💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature
*SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''
Wattpad https://my.w.tt/zq9Wot0H9bb
PAGE4️⃣4️⃣
Dafani mom tayi "khubra ya kamata ki sassauta ma kanki haka nan , kifawwala ma Allah komai duk wanda yayi hakan don ganin ya k'ullamiki sharri in sha Allahu kanshi abun zai koma ,kiyi hakuri karki sanar da gidanku kibar komai ma amjaad zaiyi buncike akan haka,don ma alhaji baya gari dubi yanda duk kika zabge a kwanakin nan ,ko abincin kirki bakici daughter,ki sanifa yanzu bake d'aya bane dole zakina daurewa kikecin wani abun ko yaya ñe .*****
K'ass k'ass kakeji Karan cumgum d'in ta duk yabi yacika falon da k'ara ,da sallama ya shigo cikin falon kallon rumana yayi yaga se taunar cumgum d'in ta takeyi ga shigar data sabayi ako yaushe na d'amammun dogayen riga Wanda suke bayyana tsamure wan jikinta ga kid'a na tashi tana rausaya kanta hankali kwance,shigeta yayi batare da yace mata komai ba don ita ya kamata ta mai sannu da zuwa bashiba,haurawa sama yayi don rage kayan jikinshi harara rumana tabi bayanshi dashi tare da cewa"munafikin banza munafikin hofi haka zaku karaci iyayenku kadawo da lgidannan waiku makirci ka d'auki matar so batajin dad'i ankaita ma uwar miji ,tsaki ta sake ja tareda gyara zaman ta tana kad'a led d'in ta duk da batajin dad'in jikin ta amma baya hanata jin haushi inta tuno khubra bata gidan ,bata tashi daga gurin ba har amjaad yayi wanka ya sauya kayan jikinshi zuwa nashan iska ya futo falon ,dubanta yayi ya dubi kan dinning yaga ba alamar kular abinci akai zama yayi a d'aya daga cikin kujerun falon ya ciro wayarshi yana dannawa.
"Ina abinci na ?
yayi maganar batare da ya dubi inda take ba.
a yatsine rumana ta dubeshi"banyi ba nima dakyar na dafa makaina indomie.
Kai amjaad ya kad'a tareda sake tamke fuska alamar ba wasa alamarin "nabaki nan da 5mints ki tabbatar kin samamin abunda zanci,kuma in har kikamin jagwal-gwalenki to ki kwan da Shirin tas sekin cinye stupid girl ahakan ne kike ikirarin kina son miji ? wannan 'yar indomie sassauk'a baki iya dafawa ba,kuma dayake Sam baki da kunya kin iya bud'e baki kice ma mutum baki iyaba ke ko kunya bakiji?kiduba dai ki gani a girme kin girmi khubra amma tafiki sanin yanda zata tafiyar da miji ,tabashi kulawar daya dace,kekuwa ko d'an sannu da dawowa bakinsan ki tari mutum dashiba ,kin wani lakuye ajikin kujera sekace wata tsumma,gara ki taimaki kanki ki gyara inba hakaba banga ta yanda kike da ma mora ba,a gadon ba dad'i kike dashiba, d'an girkin ma da za'a ce kin sace zuciyar mijin dashi inkin yinma ba dad'i yakeyi ba bare fasali,a kyawun suran ma mutum sedai ayi manage,dama kin zo da mutum takan ki ne gidan aurenki may be kiyi daraja a Ido na, to wallahi gara ki nema ma kanki mafuta tun lokaci bai k'ure mikiba ya kareshe maganar da jan tsaki.
wani irin bak'in ciki ne ya tushe ma ruma ba k'awon k'irji tareda wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata akan fuskarta,bata damu data share ba don tasan tabbas duk a bunda amjaad ya fad'a agame da ita gaskiya ne amma gaya matan da yakeyi a gabanta tana ganin kamar cin fuska ne hakan ,tashi tayi batare da ta kulashi ba ta nufi kitchen don bata jin magana yau .
tsayiwa tayi tana nazarin me zata girka mishi Wanda zaiyi dama dama ,ganin bata da wani abun da ta iya se indomie shine take da tabbaccin zai iya ci.
kan dinning ta ajiye mishi tareda ruwa da duk wani abunda zai buk'ata sannan ta dawo gurin dayake
"na gama ."
