Chapter 27

478 53 1
                                        

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻 Real Rashida Bature

PAGE 2️⃣6️⃣

Yau tsawon sati guda kenan rabonshi da kirana ,agefe guda hiran da mukayi ranar yaki futa azuciyar amjaad ,isan y lumshe ido ba abunda yake kiyowa a kunnuwanshi illah sautin daddad'an muryana ina zuba mishi kalamai na .rintse idon yayi tareda mik'ewa yashiga bathroom ya jima aciki kafun yafito ya shirya.

"falo ya nufa domin yin breakfast mom ya tarar itada autar ta wato sateera,zama yayi a d'aya daga cikin kujerun dining gaisheta yayi tareda suban sateera wacce take gaisheshi dubanta yayi yace sarkin rigimar gidannan ya akayi daga ganin wannan gaisuwar da alamar tambaya , dariya tayi tace no bros kawai dai Ina tuna makane Inka sake komawa kadan  siyomin cinnaka kaji bros?

dubanta yayi yace miye cinnaka?
Kai bros karkacemin harka manta da abunda kasiyomin dinnan Wanda kawata ta sammin har nace kasiyomin agarin buzaye.

oh na tuna amma karkisa ranki don ban Miki alkawari ba .
Kai bros please tayi maganar tana had'e hannayan ta waje d'aya,ta dubi mom cikin shagwaba tace mom kisa baki mana kinji bros ko?shareshi zaima sayi miki karki damu yi maza ki gama karki makara .

"futowa yayi daga sashinsu ya nufi sashin hajiyan shi,ya tarar da ita zaune a falo tana magana da me mata abinci zama yayi a d'aya daga cikin kujerun falon yana me jiran ta kammala ,bayan hajiyar ta sallami me aikinta ne ya taso ya d'aura kanshi a cinyar ta yana cewa hajiya ta antashi lpia , lpia lw amjaad ya aiki da d'awainiya alhamdulillah hajiya ,anfito kenan za'a tafi?
            "Ey hajiya "
to madalla Allah yayi miki albarka yasa afuta a sa'a ya karemunku daga sharrin mutum da aljan.
      "Amiin hajiya"

"ammm hajiya nace nikam da abba sukaje gidansu rumana abba ne yace zaku aura min wata bayan rumanan?

"gyara zaman glass din idonta hajiya tayi ta dubeshi dakyau tace wani abun kagani ?

"ey to ranar ne tasamen da zancen wai ance mata su biyu za'a auramin shine abun ya d'auremin kai don nasan ita kad'ai ce don banji kunmin maganar ba.

"Ey to maganar gaskiya akwai yarin yar data kwanta min araina sannan nutsuwarta yayimin, kuma nake ganin dacewar ku da ita ,shine naje na nema maka auranta dafatan bazaka bani kunya ba ganin nacika wannna kyakykyawan halak'a danakeson k'ullawa atsakaninku.

"shiru amjaad yayi yana me duban kakan tashi idonsa har sun canza kala sannan yace yanzu kema hajiya auren dolen zakimin kamar yanda abba zaimin , hajiya Ina zankai mata har guda biyu ?
ku tausayamin don Allah . amjaad kenan bazaka gane nufina ba ayanzu amma asannu zaka fahimci hikimar danayi naganin an had'a aurenka dana wancan yarinyar ,da raina da lafiya ta bazanso naga kashiga wani yanayi ba dake allah yana duban zuka tanmu seya had'ani da yarinyar nan take kuma yasanyamin kyaunarta inakuma da tabbaccin kaima inka ganta kaga halayyar ta na tabbata zatayi maka .

"kanshi ya saukar kasa daga kallon ta dayakeyi yace hajiya bawai naki taki bane wallahi ni Sam atsarina banida tsarin nayi mata sama da d'aya amma tunda har kin sanya manya aciki wallahi bazan tab'a miki jayayyaba don nasan kinada iko akaina ne shiyasa kika yanke hukunci nagode da Wannan karramawa Allah ya kara girma yajikan mahaifa.

"amiin amiin Allah yamaka albarka yasa wannan aure ayishi asa'a ,na tabbata in sha Allah bazakayi dana sanin yimin biyayya ba zakuma kaji dad'in zab'in danama ,maza tashi ka tafi gurin aiki Allah yatsare yadawomin daku lpia.

jikinshi babu kuzari  a hankali yake tuk'i har ya isa kamfaninsa , direct office ya nufa ma'ikatan sa sunata gaisheshi amma sam bayima ji balle yasan me suke cewa.

"ahankali ya nufi kujeran office d'in Wanda yake mallakin sa zama yayi ya kifa kanshi akan table din yayi shiruuuu domin sam brain d'inshi takasa aiki .

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now