*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*25**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_**Ahayye mata masu aji, mata masu ji da kansu, macen data yarda da kanta, shin kinsan akwai ingantattun maganin mata, sannan akwai sahihin maganin sanyi, tayaya zaki zauna babu gyara kina ƙyashin siyan kayan da zasu gyaraki amma kinsan ki tattala kuɗi kiyi adashi, anya wannan ajine kuwa?, ga dama ta samu dan siyan ingantaccen maganin mata dana sanyi, dan Allah idan kinsan baki shirya ba karkimin magana, karkizo kicemin ke ƴan 5h kikeso, kayana ba ƴan tagajan-tagajan bane, domin na yadda dasu wanda sukai amfani dashi suma sun yadda dasu, uwargida, amarya ki garzayo kizo ki nemi ingantaccan magani domin samun kima da daraja wajan mai gida, kina da yarinyar da zaki aurar amma kin rasa wani magani zaki bata?,to maza garzayo a haɗa miki ƴarki cikin sauƙi da rahusa, kin haihu kinaso ki gyada kanki amma kin rasa wani magunguna ya dace kisha?, hmm manyan mata kenan maza kizo a haɗaki miji ya kasa gane shin kin taɓa haihuwa ma kuwa*
Domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannan numbern 08130515037Jingina tayi da motar Ahmad murmushi shinfiɗe a fuskarta tace "Gaskiya Ya Ahmad ka shammaceni, ba saika faɗamin zakazo yau ba"
Murmushi yayi yace "Nasan idan na faɗa miki baza kiyi murnar ganina ba yadda kikeso"
Murmushi tayi tace "Kuma hakane, Allah kaɗai yasan irin farin cikin danake ciki yau"
Kallanta yayi naɗan sakwanni kaɗan yace "Naga kamar bakya cikin natsuwa Hope dai kina lafiya?"
Lumshe ido tayi tace "Ƙalau nake Ya Ahmad kawai dai yanzu makarantar ce ta fitanmin arai"
Zaro idanu waje yayi yace "Bakyaso fa kikace?"
Ɗaga mishi kanta tayi fuskarta cikin damuwa, ta buɗe baki zatayi magana kenan ta hango Mahbub yana tahowa, tafiya yake cikin ƙasaita da taƙama.
Ahmad kallan inda Binafa take kalla yayi ya hango Mahbub yana tahowa, da mamaki ya kalleshi yace "Mahbub Madaki"
A zabure Binafa ta ɗago da fuskarta tana kallan Ahmad tace "Kasanshi ne?"
Cike da al'ajabi da tashin hankali yace "Nasan Mahbub farin sani, kema kin sanshi ne?"
Ya tambayeta tare da kafe ta da idanunsa.
Ɗaga kanta tayi tace "Kamar shima lecturer ne a wannan makarantar"
Shiru Ahmad yayi hankalinshi a matuƙar tashe, tayaya Mahbub zaizo University yana koyarwa, abun ba ƙaramin mamaki ya bashi ba.
Binafa kallan Ahmad tayi tace "Shikenan yau bazan shiga lecture ba" ta faɗa kamar zatai mai kuka, ganin Mahbub ya shiga class ɗinsu.
Hankalinshi ya maido gareta yace "Look Binafa, ki natsu mai zai hana kiƙi shiga Lecture?"
Hawayan data maƙalesu ne suka zubo mata tace "Ya Ahmad, wancan Malamin da kace ka sanshi ya tabbatar min inya rigani shiga Class to ni bazan shiga harna tsawon sato ɗaya"
Harɗe hannayansa yayi yana kallanta yace "Yaushe kukai haka?"
Murya na rawa tace "A Office ɗinsa"
Runtse ido Ahmad yayi, tare da jinginar da kanshi a jikin mota yace "Binafa dan Allah ina nemab alfarmarki, duk rintsi duk wuya kiyi ƙoƙarin kama kanki, ki killace kanki, dan Allah ki ruƙe mutuncin kanki"
Yana gama faɗan haka ya shiga motarsa yace "Zan shigo gidansu zuwa da daddare yanzu zanje masaukinane"
Da kallo kawai Binafa tabi Ahmad dashi, saida taga ficewarsa sannan tayi ajiyar zuciya, tare da kallan Class ɗinsu, cikin sanyin jiki da ƙarasa Hall ɗin, ba tare data kalla inda lecturer ɗin yake ba ta fara tafiya tana neman mazauni, duk da student ɗin basu da yawa ba'a saboda ba'a gama hallara ba.
