Page 24

183 21 55
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*


*24*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*Ahayye mata masu aji, mata masu ji da kansu, macen data yarda da kanta, shin kinsan akwai ingantattun maganin mata, sannan akwai sahihin maganin sanyi, tayaya zaki zauna babu gyara kina ƙyashin siyan kayan da zasu gyaraki amma kinsan ki tattala kuɗi kiyi adashi, anya wannan ajine kuwa?, ga dama ta samu dan siyan ingantaccen maganin mata dana sanyi, dan Allah idan kinsan baki shirya ba karkimin magana, karkizo kicemin ke ƴan 5h kikeso, kayana ba ƴan tagajan-tagajan bane, domin na yadda dasu wanda sukai amfani dashi suma sun yadda dasu, uwargida, amarya ki garzayo kizo ki nemi ingantaccan magani domin samun kima da daraja wajan mai gida, kina da yarinyar da zaki aurar amma kin rasa wani magani zaki bata?,to maza garzayo a haɗa miki ƴarki cikin sauƙi da rahusa, kin haihu kinaso ki gyada kanki amma kin rasa wani magunguna ya dace kisha?, hmm manyan mata kenan maza kizo a haɗaki miji ya kasa gane shin kin taɓa haihuwa ma kuwa*
Domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓeni ta wannan numbern 08130515037

Binafa hannayanta a harɗe tana kallan Safwan yanata faman yi mata faɗa, idonta ƙyar a kanshi abunda bata taɓayi ba, ganin Binafa batada niyyar tanka mishi yasashi ƙuluwa tamkar ya janyota ya hau duka, cikin tsananin ɓacin rai yace "Magana fa nake miki amma kinyi shiru kina kallona, wato ma duk abunda na faɗa akanki gaskiya ne, to ki sani aurenmu tamkar an ɗaurane babu fashi"
Murmushin gefen baki tayi tace "Ya Safwan kenan, shin kasan tun kafin kasanni Ahmad yake sona?, tun bana ƴar kowa yake ƙaunata, tun ina asalin mayaudariya yake sona, tun kan nasan menene so naga tsantsan soyayyata a idon Ahmad, tun yana ɓoyewa harya gaji ya furtamin kalmar so, amma hakan baisa na bashi fuska ba, kasan saboda me?, saboda ina sonka Ya Safwan, naso ace nayi yaƙi da zuciyata domin na watsar dakai a rayuwata don kuwa kaiɗin ba tsarana bane amma na kasa saboda zuciyata kaifi ɗayace intace tanason abu to tabbas babu fashi tana sonshi, dan haka yanke hukunci ya rage gareka daka yarda dani dakarka yadda dani duk ɗayane, nidai na faɗa maka sirrin zuciyata" tana gama faɗan haka ta tafi abunta ba tare data jira amsarshi ba, direct ɗakinta ta nufa kasancewar Window ɗin ɗakin yana kallan harabar gidan, tsayawa tayi tana kallan Action ɗin Safwan taga yaya zayyi, ganin yanayin fuskarsa ya tabbatar mata da yana cikin farin ciki mara misiltuwa, dariyar mugunta ta kece dashi tare da komawa kan Stool ta zauna tana faɗin, "Kamar yadda ka wahalar da zuciyata tabbas nayi alƙawarin wahalar da taka fiye da tawa, lokacin da nake neman agajinka lokacin kai fatali dani akan wani dalilinka mara amfani, lokacin da nake buƙatar raɓawa inuwa kaine ka kama hannayena ka sakani a cikin rana mai zafin gaske, lokacin da nake da ƙishin ruwa tafashashshen ruwan zafi ka kawomin tare da tursasani sainasha, harna sha na ƙone duk wani muradina na rayuwa, bazan manta dakai ba, domin ka yaudareni kaci amanata, zan kwatanta maka wannan kaji shin da daɗi ko ba daɗi"

Tunda Binafa tabar wajan Safwan ya samu natsuwa, murmushine ya suɓuce masa, danshi bai taɓa tunanin Binafa zata ƙara sonshi kamar daba, dalili kuwa yadda ya gasa mata aya a hannu, sosai ya yadda da ita, sonta ne ya ƙara kanannaye masa zuciya tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, ɗakin Mahmud ya nufa dan sauke gajiyar daya kwaso.

Wayar Binafa ce a hannunta tana kallan Screen ɗin wayar, ta kira Ahmad babu adadi amma No Answer ta rasa dalilinshi nayin hakan, tsaki taja a karo na ba adadi tare da shiga Message dan aika mishi saƙon godiya na wulaƙancin da yayi mata domin ta tabbatar da wayar na hannunsa dan daga ƙarshe wayar rejecting aka farayi, zama tayi ta tura mishi Text tare da alwashin inhar bai kirata ba babu ita babu shi, sannan zata canza Number kuma zata bar ƙasar gabaki ɗaya yadda bazai ƙara ganinta ba har sai tayi aure.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now