💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
Wattpad https://my.w.tt/Su8JNMVKlcb
PAGE4️⃣6️⃣
Wani irin farin ciki ne ya lullube amjaad na albishir din da doctor yayi mishi ,don yama rasa wani irin murna zaiyi goshin sa yasa a k'asa yayi sujudud shukur yana me godiya ma Allah na wannan kyauta daya bashi a lokacin da bai zata ba ,dagowa yayi ya dubi doctor da shima murmushi yake mashi har lokacin"doctor kyautar ka ta musamman ne na wannan albishir dakamin yabashi hannu sukayi musa buha "zakaji alert bwrin nutsu.
"to godiya nake rankashi dad'e.
dasauri ya shigo falon yaga ba kowa aciki , direct sama yanda d'a kunan suke ya nufa yazo step din karshe na fito daga d'akin sateera zanyi kitchen na dibo kunun tsamiya naga hauro wanshi ,ja nayi na tsaya cak naji ya d'agani sama yana juyi dani,kan kameshi nayi don na fara ganin hajijiya .
" please amjaad ka saukeni kar wani yazo ya ganmu a haka ,kuma wallahi jiri nakeji .
cak ya tsaya da juyanin da yakeyi ,kujeran dasuke corridor gurin ne ya ajiyeni akan d'aya yana min sannu .
sanda jirin ya sakeni sannan ya kama hannuna" zomuje na nuna miki wani abu, kallon shi nayi batare da nayi magana ba .
ahankali nake sauko wa daga step din don har yanzu jikina baimin dai dai ba,gidan mu muka je muka shiga tare da sallama a bakin mu , falon ba kowa aciki harta tv a kashe yake ,sashina muka je nasa key na bud'e tareda shiga baki na d'auke da addu'a na neman tsari .
duk wani abunda yama jamcy data had'a min sharri ya gayamin se dai abun guda daya b'oye min ,don wannan sirrin matar shi ne.lumshe ido yayi bayan ya gama gayamin abubuwan da yafaru a Dan tsukin nan da yanda ya gano jamcy ne ta had'a komai.
wato wani abunda ya boye masu da basu sani ba shine ,tun daren daya samu rumana ba'a CIKAKKIYAR MACE ba ya fara binciken da wanda take mu'amula anan ya gano jamcy ita ma tana mu'amula da wanda rumana takeyi takuma bashi yarda sama da kowa ,don da shi kad'ai take tsananin jin dad'in mu'amula,duk wani bin mazan da takeyi harda taimakon jamcy don ita ke ingiza ta ko bata da ra'ayi,tun daga ranar yake neman hanyar da zai rabasu se ga wannan abun ya shigo yayi mata me gaba d'aya ,ya bar ita rumanan ne don yaga iya hankalin ta .sannan baya son ya gayama khubra aibun rumana ne don itama matar shine ya zama dole ya b'oye sirrinta,don baza taji dad'i ba idan ya futar mata da sirrin ta .
yau aka sanar da sauke senator daga mukamin shi labari ya karade duk wata kafa data ke sadarwa ,take ya yanki jiki ya fad'i yaransa suka tattareshi zuwa asibiti.
yau na tashi jikina da dan karfi don har na gyara sashina tsaf don gani nayi kwana biyun da bani gidan yayi kura .
kwance nake a main falo naji sallama kamar na kakus ,sake gyara kwanciya ta nayi don gaskata me sallamar still muryan ta nasake ji da sauri na d'ago Ina kallon yanda naji sallamar,da murna na k'arasa kusa da ita na rungume ta "nayi fushi kakus ,tun zuwanku da kuka kawoni ai nasan yanzu baki sona na k'arasa maganar da turo baki na gaba.
baki kakus ta bud'e "ke Yar nan me zan gani haka?duk kin zabge kamar wata me cutar HIV? dai dai nan rumana ta futo daga sashin ta take ta tsargu da maganar kakus,daure wa tayi ta k'araso cikin falon ta durkusa tagaida kakus wacce take tsaye har yanzu tana al'ajabin ramar danayi.
"cikin sakin fuska kakus ta amsa ma rumana gaisuwar ta tareda tambayar ta yaya iyayenta suke "dafatan dai kuna zaune lafiya dai ko? kunsan zama guri d'aya seda hakuri da juna .

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...