" Ok "
abunda yace tare da cigaba da danna wayar shi se zuwa can ya mike yanufi kan dinning,zama rumana tayi a yanda ta tashi tareda cigaba da kallon ta.
tunda ya zauna akan kujeran dinning bai motsaba se Ido daya tsura mata,ganin bata da niyar tasowa ta zuba mishi ne yasashi cewa "in bazaki zuba min ba kizo ki kwashe kayan ke komai se angaya miki yanza zakiyi ne?
jiki ba kuzari ta nufi dining ta bud'e ta zuba mishi tare da tsiyaya mishi fresh milk a cup ta juya ta koma gurin zaman ta ,tsaki yaja ya d'auki wani cup din ya tsiyaya ruwa aciki , indomie ya kalla ya tab'e baki yayi bisimillah ya faraci ,bai wani ci dayaba ya ture daga gabanshi don Wanda yacin ma daure wa kawai yayi bawai don dad'i ba,fresh milk din yasha sosai don ta gusar da masa da yunwan dayake ji ,sanda yaji cikinshi tayi mishi dai - dai sannan ya mik'e yayi sama ,bai jima a dakinshi ba ya fito ya zauna a falon, channel ya canza suna zaune suna kallo ,k'arar maganar tv ne kawai ke aiki a falon don yau tun tashin rumana takejin wani iri duk jikinta ba k'arfi.
zaune suke suna kallon labaran k'arfe 7 a tashar batv hoton da aka hasko a allon tv shiya furgita rumana ta mik'e tsaye jikinta yana mata kyarma ,hannunta akan tv ta kasa magana idonta na tsakanin amjaad da tv tama kasa tsayar dashi guri d'aya, kafad'a amjaad ya d'aga tareda mik'ewa yayi fucewarshi zuwa cikin gidan su , direct falon mom ya nufa ,yazo dai dai sashin hajiya sukayi kicibus da ita ta fito a rud'e ,batama lura da amjaad ba ta nufi sashin mom.a falo hajiya ta iskemu ni da sateera da mom munyi cirko cirko muna kallon tv dasuke labarai .
salatin hajiya ne ya dawo mana da hankalin mu gare ta , yace" oh duniya Ina zaki damu ?yanzu shi wannan abu dame yayi kama fisabilillahi?mom tace Abu kam babu dad'in ji bare gani sedai kawai muce innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, shigowar amjaad ne yasa hajiya maida hankalin ta kanshi tace amjaadu shin kaga abunda nagani kuwa ni fatu ? innalillahi wa'inna ilaihirraju'un ta samu guri ta zauna amjaad ne ya canza channel din suwa sunna tv ,ya k'araso kusa dani ya cire min hannu na danayi tagumi dashi "banson yawan damuwan nan dakikeyi ,ai komai yazo k'arshe don nagama da komai saura su karb'i nasu tashin hankalin ,Ina me tabbatar miki duk Wanda yamiki sharrin nan yanzu haka shima nashi atashe yake don nagama da komai .Ido na tsura mishi kamar maison gaskata abunda yace , murmushi yamin tare da lakuce min hanci , sunkuyar da Kai nayi don ganin abunda yamin sannan ya zauna daf dani jikinmu yana had'e dana juna ,shi ko kunyar su mom baya ji,matsawa nayi daga kusa dashi ya kamomin hannu tareda jawoni jikinshi yana cewa "mom kinga baby ko? harara ta wurgo mishi daga inda take tsaye "wai son meyasa baka da kunya ne ? duk kabi ka takuramin yarin ya da tana zaune k'alau amma daga zuwanka zaka dameta to oya tashi ka bamu waje muji da abunda yake faruwa..
RASHOWS

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Genel KurguLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...