Chapter 40

436 42 0
                                        

*💫⭐SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION💫⭐* 

'''{The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers}.'''

💍CIKAKKIYAR MACE💍

✍🏻 Real Rashida Bature

PAGE3️⃣9️⃣

bani na farka ba se wajan k'arfe 2:30,shima sateera ne ta tasheni nayi sallah amma bawai don barcin ya isheni ba.

"amjaad ne yadawo daga office bayan ya bud'e k'ofar falon yashigo ciki, duban falon yayi yaga ba kowa harta tv ma akashe yake ,haurawa sama yayi don yin uzuri a bathroom d'inshi,bai fito ba sanda ya tsaya yayi wanka kafin ya fito ,mai ya shafa ma jikinshi yana mamakin rashin ganin d'ayanmu adakin nasa har yanzu ,a gurguje yasanya jallabiya,ya feshe jikinsa da turaruka sannan ya sauko k'asa don dubamu don jinmu shirun dayayi, d'akin rumana ya fara shiga don duba lafiyar ta ,bai isketa a d'akinta ba ya dudduba har bathroom ko tana wanka ganin bai ganta bane yasa ya juyo zai futa yana mamakin Ina taje batare da sanin shiba ?
harya wuce ya Kai bakin k'ofar bedroom dinta ya juyo don ganin pack din condom da wasu tablet akan mirror d'inta da yayi,dawowa yayi da baya ya duba pills din sannan ya d'aga pack din condom din yana dubawa ga receive a gefe ,da alama ma yanda aka siyo ne aka ajiye agurin , d'auka yayi ya Sanya a aljihunshi sannan ya futa a d'akin.

saida ya koma d'akin shi ya ajiye abunda ya d'auko daga d'akin rumana sannan ya rufe kofarshi da key,saukowa yayi ya nufi sashina , murd'a handle din k'ofar yayi yajita akulle ,mamaki abun ya bashi to Ina mukaje kuma mukabar kofar falo abud'e,alhalin munsan lokacin dawowarshi gida yayi?

"fitowa yayi yanufi cikin gidan su , direct sashin hajiya ya nufa,a falo ya isketa tana cin abinci ,ganinshi yasata washe fuska tana murmushi tace yaron kirki andawo?
Kai ya gyad'a mata batareda yayi maganaba ,ya samu guri ya zauna yace Kaka na sameku lafiya?Yaya kika karajin jikinki?

alhamdulillah jiki se godiyan Allah,masha Allah.

Dubanta yayi yace khubra fa don yasan itace ke shigowa cikin gidan?

Hajiya ma kallonshi tayi tace bata gidan kane?

Kai ya d'aga mata .

ka duba gurin mahaifiyar taka kuma?

No nan na fara zuwa tukum ,amma barin dubota acan senazo naci girkin tsohuwar matata,don yau naki zanci don haka kisa ashirya min table.

bansan ba, idan kuma matanka sunma na tarya Yaya kenan ?
salon kasa su k'ullaceni ko suga na kwaceka , to banyarda da wannan salonba.

bata fuska amjaad yayi yace nikan kisa nagaya miki azubomin .

duk da hajiya ta ganoshi domin duk ranar girkin rumana a sashinta yake cin abinci amma ta basar  dashi.

Zaune nake abakin gadon sateera,shigowar ta ne yasani d'ago kainà kayan dana sata ta d'auko min a  d'akina ta mikomin ,karba nayi don daman ita nake jira tunda na fito a wanka,bayan nagama Sanya dogon riga ne ,ta shimfid'a min abun sallah ,na hau natada sallar azahar,bayan na idar ne na koma zan kwanta tace anty khubra mom fa ke take jira ki sauko kici abinci.

tashi zaune nayi tareda d'auko da k'afafuwana k'asa,nace to muje ,a falon muka iske mom zaune tana jiran fitowar mu,gurinta na nufa na zauna a d'aya daga cikin kujerun falon nace sannu mom da aiki,tace yauwa daughter antashi kenan?nace ey ,tace to ga abinci can na shirya miki kije kisamu kici wani abu .

