💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
Wattpad https://my.w.tt/Su8JNMVKlcb
PAGE4️⃣8️⃣
yaran ya mika ma sateera datake ruke dasu ajikinshi gaban mom ya dawo ya tsugunna mom kimin rai wallahi banji Kiran datamin ba ,tana Ina ?da gaske mom ita kad'ai ta haihu innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, wallahi mom bansan bata da lafiya ba,mom ki taimaken ki gayamin tana Ina ya k'arasa màganar jiki na mazari don duk ya futa a hayyacin sa."sama ta nuna masa duk da bata nuna mai takaman man d'akin danake ba ya tafi a sukwane kamar Wanda ake turawa.
karb'an d'aya rumana tayi fuska d'auke da murmushi,bayan taga daya ne ta kuma karb'an dayar hannun sateera se yaba kyawunsu takeyi .
Ina bàrci naji an kwamushi dakyar nake futar da numfashi a wahar ce nace"waye zai kasheni ?
dariya amjaad yayi yana me juyowa dani ya rungumoni yana sauke ajiyar zuciya,sakeni yayi "sannu baby kinyi kokari sosai , nagode da wannan kyautar da Allah yabamu nagode miki dakika haifa mun ababen sona ,sake rungumoni yayi ,bata fuska nayi don naji haushi Kiran shi danayi a waya bai dagaba nakuma haihu sanda na hantse kafun ya zo .juya masa baya nayi batare dana yi magana ba ,juyo dani yayi tareda cewa"kiyi hakuri baby wallahi banga kiranki ba se yanzu da mom ta tura nazo shine take gayamin ,kema kinsan babu yanda za'ayi naga kiranki ko baki tareda wani abu naki d'agawa bare kina da tsohon ciki,ban kulashi ba ya karaci magiyar shi adole Sena seke na dawo normal muna haka rumana ta shigo d'akin ,zama tayi tana min barka da arzik'i itama ban wani sake na amsa mata ba don dukansu hau shin su nakeji ,ganin ban sake mata bane yasata ajiye min yarinyar hannunta tace"barinje nayi wanka na shirya Sena dawo ko akwai abunda za'ayi Miki yanzu?
fuska ba walwala nace"ki tambayi mom na gyara kwanciya na nabasu baya ,shiru tayi zuwa can ta futa a d'akin .dawowa gabana yayi ya tsureni da Ido "wai baki yarda da abunda nace Miki bane ?
"hmmm zaifu maka kyau idan kabi matar ka kukaje kukayi wankan tsarkin kafun ka dawo ka tabamin yara ,don ko baku fad'a akwance kuke ba yanayin kayan jikinku ya nuna don haka zaka iya tafiya na rufe ido na kamar mai barci don ba k'aramin haushinsu nakeji ba a lokacin ,ace ka haihu tun asuba kuma kuna gida d'aya ba miji ba kishiya ,har wasu sunzo amma ace mijin dayayi cikin bai zo yaga me aka haifa masaba bare yayi batun lafiyar uwar .
ganin bazan kulashi bane yasashi futa falon baiko d'auki yaranba duk kwadayin sa da yaran ,gurin mom ya nufa fuska ba walwala "son ya na ganka haka?
"na rasa me zan gaya mata ta yarda mom .
"ko nice abunda zanma seyafi Wanda tayi ma yanzu ,kana magidanci ace har a shiga gidan ka a futa da matar ka baka saniba duk hidiman da mukayi aciki kuna can kaida matar ka a kwance saboda rashin hankali,daka dawo daga masallaci base ka duba ta kaga ya ta tashiva amma saboda sakaci irin naka ,ai itama rumanan macece bazata so ayi mata hakaba saboda irin haka nace ka maido ta nan tunda cikinta ya tsufa amma fur kaki.
da a zahar kakus dasu Zahra su siyama sukazo gidan zuwan su ne ma ya man tar dani haushin amjaad dana keji na sake a cikinsu se murnan samun jariran sukeyi suna murnan na haihu lafiya, se daf magriba suka koma aka barmin kakus .
yau ta kama suna yara sunci sunan su da suka zo dashi hassana da hussaina, anci ansha bukin suna ya kayatar , amjaad yamana kaya kam ba laifi don ya had'omin da lefe na dabai minba ,taro ya watse lafiya .
Gyara kam nashashi mom tana min nata agefe guda kuma kakus tayin itama nata .
Kwance tashi ba wuya yara sunyi girma abunsu ,don harsun fara zama .rumana ma yanzu ta fara laulayi don tunda tayi hankali ta sadudu amjaad ya dauketa sukaje akamusu kwajin cututtukan zamani aka tabbatar masa da bata da wani cuta ajikinta ya dawo yayi mata fad'a ta bashi hak'uri suka dawo normal life d'in su kamar kowani ma'urata,yabata motar dataki karba da takarba harda godiya .
rumana ta haifi baby girl aka sanya mata sunan hajiya muna kiranta little .
Bayan shekara bakwai nasake haifan twins duka maza sukaci sunan alhaji na da alhajin amjaad,bayan na yaye sune muka tattara mukaje aikin hajji dukanmu gidan ,na kara dawowa wata CIKAKKIYAR MACE na gaske don komai ya zauna min ,ga wani irin farin dana kara tamkar jini zai futo ajikina.
iyayen mijina muna zaman lpia dasu suna matukar sona nima Ina kyautata musu,shirye shirye bikin satira mukeyi da za'ayi nanda sati biyu masu zuwa zamu kaita Abuja don tare zamu koma amma amjaad Karin girma agurin aikinshi,kamfaninshi ma se bunkasa take dadayi.
*ALHAMDULILLAH*
nagode ma Allah daya bani ikon kawo karshen littafin CIKAKKIYAR MACE ,kurabkuran dake ciki Allah ka yafe min fadakarwan ciki kuma Allah kasa masu hali irin haka Allah yabasu ikon gyarawa .Nagode masoya na masu bibiyar labarina damasu kirana ,kaunar ku agareni ne yasani kaiwa nan NAGODE SOSAI Allah yasake hadamu a littafi nagaba ,domin salon ba irin wannan bane .

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
General FictionLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...