💍CIKAKKIYAR MACE💍
✍🏻 Real Rashida Bature.
PAGE2️⃣5️⃣
Rumana ce take taku d'aya bayan d'aya tamkar bazata taka k'asa ba ga taunan cumgum datakeyi kai daga ganinta kasan gogaggiya ce aduniya ,ga awani taf keken gilashi dayake fuskarta , direct office d'in amjaad tayima tsinke batare da tayi nocking ba ta tura door din office d'in tashiga tana k'as k'as da cumgum din bakinta tana hurawa tana balam balam dashi.
"wani irin shu'umin kallo take mishi tareda janyo kujeran dayake gefe ta matso dashi gaban table din dayake Kai ta tsura mishi ido .
amjaad dake aiki a laptop d'inshi tun bude kofar office d'in daya d'ago Kai yaga Wanda ya bud'e be sake bi ta kanta ba .
"amjaad kenan ,wai kana ganin hakan dakayi na had'a aurena da wata shi zaisanya najanye ma k'udirin aurenka danayi?girgiza kanta tayi tace Sam kayi kuskure kuma karkayi tunanin zan barka , kasani donni kad'ai aka haliccoka muyi rayuwan aure .
waishin na tambayeka mana?,tayi maganar tana me k'ank'ace ido amjaad kakuwasan irin kishinka dakeyi ?
meyasa zakayi gigin zuwa ka had'a aurena da wata? wallahi amjaad zan iya babbaka duk wacce tayi gangancin rab'ar jikin ka don bazan iya raba wannan had'add'en jikinkan da wataba never,don haka ka gaggauta janye wannan banzar k'udirin kan inkuwa ba hakaba wallahi zan kasance nice ajalinta inkuma kana ganin kamar wasa ne to bisimillah karka janye ta karasa maganar taname buga kan table din gabanta tana me tsuke faffadar fuskarta."d'ago lumsassun idonsa Wanda suke burkita mata lissafi yayi yace Allah ko uwata ?koda yake bazance komaiba sema na gode miki domin kin tunamin lokacin kiranta har ya gota da minti biyu ,aikin danakeyine duk yajamin amma thanks dakika tunasheni inkin gama zaki iya tafiya don inason zan kira ruhina.
"wayarsa ya janyo daga gefe ya lalub'o number ya tsaya yad'anyi danne danne kafin ya danna Kira sannan ya Sanya a handsfree ya ajiye akan table .
"zaune nake abakin gadona Ina ninke hijab dina dana wanke suka bushe naji Karan wayata alamar sako ya shigo min don haka na mik'e na d'auko na dawo bakin gadon na zauna tareda bude sakon , *kizama cikin shiri yanzu zankiraki ki fara aiki*
baki na tab'e nace d'an matsala baka da damuwa, ganin wayata ta fara ringing ne se duk na daburce don wallahi ban tab'a zancen soyayya da wani d'a namiji ba."seda wayar takusa tsinkewa kafun na d'aga cikin siririyar muryata nace hello my soulmate! Ina me runtse ido,cak amjaad ya tsaya da aikinsa ya tsurama wayar ido tsakin rumana ne ta dawo dashi daga suman zaune dayi yace baby Ina kika shiga naketa kiranki baki d'aga ba ?ayya my soulmate wayar bata kusa danine hope dai ranka bai b'aciba don bani kaunar ganinka cikin b'acin rai am sorry ,no baby bakimin komaiba kuma banji haushiba, kinsan akoda yaushe Ina matukar kaunar naji muryanki .oh yaaa amjaad kakuwasan yanda nayi kewar muryanka kamar ba dazu nagama jin zazzakar muryanka ba dabadun aikiba da senace aduk lakacin dakake office ka kirani muta hira harse katashi , to amma neman halal kafuta dole nayi hakuri ,amma kuma kasani wannan yanayin shine yanayi wanda yafi muni atare dani,saboda shine yake nesanta ni da kai, to amma yana iya,nema ya zama dole kodan ka samu abin da zaka kula dani da iyayenmu baki d'aya,da wannan nake maka fatan alkhairi Allah yabada sa'a Allah yakaremi Kai da karewan sa, Allah ya kiyaye hanya, sannan ka kular min da kanka sosai my zawjy,Ina kuma rokon ka ka taimaka ka dawo dawuri domin kasamu ka tawo guna da wuri saboda karnayi fama da kewarka love you bohot bohot take care habeby .
