*🌺🌺🌺CHAKWAKIYA🌺🌺*
*_HIKIMA WRITERS ASSOCIATION_*
'''Home of peace, joint of entertainment, to educate and enlighten our readers'''
*MALLAKAR*
*_'Yar Gafai_*
*(Mum Irfaan)**WATTPAD*
*_MumIrfaan_*
*14**SADAUKARWA*
*_Teetee me rice_*
*_Mrs Audu_*
*_Oum Ramadan_*Inna sai shirya kayansu suke, yayinda Baffah shi kuma ya nemo dillalai akaima gidan kuɗin ya sayar ba tare da sanin Binafa ba, tunda Baffah yaje katsina shikenan Binafa ta koma ruwa duk abunda sukace mata ya zauna bata jayayya dasu koda kuwa tasan abunda suka sakata ba daidai bane, amma haka zata haƙura tabi umarninsu, tunda suka faɗa mata an saida gidan ta gyaɗa kanta ba tare datayi jayayya ba, amma a ƙasan ranta kuwa ko kaɗan bataji daɗin hakan ba, saidai babu yadda zata iya.
Ganin tabbas garin Kano zasu bari yasata satar jiki ta fito, tana fitowa ta samu Numbern Safwan ta kirasa amma bai ɗauka ba, ta daɗe tana kira amma no Answer, harta ajiye wayar saboda kiran da tai tayi yaƙi ɗauka, sai kuma ta ƙara kira a karo na ba adadi, harta kusan tsinkewa taga an ɗauka, da sauri ta kara a kunnanta tace "Hello Safwan!".
Shiru taji anyi ta ƙara dakewa tace "Baka jinane?"
Safwan yace "Binafa wai mai yasa kike bibiyata ne?, na faɗa miki gaskiyar abunda ke zuciyata amma kinƙi ji, nifa Love game nai miki yaka mata ace kin manta da komai"
Ajiyar zuciya tayi tace "Insha Allahu hakan nake fata, yanzu kana ina?, inaso mu haɗu ne cikin gaggawa akwai abinda zan baka mai muhimmanci"
Shiru yayi naɗan wasu lokuta yace "Gaskiya yanzu haka ina gida, ki bari idan na fito zan shigo..."
Katse shi tayi da cewar "A'a Safwan, bai zama dole na ƙara awa biyu ba a garinnan, please kaimin kwatancan inda kake gani nan"
Shiru yayi yana kallan Mommy data kafeshi da ido tana murmushi, dan duk a tunaninta da budurwasa yake waya, shiyasa ta godewa Allah da yanzu Safwan ya fara kula ƴan mata, dan kuwa ƙin kulasu yayi yana Jiran Fatima ta dawo garesa, duk da kowa ya cire rai da ita amma banda yanzu da Kande ta basu labarin komai.
Cike da ƙosawa da maganarta yace "Bari zan turo miki da Address ɗin" katse kiran yayi ya tura mata Address ɗin, ya gyara kwanciyarsa akan 3 seaters ɗin da yake zaune, Hajiya Hauwa batace mai komai ba, ta miƙe tace "Saura in tazo ka barta a waje, kuma ka hanata zuwa ta gaishe dani dan nasan hali"
Sosa ƙeya yayi yace "Mommy junior ɗinace fa ba komai ba"
Murmushi tayi tace "Koma wacece" tare da barin parlourn.Binafa kallan Address ɗin gidan tayi ta samu mai Keke Napep taimai kwatancan gidan, kasancewar gidan Alhaji Modibbo ba ɓoyayye bane yasa bataci wahalar gane gidan ba, yana ajiyeta a ƙofar gidan mai adaidaitar yace "Wannan ne gidan Alhaji Modibbo" ya faɗa yana nuna mata tamfatsetsen get ɗin gidan"
Bin gidan tayi da kallo ganin yadda aka ƙawata gidan da flowers, ƴar purse ɗinta ta ciro ta bashi kuɗin ta nufa gidan, knocking ta farayi Getman ya fito tare da tambayarta ina zata kuma gunws tazo, kasa amsa mai tayi ganin yana damunta da tambaya, wayarta ta ciro ta kira Safwan nan take ya shaida mata gashinan zuwa.
Komawa tayi ta ɗan tsaya a jikin get ɗin tana ƙarewa girman gidan kallo, jin an buɗe ƙofa taga Safwan ya fito, tana kallanshi taga ya ƙarayi mata kyau da kwarjini.
Murmushi taimai tana ƙoƙarin gaishe dashine yace "Nu shiga ciki ko"
Ba musu tabi bayanshi suka shiga, kallan wagegen filin gidan ta tsayayi ga kuma parking space can wanda a ƙalla motoci sama da goma zasu zauna a wajan ba tare da takura ba, ita dai ba baka sai kunne haka ta koma, jin ya tura ƙofar parlourn yasata shiga a ɗan tsorace ganin har yanzu bataga mace a gidan ba sai ma'aikata, kallanta yayi yace "Ki zauna"
Ɗosana ɗuwawunta tayi a tsorace tana wuri-wuri da ido, baifi minti biyar ba saiga Safwan ya dawo yace "Mommy na zuwa zaku gaisa".
Gyaɗa kanta kawai tayi ta kasa cewa komai.
Tunda Hajiya Hauwa ta hango Binafa gabanta yayi mummunan faɗuwa, daƙyar ta samu ta ƙarasa wajan tana faɗin "A'a wannan ce surukar tawa?"
YOU ARE READING
CHAKWAKIYA
FantasyBinafa tana zaune a tsaƙar gida daga ita sai wani gajeren wando daya wuce gwiwarta sai wata riga wacca taɗan matseta kaɗan kanta babu ɗan kwali gashin kanta ya sauka har gadan bayanta, tana zaune tana jujjuya abincin ta kasaci, ta lula tunanin duniy...