page 3

291 22 2
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*©HIKIMA WRITERS ASSOCIATION*

'''(home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers)'''

*~Na Mallakin~*
              *Mum Irfaan*
     A.k.a   *_Er-gafaii_*

*Follow me on Wattpad-Mumirfaan*

My Gmail Account
Www.mumirfaan77@gmail.com

                             *3*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

Binafa Kama handle d'in motar tayi Amma ta kasa fitowa, sai yak'e takeyi, ganin Wannan matashin ya nufa motarsa yasata sakin wata sassanyar ajiyar zuciya, yayinda ko minti biyar bayyi a wajan ba ya Shiga motarsa yabar wajan, Alhaji Mansur ne yace "KU fito Daddy"
Ba musu suka fito yayinda Binafa Tai mishi yak'e tace "Kajini shiru ban fito bako, Wallahi chat na tsayayi da k'awata wacca nabarwa amanar restaurant d'ina a London shiyasa".
Washe Baki Alhaji Mansur yayi yace "Masha Allah, kice kema kina da restaurant Mai zaman kanshi acan Kenan"
Baffa ne ya cafke yace "Ai shine k'aramin restaurant d'inta ma"
K'ara washe Baki yayi yace "Madallah, ya Sunan restaurants d'in naki?"
  Gabaki d'ayansu had'a Ido sukai saboda basusan wata irin k'arya zasu k'ara yimai ba gashi su Basu wani san London d'in sosai ba bare suyi k'aryar wani restaurant, dabarace ta fad'owa Binafa Tace "Ranka ya dad'e aika Bari su Mom d'ina su Shiga ciki su zauna ko"
Cike dajin kunya yace "Am sorry my Queen, Dad, Mom muje ko"
Ba musu suka bishi a baya yayinda Inno take da guntse dariyar ta ganin Yadda Alhaji Mansur ke respecting d'inta alhalin ya girmemata nesa ba kusa ba.
Babu laifi gidan Yana dakyau daidai gwargwado, flat ne 3 bedrooms, komai akwaishi a gidan, tsarin gidan yayi kyau matuk'a, kayansu suka loda a cikin wardrobe kowa ya d'auki nashi d'akin, kafin wani lokacin k'ank'ani sai gashi an kawo musu uban kayan abinci, a store aka zuba, sai kayan drinks him guda, shima an zuba a fridge d'in kitchen da Kuma na parlourn harda extras aka zuba a store, sosai Binafa ta Gama believe sun samu gara zasu wanke.
Shi kuwa Alhaji Mansur Diary ya samu na musamman ya buga lisaafin kayan abinci dasu drinks ya kashe kud'i a k'alla zakai dubu d'ari da hamsin, murmushi yayi ya saka plus dubu d'ari uku, ma'ana ya ninka kud'in abincin yadda idan ya tashi kar6ar kud'in zai amsa d'ari da hamsin d'insa na abinci sa sai Kuma zallar ribarsa ta dubu d'ari uku, murmushi yayi yace "Komai nai muku a list Zan saka saboda yadda Zan kar6i kud'ina da kauri" dariya ya k'yalk'yale dashi yace "Na samu garori" kwanciyar shi yayi hankali kwance.

Su Baffa an samu na banza Haka suka baje suna kwasar garar da Alhaji Mansur ya kawo musu, yayinda Binafa ta saka k'afa d'aya kan d'aya tana faman canza tashoshi sai kace Wanda suka shekara a cikin gidan.
Kamar an mintsineta ta tashi ta d'auko wani k'aramin veil ta saka ta fice, kallan anguwar tayi taga yadda tsarin yayi kyau matuk'a, murmushi tayi ta tsaya a bakin Titin anguwar tana kallon yanayin garin, ganin wasu 'yan Mata sun fito daga mota suna shewa yasata tsayawa kallansu, a k'alla zasukai shekara Ashirin da biyar , matane wayayyo na gani na fad'a, saidai Basu da kyan azo a gani Amma akwai gayu, sosai suka birge Binafa duk da sun girmemata nesa ba kusa ba, murmushi tayi ta hard'e hannayanta tana kallansu, wayar ta ta Ciro daga purse ta ruk'e a hannunta yayinda ta gyara warwaron zinaran hannunta dansu gansu dakyau, tana ganin sun juyo inda take Tai saurin saka wayar a kunnanta, fad'i take "Shikenan, maybe next week na shigo Dubai d'in, saboda akwai kayan da nakeso Zan siya a Nan d'in, noo Karki damu ki bar shi Wallahi Kya siyawa Yarana sweet, oh Niko maye 1million Danna Baki k'awata ai kinfi Haka"

Duk hirar da Binafa tayi wa 'yannan Classic Ladies d'innan suna jinta, ganin shigarta da Kuma wayar dake hannunta suka tabbatar da maganarta Gaskiya ce ba K'arya a ciki, Aziza ce ta kalli Hamida yayinda itama Hamidan kallanta take, Aziza Tace "Dad d'ina Yana ruk'e minister of Education ace banyin Wannan wadak'ar da dukiya sai waccar Babyn, shinma wacece ita a wannan Area d'in?"

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now