"wata irin shu'umar murmushi amjaad ya sake yana gyad'a Kai tareda lumshe ido cikin kasala yace in sha Allah zan iso dawuri kiban 5 mints yau kam natashi duk da d'azu nafito ,tunda kina buk'atar ganina ai dole nazo , no baby ni dai Allah ka zauna kayi aiki inka gama karka tsaya komai ka tawo nidai .
hmmm baby Kona tsaya anan bazan iya ci gaba da aikiba don gaba d'aya kin tayarmin da tsimin nazo naganki , matukar banga wannan cute face dinnan nakiba bazan iya aiwatar da komaiba kema kin rigada kin sani ,kin gama shagwab'ani don haka abarni na tawo .
"ni dai o'o karka tawo yanzu seka rage aikinka don banson aiki yama yawa gobe kaji baby na .
"to ya na iya naji zan daure naga nayi koda da 1 hr ne ince hakan yamiki?
no my gova duk da nasan yanzu hakan a takure kake an tsastsareka da ido to ka mance da kowa kaci gaba da aiki duk me kallonka kuma ka d'auka tamkar nice agurin ,na tabbata baby na zakaji dad'in aikin barin barka kayi aikina I love you , love you too baby ki kulamin da kanki da abubuwa na byeee .
"wani irin wawura rumana takawo ma wayar yayi sauri ya d'auke wayarshi tareda nuna mata kofa yace zaman me kikemin a office ? inace tun d'azu na sallameki ashe baki tafi bane kin makale a kujera kinajin hiranmu to kisani ban yafe Miki jin daddad'an muryan baby na dakikaji ba kije keda allahu.
"bala'i lallai amjaad ka taro March baka da player , to wallahi ka shirya karban gaisuwar mutuwan wannan jakan don tabbas Sena kasheta da ranta zan babbakata ,ta finciki bag dinta tamkar shiyayi mata lefi tayi fucewarta cikin b'acin rai , allah ne kawai ya kaita gurin motarta don gaba d'aya jin garin takeyi yana juya mata.
"nikuwa bayan ganin ya kashe wayar ajiyan zuciya na sauke Ina me taura ma wayar ido tamkar zanga amjaad din ta gabar wayar ,muryan kakus naji akaina tana cewa kekuma dawa naji kina waya haka kamar vesan zafin kudinshiba ?
"Kai kakus bafa wani bane illa amjaad naki ,baki kakus ta washe tare da cewa au kice jaad ne ashe shima ya iya soyayya haka Inka ganshi da tub'unannan fuska bazaka zaci zai iya zama yake wannan kalamin ba oh ni zainabu abu Kai dai kawai kaga mutum.
"Kai kakus yanzu ashe labe kike min ?
"haram karkice haka magana nazo miki senaji kunata zuba soyayya ni karkimin sharhi kingama tafiyata .
da ido na bita don kakus se ita ,da yanzu agabanshi ne bazata iya cemasa na turb'une duskaba ko wanine ya fad'a kakus seta gaya mashi , juyawa nayi na cigaba da aikina inayi naji karan shigowar sako na duba naga amjaad ne na bude kamar haka .
" *hmmm ba laifi inaga dake zamu cigaba da aikin*
"murmushi nayi nace zamaka fadi abun da kakeson fada da bakinka yaro ,nayi saurin toshe bakina da hannayena duka biyu don kar aji nace mishi yaro tamkar yana gurin ,don inda zaiji Allah ne kawai zai rabani dashi.

YOU ARE READING
CIKAKKIYAR MACE
Fiksi UmumLittafi ne na CIKAKKUN MATA wa da suka amsa sunansu CIKAKKUN MATA M , yarinyace wacce take da burin ganin kowace mace agarin tazamo CIKAKKIYAR MACE wacce zata iya sarrafa mijin ta ,ta tarairayeshi ,ta nuna masa tsantsar soyayya,wacce zata zamo tana...