yace "Baban soyayya an manta dani anzo anashan soyayya ko"
Sosa ƙeya Safwan ya farayi yace "Abokina bazaka gane bane, kainane ya ɗauki caji" kallanshi yayi yace "Muje ko"
Murmushi Ahmad yayi yace "Kaje Mommy na kiranka kai sauri ka dawo yau nakeso zan wuce"
Gyaɗa kai kawai Safwan yayi yace "Bari in dawo"
Binafa ganin haka tai sauri zatabi bayan Safwan, Ahmad kallanta yayi yaga hankalinta baya wajansa ma kwata-kwata, danne kishin dake matuƙar damunsa yayi yace "Amaryarmu ina zuwa haka, baza a haƙura ya dawo daga wajan Mommyn ma"
Juyowa Safwan yayi yaga zata bishi, tsayawa yayi yana jifanta da wani irin shu'umim murmushi yace "Bari in dawo ba daɗewa zanyi ba"
Gyaɗa kanta tayi tana wasa da Veil ɗinta, dan tasan gamonta da Ahmad bazai mata da daɗi ba, dan ta lura mugun kishine da shi.
Tsayawa tayi nesa, Ahmad ganin Safwan ya tafi yasashi takowa har inda Binafa take fuskarsa babu fara'a ko kaɗan, Binafa ganin yana matsowa kusa da ita yasa gabanta faɗuwa tare da runtse idanunta tana fitar da wani irin huci mai zafin gaske saboda fargaba.
Ahmad saida ya ƙare mata kallo dakyau yace "Binafa mai nai mike ne har haka da baki sona?, mai yasa baki da tausayine?, mai yasa kanki kawai kika sani a rayuwarki?, ki faɗamin" ya ƙarashe faɗa yana janyo numfashinshi daƙyar saboda jin barazanar ɗaukewar da zayyi.
Binafa itadai idanunta a rufe tanajin duk abunda yake cewa.
Jingina yayi da bango ya zauna a ƙasa dirsham yana maida numfashi, cikin sanyin murya yace "Da da yadda zanyi na cire soyayyarki a cikin zuciyata wallahi danayi kodan Safwan da muke tare dashi, na rasa yadda zanyi Binafa"
Shiru yayi ya saka kansa tsakiyan cinyoyinsa, yana tunani barkatai a zuciyarsa.
Jin an dafashi yasashi ɗago da kanshi a hankali, ganin Safwan yasashi lumshe ido, Safwan kallan inda yabar Binafa yayi yace "Ina Binafar?"
Ahmad shiru yayi dan baimasan bata wajan ba, sauke ajiyar zuciya yayi yace "Ta shiga ciki"
Safwan kallan inda ya zauna yayi yace "Ya naga ka zauna dirsham a ƙasa?"
Murmushi Ahmad yayi yace "Naji daɗin zaman ne" tashi yayi ya fara kakkaɓe jikinsa yace "Ni zan wuce, dan banaso ina tuƙin dare"
Safwan shima miƙewa yayi yace "Muje na rakaka Parking Space, ba musu ya tashi duk da jikinsa babu daɗi, yana tunanin tun yaushe Binafa tabar wajan baisani ba, shiru yayi har suka isa wajan motarshi, sallama yayi mishi ya shiga motarsa ya tayar zuciyarsa sam babu daɗi.Binafa tana jikin window ɗin ɗakinta tana kallan duk abunda ya faru, jingina tayi tare da dafe ƙirjinta tana jin babu daɗi, ta rasa a cikin Safwan da Ahmad wanene takema son gaskiya, tabbas tanajin Safwan a ranta haka zalika Ahmad shima tanajin shi a zuciyarta, wa zata samu ya warware mata zare da abawa tsakanin Ahmad da Safwan?, shine amsar datake buƙata daga gareta.
Wayarta ta ɗauko ta tsurawa numbern Ahmad ido tanaso ta kirashi amma kuma tana tsoron maizai biyo baya, daurewa tayi ta danna kira gabanta na cigaba da faɗuwa, ringing take tayi amma ba'a ɗauka ba harta katse, ajiye wayar tayi jiki a sanyaye.
Tana ajiyewa saiga kira ya shigo cikin wayar tata, tana dubawa taga Ahmad ne, cike da fargaba ta ɗauka tace "Ka tafi ne?"
Iska ya furzar yace "Na tafi, saboda naga kamar ina takura miki kuma bakya buƙatata, wallahi Binafa ɗazu da kin furtawa Safwan kalmar so ina tunanin da a take a wajan zuciyata zata buga, dan Allah ki sassautamin haka, abun yayimin tsauri"
Cikin sanyin jiki tace "Ba dagani bane Ahmad wallahi zuciyatace taƙi tsaidani waje ɗaya, ɗazu kuma taka ganmu haka ran Ya Safwan ya tashi wallahi ya shiga cikin damuwa daka faɗa mishi haka, ban taɓa ganinshi a irin wannan yanayin ba, dan Allah koda wasa karka ƙara faɗa mishi kwatankwacin wannan kalmar"
Murmushin takaici Ahmad yayi yace "Yanzu driving nake idan na sauka gida in dare bayyi ba zan kiraki and ki kulamin da kanki"
Katse kiran yayi yanajin ɗaci cikin ransa.
Binafa ɗagowar da zatayi taga Safwan akanta ya kafeta da idanunsa ta suka sauya kala.
A firgice Binafa ta yarda wayar jikinta ya fara tsuma, tanaso tai ƙoƙarin saita kanta amma ina ta kasa saboda yadda ya kafeta da rinannun idanunsa.
A hankali ya taka har inda ta yar da wayar ya ɗauka, cikin zafin kishi da tsananin ƙaunarta yace "Dan Allah ki faɗamin dawa kike waya?"*Kuyi maneji yau ina busy*
*More comments more typings*
*#Comments*
*#Shares*
*#Votes*
*#Likes**#Team Binafa and Ahmad*
*#Team Binafa and Safwan*
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...