Page 20

198 21 9
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *20*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*_Ina matayan da sukeso su cancaɗa kansu wajan kwalliya ga atamfofi dasu laces, domin burge mai gida?, ƴar uwa maza garzayo kamfanin Mrs Maidala's Collections domin samun kayanmu mai sauƙi akan farashi mai rahusa, matso kusa ga dama ta samu wajan siyan takalman yara, takalman uwargida na kece raini, atamfofi, laces, jakunkuna, kayan kitchen da sauransu, siyan ɗaya ko sari muna aikawa ko ina dake faɗin duniyar nan bama a Nigeria kaɗai ba, domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓemu ta wannan Numbern kamar haka 08162943828_*
*Domin samun shiga group ɗinmu wanda zaku runƙa ganin abubuwan da muke posting maza shigo cikin wannan Link ɗin*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gvu1O311g6pGZXFmwYiTuJ

*RANAR LITININ*

A yaune ake zaman kotu da Baffah dasu Binafa, yayinda Kotu ta cika maƙil da jama'a abun fa ba'a magana, a ciki kuwa akwai su Alhaji Aminu, Alhaji Mansur, Prof Sunusi da wasu mutane da dama.
Baffah yana tsaye shida Inno yayinda jami'an tsaro suka tsaresu, duk wasu hujjoji da shedu an kammalasu, hatta malamin da yakewa su Baffah aiki saida aka cafko shi domin shima bada shaidar, kotu tayi tsit babu abunda kakeji sai ƙarar fanka da A.C.
Alƙali ne ya buƙaci ganin Binafa akan ta fito anaso ayi mata wasu tambayoyi.
Binafa wuri-wuri tayi da idanu tana kallan Safwan ta kasa koda motsi tsoro fal cikin ranta.
Tashi yayi yazo wajanta cikin murya ƙasa-ƙasa yace "Taso mu tafi, ki kwantar da hankalinki, duk abunda kika sani game da Baffah da Inno ki faɗa karki ɓoye komai, har aure-auren da kikai ki faɗama alƙali domin bayason ƙarya, sannan da zaran kinyi zai gane hakan"
Gyaɗa mishi kai tayi yayinda ruwan hawaye suka ciko mata daga idanunta, alamu yayi mata da kartai kuka, kallan Hajiya Hauwa tayi itama tai mata alama datashi ta tafi, sannan ta kalli Alhaji Modibbo shima murmushin yayi mata, tuni taji wani ƙwarin gwiwa yazo mata ta tashi ta tafi cikin natsuwa ta isa inda aka buƙata data tsaya.
Cikin sanyin muryarta tace "Ya mai girma mai shari'a gani"
Ta faɗa tana sadda kanta ƙasa.
Kallanta alƙali yayi yace "Zaki iya faɗa mana sunanki, sannan menene dangantakarki dasu Baffah?"
Kallan Baffah tayi taga ita yake kallo, wani irin kallo yake jifanta dashi wanda bazata iya fassara wani irin kallo yake mata haka ba, cikin dakiya tace "Ya mai girma mai shari'a sunana Fatima Modibbo wacca aka fi sani da Binafa, dangantakar dake tsakanina dasu shine sun ruƙeni tun ina jaririya a matsayin ƴar da suka haifa ba tare dana sani ba,  sannan tun ina ƴar shekara goma na fara aure-aure, abun harya kasance na fara aure kan aure tare da damfarar mazajan danake aura, abun yana matuƙar damuna saidai na rasa yadda zanyiwa lamarin shiyasa na fawwala Allah lamarin, a haka har mukazo garin Kano bincike yayi bincike akan basune suka haifeni ba saceni sukayi, har suka buɗe bakunansu da cewar duk abubuwan da nakeyi ba'a cikin hayyacina nake yinsa ba, suna da malamin da yake musu aiki akaina don ya rufemin baki, wannan shine abun da naji Ya Mai Girma Mai Shari'a"
Babu abunda kakeji a Kotun sai hayaniyar mutanan wajan, saida alƙali ya tsawatar sannan kowa yayi shiru, Alƙali kallan Baffah yayi yace "Shin abunda ta faɗa gaskiyane?"
Baffah cewa yayi "Hakane mai Shari'a saidai bata faɗa maka maganar Sonta da ƙaunarta da nakeyi ba..."
Ba tare daya ƙarasa ba alƙali ya daka mishi tsawa akan yayi mishi shiru, kallan Inno yayi itama yace "Kina da ja da abunda aka faɗa"
Kanta a ƙasa tana tsiyayar hawaye tace "Ya mai girma mai shari'a bani da abunda zance, saidai ina zargin Baffah nima kamar yamin asiri, dan nima ba'a son raina muke barin Binafa tana aikata hakan ba saidai babu abunda zanyi"
Murmuhshi kawai Malamin da yake musu aiki yayi jin abunda Inno tace.
Alƙali kallan Malamin yayi yace "Shin Baffah ya taɓa baka aiki akan Inno kuwa?"
Malamin yace "Tabbas ya taɓa bani aiki, aikin shine akan kuɗine da Binafa ta samo suka fara rigima akan kuɗin shine yazo yacemin na rufe mata baki akan duk abunda ya bata ta amsa, bayannan kuma bai ƙara sakani wani aikin ba, domin duk abunda suke sakani nayi tare suke zuwa ko suyimin aike, tabbas banda ja da abunda Binafa tace ya mai shari'a"

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now