Jawabi yake musu cikin ƙwarewa ta harshen turanci, ganin ta shigo yasashi yin shiru yana kallan Step ɗinfa, har saida takai ga zama, cikin gadara yace "Stand Up"
Tashi tayi daga zaunan da take ta tsaya, wayarsa ya ciro ƙirar iPhone tare da Earpiece ɗinsa ya kira wata student, miƙa mata yayi tare da umartarta data sakawa Binafa a kunne.
Tunda ta sakawa Binafa a kunne Binafa ta runtse ido tana ƙoƙarib cirewa saboda sautin kiɗan dake tashi yayiwa kunnanta yawa.
Kallan daya jefeta dashine yasata tsayawa har saida wannan budurwar ta saka mata, Binafa saurin gyara gyalenta tayi ganin yadda ya ƙurawa Boobs ɗinta ido.
Mahbub ganin taja gyale ta gyara yasashi taɓe bakinsa ya cigaba dayi musu jawabi cikin ƙwarewa.
A ƙalla yakai awa biyu yana musu jawabi, yayinda Binafa ta gaji da tsayuwa ga ƙafarta harta fara ƙaiƙayi saboda tsayuwar datake gashi bata sababa, gashi yayi mata warning akan jingina da bango, ko kaɗan batajin abunda yake faɗa, ganin wani student ya ɗauko masa wasu takaddu sunyi hanyar fita yasata sakin ajiyar zuciya dukda har yanzu wayar shi na hannunsa, tana ganin ficewarsu ta samu guri ta zauna tare dajan dogon tsaki tana sosa ƙafarta saboda ƙaiƙayin da take mata, tana duba screen ɗin wayar ta ganshi fes akan wayar yayi kyau matuƙa, saidai mahassada, taɓe baki tayi tace "Ahmad ɗina yafi wannan komai na rayuwa, Ahmad fa daban yake jikin maza, komai nashi classic ne"
Ta ƙarashe faɗa tana lumshe ido, jin hannun mutum cikin nata yasata buɗe idonta cikin sauri Malam Mahbub ne ya dawo ya karɓa wayarsa.
Tsuru tayi dan tasan tabbas ta tafka taɓozara, miƙa mai wayar tayi, ta kauda kanta ganin wani irin fitinannan kalli dayake watsa mata.
Cikin muryarsa mai Daɗin sauraro yace "Ki sameni a Office" bao jira amsarta ba yayi gaba abunshi.
Kallo tabishi dashi tana tunanin uwar mai zatai mai a Office ɗin nasa,
Miƙewa tayi ganin zata ɓatawa kanta lokaci ta mara mishi baya.
Tafiya take cikin natsuwa , ganin wasu dandazon ƴan mata masu ajin gaske yasata ƙara saita tafiyarta, muryar wata matashiya taji maiji da aji ta bi bayan Malam Mahbub da harara sannan ta juyo zuwa ga ƙawayanta tace "Bebs wannan malamin ɗan rainin wayo ne, kingashi wani shegen miskili gashi iskancinsa yafi ƙarfinsa, nifa abu ɗaya yake haɗani dashi da zaran ya ɗanɗana mace so ɗaya shikenan zai tattara ya watsar dake, gashi abun takaici yafison Virgin, ni bansan tayaya yake gane Virgin ba wallahi, nidai ya cuceni wallahi" ta ƙarashe faɗa kamar zatai kuka, watace ta dafata tace "Shiyasa tun farko na gargaɗeki da faɗawa soyayyarshi amma kinƙi ji"
Jan numfashi tayi tace "Bazaki gane ba, wallahi guy ɗin ya haɗu ta yadda bakya tsammani, komai nashi a tsari yakeyinsa, gashi jinin sarauta"
Taɓe baki wata tayi tace "Nifa kyanshi bai taɓa ruɗata ba wallahi, ɗazu naga namiji iya namiji ya fita daga makarantar nan banajin a School ɗinnan yake maybe ziyara ya kawo, but wallahi naso ku ganshi wane Malam Mahbub..."
Ganin tayi nesa dasu yasata daina jin abunda suke cewa game da Malam Mahbub ɗin, tuni jikin Binafa ya ɗauki rawa, tunani ma take anya zata shiga cikin Office ɗin, jiki ba ƙwari ta tura Office ɗin ta shiga.
Yana zaune akan kujerarsa dagashi sai singlet sai dogon wandan daya cire.
