Chapter 22

464 57 0
                                    

💍CIKAKKIYAR MACE💍

  ✍🏻 Rashida Bature

PAGE2️⃣1️⃣

Ay ! tabbas kece mahaifiyar ta kwarai sannu da zuwa hajiya mu k'arasa daga ciki cewar kakus wacce rabe yaje yakirata don tazo taji me Inna saratu tace .

"afalo kakus da hajiyar amjaad suka zauna suna gaisawa nashigo falon bakina dauke da sallama na nufi kitchen na zuba dambun nama na d'auko cucumber juice da ginger juice se laidar pure water guda biyu na jerasu akan babban tire na nufo falon yayi dai dai shigowar amjaad da safwan Wanda rabe yamusu jagora zuwa ciki.

"tsugunawa nayi tareda ajiye tiren hannuna na rusuna nagaida hajiyan amjaad ,kaina ak'asa tareda girmamawa, hannu ta mikomin maza matso kusa dani "yata Allah yayi miki albarka ahankali nace amiin ,na kwantar da kaina akan cinyarta hajiya ne ta dubi kakus tace amma gaskiya kunyi dacen samun nagartacciyar yarinya kunyi kokari wajan tarbiyan tar da ita ,tashi daya tashiga raina ,ta duben tace

" yata wani makaranta kikayi haka kikasan komai na rayuwan zaman duniya?

"Fuskata na rufe Ina me cewa center malama zuwairiyya nayi mune daliban da akafara yayewa a center .

"Mashà Allah to karatun boko fa ?ko haryanzu anakanyi ne?

"A'a daga secondary School na tsaya .

"Kakus ta kalla tare da cewa meyasa baku barta taci gaba da karatuba ?a yanda ta taso da basira be kamata ace kun dakatar da ita a iya secondary School ba yakamata ku bata da ma tasamu ilimin da nan gaba zata taimaki kanta takuma taimaki al'ummar kasanta .

A'a hajiya ni dakike ganina inda inada hali to ko bangon duniya ake zuwa don ayi karatu zanbiya ma khubra tayi , to dayake ubanta yaga bandashi shine ya kama bakin aljihunshi ya rufe ruf yace karatun ya isa haka yayi kokari ma daya barta ta gama secondary School din don kaf garinnan babu wacce ta taba gama secondary se ita ,amma dayake ita Yar albarka ne daya hana seta kama sana'a don Sam batason zaman banza.

In bazaku damuba zanso ganin mahaifinta duk da bansan ra'ayinshi na hanataba zan tuntubeshi naji inda hali abartan taci gaba don da ganima bawani shekaru ne da itaba .

Ashe kin gane du du du shekaranta 19 ne ,ni dai daman na zuba mashi ido ne naga iya yinshi innagaji nasanyata amakarantar da ranta yakeso .

to qamshi tashi mata ajikin mana tasamu tasha ko ruwa ne ,kekam da son jiki sekace kuliya duk kimbi ki nadeta, Kakus tayi maganar tana me tsiyaya ma hajiya juice a cup .

"mikewa nayi tareda duban su safwan idonane ya hard'e dana amjaad  ya watsomin harara nima na rama na koma gefe nace ya safwan anwuni lpia ,lafiya lw yar hajiya ya kokari da jama'a? nace alhamdulillah .

"na mike naje na kawo musu suma ruwa da juice na ajiye tareda tsiyayawa a cups zan mike naji amjaad yace kaka ni banison wannan kunun aya zansha tace to ai akwaisu khubra maza jeki canzo mishi .

"naje na d'auko kunun ayan na zuba mishi na bari akan tiren batareda na mika mishiba nayi tafiyata d'aki . hajiya da kakus se hira sukeyi tamkar daman sunsan juna , amjaad ne ya mike ya nufi hanyar waje safwan yace Ina kuma zaka?

"be kulashiba sannan bai dakata ba kakus tace yaro na bakaci komaiba zaka futa ? juyowa yayi yace kaka takawo min mota zan danyi abune kafun hajiya ta gama .

khubra ! khubra yi maza kizo ki kaima jad abunsha a waje .

"futowa nayi nace kaka waye za'a kaimashi abu wajen?

"yaron nan jaad ne wai zaiyi abu a mota shine yace kibishi da abunsha waje .

"dubanta nayi sororo, wai ni kaka waye kika samu me suna" jaad "?

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now