Page 35

179 22 6
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *35*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*Kai masha Allah, yanzu babu ruwana da zuwa kasuwa cikin cunkoso, Lanika shin kinsan shararriyar nan mai saida kayyakin abubuwan more rayuwa?, to ƴar uwa kamfanin Maman Fatiman Collection ya kawo mana abubuwa da dama kamarsu Bedsheet, Furnitures, Kitchen Wire, Carfet, Night Gown, Laces, Materials, Shadda, Atamfofi, Baby set da sauransu, maza ki samu Maman Fatima Collection domin samun kaya cikin sauƙi da rahusa, Lanika kallan Binafa tayi tace "Tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, domin ga dukkan alamu kayanta suna da matuƙar kyau d inganci, Binafa ai naga ba a ko ina kike siyayya ba", Binafa murmushi tayi ta jujjuya mata bayanta tace "Kinga tun daga kan takalmin ƙafata har zuwa kan Veil a wajanta na siya, nifa bazan iya siyayya agun kowa ba inba agun Maman Fatima Collection ba", lanika cike da zaƙuwa tace "Dan Allah tayaya zan samu wannan Maman Fatima Collection ɗin?, yatsina fuska Binafa tayi ta ciro wayarta tace "Ga numbernta badan halinki ba 08178627493", lumshe ido Lanika tayi tace "Ina matuƙar godiya ƴar uwata, amma dan Allah nasan irin wa ƴannan ƴan kasuwan basu rasa Group ɗin da suke posting, yaya za'ai na shiga Group ɗinta dan ganin ingantattun kayanta?", binafa tace "karki damu yanzu kuwa zan turo miki da link din" godiya Lanika tayi tace "Yanzu zan kira Ya Mahmud domin sanar dashi kamfanin Maman Fatima Collection don ya haɗomin akwatin aurena acan", dariya Binafa tayi tace "Wallahi baki da kunya ko kaɗan"*
*Domin samun damar shiga Link ɗin Maman fatima Collection antayo cikin nan amma dan Allah banda maza, idan kanason hada akwatinka ne to ka turo Auntynka ko matar da zaka aura don ta shiga*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/8FW9h373nOWE3ZYHyiZL1Q

*ALLAH YA SAUKI MAMAN FATIMA COLLECTION LAFIYA SAIDAI YARON BAIZO DA RAI BA, ALLAH YA YASA MASU CETONMU NE, ITA KUMA MAHAIFIYARSA ALLAH YA BATA HAƘURI DA JURIYA NA RASHINSA, ALLAH KUMA YA ƘARA MATA LAFIYA*


Ahmad kallan Binafa yayi yanaso yaga yanayinta, ganin kanta a duƙe ya fara in-ina yace "Kawu Please muje waje muyi magana"
Alhaji Mansur tsayawa yayi yace "Ba inda zani, so nake naji ka furta mata kalmar saki domin wannan da kake ganin tantiriyar mayaudariyace"
Kwaɓe fuska yayi ya ruƙo hannun Binafa yace "Zo muje"
Ba musu tabi bayanshi gabaki ɗaya hankalinta ba'a kwance yake ba.
Alhaji Mansur harɗe hannayansa yayi yana kallan ikon Allah ganin Ahmad baibi ta kanshi ba, Ahmad ɗin da yake matuƙar jin maganarsa tamkar shine ya haifesa, ƙwafa yayi ya baza babbar rigarsa yabar Parlourn.
Matarshi ce tabiyo bayansa tana faɗin "Alhaji bafa a yiwa yaran zamani irin haka, ko kai ka haifesa dole kai haƙuri dashi, dan ka samu yana maka biyayya shine zaka aibata masa mata a gabanshi kuma agabanta, shin maitai maka har haka kake faɗa mata wa ƴannan mugayan kalaman?"
Alhaji Mansur numfashi yaja yace "Itace yarinyar da nace zan aura ta damfareni, tayaya zan zuba ido ina gani ta cutar da Ahmad, kisan irin wa ƴannan bazasu taɓa daina halinsu ba, saidai suyi kwantan ɓauna"
Cike da Mamaki Maman Husnah tace "Amma kwanaki da bakinka kake faɗamin cewar kunje Kotu akan case ɗinta nan aka warware muku zare da abawa na cewar duk abinda take ba'a hayyacinta take yinsa ba"
Shiru Alhaji Mansur yayi sannan yace "Nifa naji sune kawai amma ko kaɗan ban yadda ba, maza ki kirasu Husnah a waya kice suzo mu tafi yau Ahmad ya nunamin iyakata"
Girgiza kai Maman Husnah tayi tace "Karkace masa haka, yaka mata kai mada uzuri"
Baza malun-malun ɗinsa yayi ranshi babu daɗi.
Yayinda Maman Husnah ta ɗauki wayarta ta kirasu Husnah akan su fito suzo su wuce.
Basu ɗauki lokaci mai tsayi ba sai gashi sun fito nan Alhaji Mansur ya tada motarsa suka bar gidan.

Binafa tana zaune gefen Gado yayinda Ahmad ya janyo Stool ya zauna kusa da ita yama rasa me zai faɗa mata, ƙara gyara zamansa yayi yace "Dan Allah..."
Hannunta ta ɗaga alamun ya dakata, ba musu yayi shiru yana kallanta da fararan idanunsa.
Hawayene suka sauka akan kuncinta tace "Dama kana da wata alaƙa da Alhaji Mansur shine baka faɗamin ba?, ashe shine Mahaifin Husnah baka taɓa furtaminin ba?, mai yasa zai jefeni da wa ƴannan kalaman masu matuƙar nuni a gareni"
Hannu ta saka ta goge hawayanta tace "Tabbas abunda Alhaji Mansur yayimin banji daɗinsa ba ko kaɗan"
Matsawa tayi ta janyo blanket ta juyawa Ahmad baya ba tare data kalla inda yake ba.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now