Binafa tunda ta ganshi tai saurin sadda kanta ƙasa ganinshi a haka.
Fuskarsa ba fara'a yace "Zauna"
Kamar jira take ta zauna, tashi yayi yazo har inda take ya dafa kujerar datake zaune, ƙamshin turaransa ne ya daki hancin Binafa nan take ta lumshe ido tana shaƙar turaran, ƙare mata kallo yayi dakyau, yaga tabbas ta haɗu kota ina, wannan itace irin matar dayake da muradin aura, saidai a yanzu babu tsarin aure a rayuwarsa tunda duk abunda ya nema a duniyarnan yana samu, kallan Boobs ɗinta yayi wanda tun ɗazu ya daɗe yana kallansu, Binafa tana buɗe ido taga Mahbub ya kafema na shanunta ido tai saurin jan gyalenta zata rufe, sauri ruƙe hannunta yayi wanda take ƙoƙarin rufe ƙirjinta, ɗayan hannunsa yasa a saman Boobs ɗinta nan take Binafa tayi wata irin zabura jikinta ya fara rawa.
Cikin muryarsa ta Izza yace "Karki sake ki fita" ba tare data sauraresa ba ta fara yunƙurin fita ganin tabbas idan ta tsaya a wajannan rayuwarta gab take da lalacewa, taku uku yayi sai gashi a gabanshi, kallanshi tayi tana mamakinsa domin a fuska ko kaɗan bazaka kawo wani abu game dashi ba domin kuwa fuskarsa kamilalla ce.
Janyota yayi jikinsa ya rungumeta tsaf yana fitar da wani irin numfashu, cikin ƙarfin nama Binafa ta tureshi ta koma tamkar wata mahaukaciya faɗi take "Stop it" ɗauko gyalenta tayi daga ƙasa, tare da ɗauko handbag ɗinta, ganin ya taho inda take yasata wanka mishi mari, tare da jan tsaki tace bunsuru kawai.
Ganin wayarta na haske ya tabbatar mata da kiranta akeyi tana dubawa taga Ahmad ne, jikinta rawa ya farayi, taƙi ɗaukar wayar ta doshi ƙofar fita waje.
Mahbub kuwa tunda ta mareshi ya ɗauke wuta cike da tsantsan ɓacin rai ya mara mata baya dan saiya rama, tana fitowa kasancewar akwai Balcony a wajan yasata tsayawa saita kanta.
Shima buɗe ƙofar yayi a fusace sai sukaci karo da ita, ya ɗaga hannu zai wanka mata mari kenan ya hango Ahmad, dukda bai wani ganeshi ba sosai amma ganin mutum a wajan yayi azamar rungume Binafa, tare da saka harshensa cikin kunnanta ya fara yi mata wani irin wasa mai wuyar fassaruwa.
Jikin Binafa rawa kawai ya farayi saboda wani irin yanayi data tsinta kanta, sosai take yunƙurin turesa amma ina ta kasa ya sakar mata nauyinsa.
Juya idon da zatai ta hango Ahmad rungume da hannayansa idonsa ya canza launi, batasan lokacin da ƙarfi yazo mata ba ta turesa da ƙarfi tana zubda hawaye.
Kanta a ƙasa ta kasa haɗa ido da Ahmda dan batasam mai zatace masa ba.
Jikin ba ƙaramin rawa yake ba, a hankali ta taka har inda Ahmad yake, cike da tsoro da fargaba tace "Yah Ahmad....."
Ɗaga hannunsa yayi alamun ta dakata, bai jira cewarta ba ya tada motarsa a fuuu yabar makarantar hankalinshi a matuƙar tashe, ko kaɗan baya ganin gabansa daƙyar Allah yasa ya kaisa inda zashi.
Binafa tsayawa tayi cikin tashin hankali ta rasa yaya zatai, tunani take dama haka jami'ar take, nan take taji ta tsani makaranta ko kaɗan bata ƙaunarta.
Jin kamar mutum a bayanta tai mugun razana, ganin Safwan ne yasata sauke wani irin ajiyan zuciya, kallan tuhuma yayi mata yace "ƙalau kike kuwa?"
Shiru tayi ba tare datace dashi uffan ba.*More comments more typings*
Kuyi maneji yau banda caji😩
*#Team Binafa and Ahmad*
*#Team Binafa anad Safwan**#Comments*
*#Shares*
*#Likes*
*#Votes*_ƴar gafai_
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...