Page 22

207 21 6
                                    

*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*

*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*

'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''

*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)*

*WATTPAD*
*_MumIrfaan_*

 
                               *22*

*SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*

*_Ina matayan da sukeso su cancaɗa kansu wajan kwalliya ga atamfofi dasu laces, domin burge mai gida?, ƴar uwa maza garzayo kamfanin Mrs Maidala's Collections domin samun kayanmu mai sauƙi akan farashi mai rahusa, matso kusa ga dama ta samu wajan siyan takalman yara, takalman uwargida na kece raini, atamfofi, laces, jakunkuna, kayan kitchen da sauransu, siyan ɗaya ko sari muna aikawa ko ina dake faɗin duniyar nan bama a Nigeria kaɗai ba, domin neman ƙarin bayani ku tuntuɓemu ta wannan Numbern kamar haka 08162943828_*
*Domin samun shiga group ɗinmu wanda zaku runƙa ganin abubuwan da muke posting maza shigo cikin wannan Link ɗin, please bama bukatar namiji duk namijin daya shigo Allah ya isar mana*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gvu1O311g6pGZXFmwYiTuJ

Binafa kallanshi tayi ta kauda kanta gefe tace "Ka duba zakaga ko waye ma" ta faɗa tana kauda kanta gefe ga ƙirjinta na bugawa.
Kallanta yayi yace "Au haka ma zakicemin?"
Kuka kawai ta fashe mai dashi ganin da gaske wayar zai duba, kallanta yayi a gigice yace "Lafiya Binafa meke damunki?"
Cikin shashsheƙar kuka tace "Haba Ya Safwan yanzu fisabilillahi ace a tsakaninmu dakai babu yadda sai zargi tun kafin mukai ga aure, yanzu hakanka faɗomin ɗaki ba sallama bansan da mutum a ciki ba tsakaninka da Allah abunda kakemin kana kyautamin kuwa, maye laifina dan Allah?, kodan ina sonka shine kakemin duk abunda kaga dama"
Ajiye wayar yayi akan bedside drawer yace "Am sorry my Angel ni wallahi ba haka nake nufi ba, banaso in cigaba da sonki daga baya kuma naga kina tarayya da wanina ne shiyasa, but am sorry please bazan sake ba"
Tashi tayi bata tanka mishi ba ta cigaba da shashsheƙan kukanta ta shiga bayi ta rufo, tana shiga ta lumshe ido tare da kallan wayarta tai sauri ta goge numbern Ahmad tana sauke ajiyar zuciya ganin tasha daƙyar.
Safwan kuwa gajiya yayi da jiranta ya tashi ya fita tare da rubuta mata saƙon ban haƙuri a wata ƙaramar takadda haɗe da ƙara jaddada mata irin son da yake mata.
Tanajin alamun an rufe ƙofa ta fito tare da kwanciya akan gado, tausayin Safwan fal cikin ranta yadds take mishi abubuwa da dama yana jurewa, lumshe idanu tayi dan ba ƙaramin bacci take jiba.

*ADAMAWA STATE*

Fuskar Ahmad shinfiɗe da murmushi ya fito daga motarsa tare da saka mata key yana maijin sanyi a cikin zuciyarsa, ƙanwarsa ya gani wacca bata wuce sa'ar Husnah ba ta taho da murna tana mai Oyoyo, fuskarsa kadaran kadahan ya amsa mata kasancewar Ahmad bai cika sakewa ƙannan sa ba saidai yana matuƙar kyautata musu sosai, hannun jakarsa ta ansa tana me mai sannu da zuwa, direct part ɗinsa ya wuce domin yanaso yayi wanka sannan yaje ya gaida Mom ɗinsa.
Wanka yayi tare da sallolin da ake binsa ya saka jallabiya wacca ta amsa jikinsa ya fito ya nufa part ɗin mahaifiyarsa, suna zaune suna kallan wani series film gabaki ɗayansu hadda Mom ɗinsu.
Kallan agogo yayi yaga goma saura na dare, gyaran murya yayi kowa ya watse, yayin tunda Ahmad ya shigo ɗakin ƙamshin turaransa ya sanar da Husnah kasancewar tazo musu hutu kuma tana da buƙatar ganin masoyinta dan kwana biyu bata sakashi a idanunta ba, kallanshi take tamkar mayya har saida Haajara ta taɓota tace "Tashi muje kafin ya fara bala'in nasa" hannunta taja suka shiga ɗaki, shiko Gogan bai masan tanayi ba domin baisan tana gidan nasu ba.
Mahaifiyarsa tana ganinshi tace "Babana naga kana ta fara'a ne yau anya lafiya kuwa?"
Nurmushi kawai yayi tare da gaishe ta, shirune ya biyo baya kallan agogon hannunsa yayi yace "Mom bari naje na kwanta kema yaka mata kije ki kwanta domin dare yayi" yana gama faɗan haka ya fita yana mata murmushi.
Mahaifiyarsa yanzu halinsa na rashin magana ha daina bata mamaki ta gane hakan halittarsa ce domin tun yana yaro haka yake bayason hayaniya ko kaɗan, murmushine ya suɓuce mata tace "Zanso naga randa Babana zai fara soyayya itama shirun zai runƙa yi mata koko yaya"
Tashi tayi taje ta kashe kayan kallon itama tahau Upstair dan ta samu ta kwanta.

CHAKWAKIYAWhere stories live. Discover now