tashi nayi na nufi kan dinning din,tasowa mom tayi itama ta bubbud'e kulolin tace wanne kikeso naga kina barci ne dana tambayi abunda kikeso ,shiru nayi inabin abincin gun da kallo har idona ya tsaya akan sinasir ,sekuma gyad'a dafaffiya.

kulan sinasir din na d'auko zan zuba ,mom tayi sauri ta karb'a tace no barshi zanzuba miki,fatana kisamu kici kozakiji k'arfin jikinki.

naci sosai kuwa don sinasir din da miyar yakuwan yamin dad'i sosai ,nakusa cinyewa naga anturo k'ofar falon ,Kai na d'aga don ganin me shigowa,idon mu ne suka sarke dana juna, murmushi nayi masa tareda sauke kaina nacigaba da cin abinci na.

gurin mom yaje ya kama hannunta yace mom ashe ke kika riketa naje inata cikiyarta,baki ta kama tace cab din lallai amjaad baka da ta ido,matarkan ne don baka ganiba kake ta cikiyarta harma kake gayamin , to gatacan karka Kai cikiyar gidan radio,dariya yayi yace ai mom nakusa kaiwa kuwa,dungurin kanshi tayi tareda mik'ewa tayi ciki , shikuma ya nufo kan dinning din, rungumoni yayi tareda mannamin kiss a goshina sannan yaja kujera ya zauna ,yana dudduba abunda yake gurin sannan ya duben yace,yau kuma nan kika tare aka barni acan? gira na d'aga mishi,don har yanzu banjin dad'in jikina,yace meyasa dazakizo baki taho da wayarki ba naketa kiranki   ban samekiba sedai tata ringing ba amsa?
sorry mantawa nayi ,ni seyanzu ma natuna dana bar wayar acan.dubanshi nayi nace wanne zan zuba maka ?
yamutsa fuska yayi yace bani abunda kikaci ,zuba masa nayi sannan na janyo roban dafaffiyar gyad'a nafara ci a hankali ,yanaci yana kallo na ,ahaka mom ta sauko ta samemu ,tace amma dai ba daughter bane tayi serving nakaba ?kallon mamaki yabi mom dashi yace mom itace wani abunne?
ey wani abune don bata da lafiya ne ,shine Kai don rashin tausayi kasata ta zuba maka ,bayan barinta dakayi tsawan kusan sati da yunwa.
baki ya bud'e yace mom yunwa kuma?yanayi yana kallona ,sunkuyar da Kai nayi ,yace mom ita tace na barta da yunwa? ba ita taceba ,amma son kwana nawa tanason cin abu bata samuba kuma kana sane batacin abincin kirki ka zuba mata ido ka barta har yunwa yayi mata kamu ,neman fad'uwa takeyi fa datazo gidannan ,donma tayi tunanin zuwa ta nema dakanta .

goge bakinshi yayi tareda tashi daga yanda yake ya dawo kusa dani ,yajanyo kujera tareda kama hannuna yace mom meyasa ba'a kirani ba ?kuma nima tun safen nake Kiran wayarta bansamunta.

doctor gidan ya Kira awayarshi sannnan ya kama hannuna muka koma kan kujera mom tana biye damu ,tace son ga wannan hoton ka d'auka ka turama zuwaira zandai Sanya data ma wayata yau nima na wuta,kannuwarta kenan datake kano,karba yayi yace gaskiya mom kisa kam don mom zuwaira akwai jidali wataran fa Ina gurin aiki setace wai na nuna miki abu alokacin senace mata baki kusa wataran tace wai nabada wayar akawomiki ki gani , to karka damamin yar uwa ,kuma ta isa dakaine shiyasa, to amma mom don ta isa dani Setana damuna,oh son Allah yashiryamin Kai .karba yayi tareda d'aukar photo a wayarshi , sannan ya bud'e datan don ya tura mata.

sakone ya shigo wayarshi ,Wanda baisan me number ba ,kamar zai share sekuma ya bud'e sakon , mik'ewa yayi yana me had'a zufa duk da ac dake falon yana aiki be hanashi yin zufa ba,take yanayinshi ya sauya .......

CIKAKKIYAR MACEWhere stories live. Discover now